Cutar Lasa: Ba za mu bar cin naman bera ba – Mutanen Taraba

Duk da barnar da cutar Lassa da beraye ke haifarwa take yi a sassan kasar nan, wasu daga cikin mutanen Jihar Taraba suna ci gaba da cin naman beraye.Binciken da wakilin Aminiya ya gudanar ya gano cewa har yanzu wasu mutanen Jihar Taraba na ci gaba da cin naman bera ba tare da la’akari da […]

Cutar Lasa: Ba za mu bar cin naman bera ba – Mutanen Taraba
Cutar Lasa: Ba za mu bar cin naman bera ba – Mutanen Taraba

Duk da barnar da cutar Lassa da beraye ke haifarwa take yi a sassan kasar nan, wasu daga cikin mutanen Jihar Taraba suna ci gaba da cin naman beraye.
Binciken da wakilin Aminiya ya gudanar ya gano cewa har yanzu wasu mutanen Jihar Taraba na ci gaba da cin naman bera ba tare da la’akari da illar da cin naman beraye ke haifarwa ba.
Binciken ya kuma gano cewa ana sayar da kyafaffun beraye a wasu daga cikin kasuwanin jihar da suka hada da kasuwar Tella da Maihula da dan’anacha da wasu kasuwanni a sassa daban daban na jihar.
Har wa yau kuma ana ci gaba da farautar beraye a wasu sassan jihar inda cin naman berar ya zama gado kaka da kakanni.
Wasu daga cikin masu cin naman beran da wakilinmu ya zanta da su, sun nuna cewa duk da bullar cutar ta Lassa, su ba za su bar cin naman bera ba domin nama ne mai dadi.
Wani magidanci mai suna Mista James Awoko ya shaida wa wakilinmu cewa yau fiye da shekara 50 ke nan yana cin naman bera kuma ba abin da ya taba samunsa. Ya ce ya ta so ya ga iyayensa suna cin naman bera kuma ba su taba ganin wata cuta da ke da alaka da cin bera ta shafe su ba.
Da yake magana dangane da wannan al’ada ta cin naman bera da wasu jama’ar jihar ke yi Shugaban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo, Dokta Wiza Inusa ya ce akwai matukar illar a cin naman berar kuma ya zama tilas a watsar da wannan al’ada.Ya ce ya kamata gwamnatin Jihar Taraba ta tashi tsaye ta wayar da kan jama’a kan illar cin naman bera, musamma da yake beran ne ke hifar da cutar Lassa wadda tuni ta hallaka mutane masu yawa a kasar nan har ma da Jihar Taraba.
Dokta Wiza ya ce yau shekara hudu ke nan ana samun bullar cutar Lassa a kowace shekara a jihar. Don haka ya ce ya zama tilas a fadakar da al’ummar jihar illar da ke tattare da cin naman bera kuma tabbas beraye ne ke hassada wannan mummunar cuta.
Shugaban ya ce saboda barazanar da cutar ke yi a jihar Gwamnatin Tarayya ta amince a gina cibiyar binciken cutar ta Lassa a jihar.
Cutar ta Lassa ta hallaka rayukan likitoci biyu wato Dokta Manu Abba Tukur da Dokta A’isha Nasiru Bobboji bayan sun yi wa wadanda suka kamu da cutar ta Lassa jinya a jihar.