Cutar MERS: Saudiyya za ta hana hadaya da rakuma a bana

Sakamakon barkewar cutar murar nan ta MESR a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, tare da tsoron barkewar cutar mai saurin hallaka mutane, mahukuntan kasar suna duba yiwuwar hana yin hadaya da rakuma a yayin aikin Hajjin bana.Ministan Lafiya na Saudiyya Khalid AL-Falih a ranar Asabar ya fadi a shafinsa na Tweeter a ranar Asabar cewa […]

Cutar MERS: Saudiyya za ta hana hadaya da rakuma a bana
Cutar MERS: Saudiyya za ta hana hadaya da rakuma a bana

Sakamakon barkewar cutar murar nan ta MESR a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, tare da tsoron barkewar cutar mai saurin hallaka mutane, mahukuntan kasar suna duba yiwuwar hana yin hadaya da rakuma a yayin aikin Hajjin bana.
Ministan Lafiya na Saudiyya Khalid AL-Falih a ranar Asabar ya fadi a shafinsa na Tweeter a ranar Asabar cewa “Ma’aikatar Lafiya tana aiki wurjanjan don dakile cutar da ta barke a baya-bayan nan.” Kamar yadda jaridar Wall Street Journal ta ruwaito a ranar Lahadi.
Saudiyya ta ce an samu rahoton barkewar cutar MERS sau shida a ranar Lahadi a daidai lokacin da miliyoyin maniyyata aikin Hajji suka fara isa kasar.
kwayoyin cutar MERS suna haifar da matsalar numfashi da zazzabi da cutar nimoniya da kuma illa ga huhu, kuma tana hallaka rabin mutanen da suka kamu da ita.
Tun bayyana cutar a shekarar 2012 ta harbi mutum 1,147 tare da hallaka 487 kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta bayyana.
Kuma a kokarin dakile yaduwar kwayar cutar ne kasar take duba yiwuwar hana yin hadaya da rakuma a bana, bayan da aka hakikance suna yada kwayoyin cutar ga mutane.
Kakakin Ma’aikatar Lafiya na Saudiyya Khaled Al-Mirghalani ya shaida wa jaridar Arab News a Juma’ar da ta gabata cewa ma’aikatar tana tattaunawa da jami’an Gwamnan Makka da biranenta kan yadda za a hana yin hadaya da rakuma a Hajjin bana.
“Idan bangarorin uku suka cimma matsaya, za a sanar da hanin nan da ’yan kwanaki kafin fara aikin Hajjin,” inji shi.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50