Cutar Lassa ta ci Nas mai kula da majinyata a Nasarawa
Wani jami’an Nas mai suna Ibrahim Oshafu da ke aiki a Asibitin dwararru na dalhatu Arab da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ya rasu bayan ya yi wa wata matar aure mai dauke da cutar zazzabin Lassa jinya a asibitin. Wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Asibitin Dokta Yakubu Afiku ta tabbatar da rasuwar […]
Wani jami’an Nas mai suna Ibrahim Oshafu da ke aiki a Asibitin dwararru na dalhatu Arab da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ya rasu bayan ya yi wa wata matar aure mai dauke da cutar zazzabin Lassa jinya a asibitin.
Wata sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Asibitin Dokta Yakubu Afiku ta tabbatar da rasuwar Nas din inda ta ce bayan Nas din ya yi jinyar matar wacce ta rasu daga baya, sai shi ma ya rasu sakamakon kamuwa da dwayar cutar da ya yi daga matar.
Shugaban Asibitin wanda ya yi addu’ar Allah Ya jidan Nas din ya bayyana shi da matsayin mai dwazo a aiki inda ya kuma shawarci sauran likitotin asibitin musamman wadanda ke kula da masu cututtuka masu yaduwa irin su zazzabin Lassa, su tabbatar suna bin da’idodin aikin jinya a duk lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Bayan rasuwar Ibrahim Oshafu dungiyar ma’aikatan asibitin a dardashin jagorancin shugabanta Dokta Suleiman Musa sun gudanar da zanga-zangar lumana inda suka budaci Hukumar Gudanarwar Asibitin ta samar musu da isassun kayayyakin jinya ga masu dauke da cutar Lassa da sauran cututtuka masu yaduwa.
A cewar shugaban a yanzu babu isassun kayayyakin kare-kai na likitoci da ma’aikatan asibitin shi ya sa suke kamuwa da cututtuka daga wadanda suke jinyarsu.
Da yake mayar da martani Dokta Yakubu Afiku ya yi aldawarin idar da sadonsu ga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar cikin gaggawa inda ya budaci likitoci da ma’aikatan su yi amfani da kayayyakin kariya da ke asibitin a yanzu yadda ya kamata don guje wa sake aukuwar lamarin a gaba.
Aminiya ta gano cewa mutum uku da suka kamu da cutar Lassa sun rasu a jihar.