Cutar munafunci (2)
Daga Hudubar Sheikh Aliyu Bin Abdurrahman AlhuzaifiMasallacin Annabi (SAW), Madina Kuma daga cikin munafunci na kudiri akwai: Yin farin ciki idan Musulunci ya samu rauni da yin farin ciki idan mutane sun yi masa tawaye da karan-tsaye da burin lalacewar koyarwarsa da nuna kyama ga rinjayen shiriyar Manzon Allah (SAW) da daukakar addininsa. Allah Madaukaki […]
Daga Hudubar Sheikh Aliyu Bin Abdurrahman Alhuzaifi
Masallacin Annabi (SAW), Madina
Kuma daga cikin munafunci na kudiri akwai: Yin farin ciki idan Musulunci ya samu rauni da yin farin ciki idan mutane sun yi masa tawaye da karan-tsaye da burin lalacewar koyarwarsa da nuna kyama ga rinjayen shiriyar Manzon Allah (SAW) da daukakar addininsa.
Allah Madaukaki Ya ce: “Hakika sun nemi fitina a gabani, kuma suka juya maka al’amura har gaskiya ta zo, kuma al’amarin Allah ya bayyana alhali suna masu ki.” k: Tauba:48). Kuma Allah Ya ce: “Munafikai maza da munafikai mata sashinsu ga sashi suna umarni ne da abin ki, suna hana alheri, kuma suna damke hannunwansu (rowa), sun manta Allah, sai Ya mantar da su kawunansu. Lallai munafikai su ne fasikai.” (k:Tauba:67).
Ma’abucin wannan nau’in munafunci na kudiri, a Lahira yana gida mafi kaskanci a cikin wuta, shin ya hada wadannan nau’o’in munafuncin ne ko kuma ya siffantu da nau’i daya daga cikin nau’o’in, sai dai in ya tuba zuwa ga Allah.
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai munafikai suna a cikin mafi kaskanci gida a ciki wuta. Kuma ba za ka sama musu wani mai taimako ba.” (k:4:145). Wannan saboda cutarwar munafiki ta fi tsanani ne daga cutarwar kafirin da ya bayyana kafirci.
Nau’i na biyu na munafunci shi ne munafunci na aiki. Munafunci na aiki shi ne: Mutum ya aikata wani abu daga cikin ayyukan munafunci tare da hakan yana mai imani da Allah da Ranar Lahira. Yana son Musulunci yana aiki da rukunansa, to wannan ya aikata sabo ne, kuma ba za a kafirta shi don aikata sabo ba.
An karbo daga Abdullahi Bin Amru (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Abu hudu wanda ya kasance yana tare da su cikakken munafiki ne, wanda yake da daya daga ciki, yana da yankin munafunci har sai ya bar shi: wato idan zai yi magana ya yi karya; idan ya yi alkawari ya saba; idan aka ba shi amana ya yi ha’inci; idan ya yi husuma ya yi fajirci.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Ma’anar “idan ya yi husuma ya yi fajirci,” shi ne ya nemi fiye da hakkinsa, ko ya yi da’awar abin da ba nasa ba, ko ya ce ba a ba shi hakkinsa ba.
Kuma an karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Alamun munafiki uku ne: idan ya yi magana ya yi karya; idan ya yi alkawari ya saba; kuma idan aka ba shi amana ya ci.” Muslim ne ya ruwaito.
Wadannan dabi’u ko halaye idan Musulmi ya aikata su, alhali yana aiki da rukunan Musulunci, yana sonsa, to sabonsa munafunci ne na aiki ba na kudiri ba.
Kuma dabi’u da halayen munafunci ba su takaita kan wadannan nau’uka ukun kadai ba, domin yankin munafunci yana mukabala da yankin imani ne. Kuma hakika Annabi (SAW) ya ce: “Imani yanki saba’in ne da doriya. Mafi daukakarsu fadin: La’ilaha illallah, na karshensu kuma kawar da abin cutarwa daga kan hanya.” Buhari da Muslim ne suka ruwaito daga Hadisin Abu Huraira (RA).
