Cutar Lassa ta halaka mutum daya 32 sun kamu a Gombe
Rahotanni daga ma’aikatar lafiya ta jihar Gombe na bayyana cewa, an samu bullar cutar zazzabin lassa inda ake zargin mutum 32 sun kamu, an tabbatar da mutum biyar suna dauke da cutar kuma guda ya rasu sanadiyyar cutar. Likitan babban asibitin Dakta Nuhu Bile ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a jiya […]
Rahotanni daga ma’aikatar lafiya ta jihar Gombe na bayyana cewa, an samu bullar cutar zazzabin lassa inda ake zargin mutum 32 sun kamu, an tabbatar da mutum biyar suna dauke da cutar kuma guda ya rasu sanadiyyar cutar.
Likitan babban asibitin Dakta Nuhu Bile ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a jiya Alhamis.