Annabi (SAW) ya ambaci munafunci a cikin wadannan al’amura uku ne, saboda sauran dabi’u da halayen munafunci suna komawa ne gare su, saboda su ne asalinsu. Idan Musulmi bai ji tsoro ya kange kansa daga dabi’un munafunci a aikace ba, kuma idan bai tuba zuwa ga Allah daga gare su ba, har suka zame masa jiki suka ja shi zuwa ga munafunci na kudiri, sai ya koma cikin masu dawwama a cikin wuta.
Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wandanda suka yi imani! Ku yi wa Allah takawa, kuma ku kasance daga cikin masu gaskiya.” (k: Tauba: 119).
Allah Ya yi mana albarka a cikin bin Alkur’ani Mai girma, kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da yake cikinsa na Zikiri Mai hikima. Kuma Ya amfanar da mu da shiriyar Shugaban Manzanni da maganarsa datacciya. Ina fadin wannan magana tawa ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku da sauran Musulmi.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai kuma waliyin muminai. Ina gode wa Ubangijina ina yi maSa shukura. Kuma ina tuba gare Shi, ina neman gafararSa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Mai karfi, Matabbaci. Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda aka aiko da shiriya da yakini. Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci da albarka a bisa bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah da takawa bisa hakkin bin Sa da takawa, domin bin Allah shi ne mafi alherin guzuri a duniya da ranar da ake komawa gare Shi.
Ya bayin Allah! Lallai zunubai duk yadda suka kai da girma da yawa, to a bangaren rahamar Allah su ababen gafartawa ne in aka tuba ga Allah Madaukaki.
Hakika Allah Ya kira mushirikai zuwa ga tuba, alhali suna sanya wa Allah wani abin bauta. Sai Allah Madaukaki Ya ce kan Annabi Salihu (AS): “Ya ku mutanena! Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta koma bayansa. Shi ne Ya kaga halittarku daga kasa, kuma Ya raya ku a cikinta. Don haka ku nemi gafararSa, sannan ku tuba zuwa gare Shi. Lallai Ubangjina, Makusanci ne Mai amsa (tuba). (k:Hud:61).
Kuma Allah Ya umarci wanda ya sanya wa Allah da kan ya tuba, inda Madaukaki Ya ce: “Shin yanzu ba za su tuba zuwa ga Allah ba, kuma su nemi gafararSa? Kuma Allah Mai gafara ne Mai jin kai.” (k:Ma’ida:74). Kuma Ya bude wa munafikai kofar tuba, inda Ya ce: “Lallai munafikai suna a cikin mafi munin gida a cikin wuta, kuma ba za ka sama musu wani mai taimako ba. Face wadanda suka tuba kuma suka gyara, kuma suka yi riko da Allah, kuma suka tsarkake addininsu saboda Allah. To wadannan suna tare da muminai. Kuma da sannu Allah zai zo wa muminai da lada mai girma.” (k:Nisa’i: 145-146).
To ya kai Musulmi! Idan an jarrabe ka da wani abu daga cikin dabi’u ko siffofi ko alamun munafunci, to ka tuba zuwa ga Allah Madaukaki. Ka tsarkake ranka kafin ka mutu, kuma ka roki Allah Ya kare ka daga munafunci da alamominsa, domin Allah Madaukaki Makusanci ne Mai karbar tuba.
Daga cikin addu’o’in Annabi (SAW) akwai: “Allahumma inni a’uzu bika minan nifaki wasshikaki wa su’ul akhalaki.” Ma’ana: “Ya Ubangiji! Ina neman tsarinKa daga munafunci da shakiyanci da munanan dabi’u.” A wata addu’ar kuma yana cewa: “Allahumma dahhir kulubana minan nifaki wa a’amalana minar riya’i wa a’ayunana minal khiyanati.” Ma’ana: “Ya Ubangiji! Ka tsarkake zukatanmu daga munafunci da ayyukanmu daga riya da idanunmu daga ha’inci.”
Ya bayin Allah! “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi.. Ya ku wadanda kuka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi (masa) taslimi da sallamawa.” (k:Ahzab:56).