Cutar murar tsuntsaye: Ana ci gaba da cin kaji a Kano
Bayan mako biyu da samun labarin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihar Kano, jama’ar jihar suna ci gaba da cin naman kaji ba tare da wata fargaba ba. Binciken da Aminiya ta gudanar a gidajen sayar da abinci a Kano ya gano cewa masu sayen abinci na ci gaba da sayen naman kaji kamar yadda […]
Bayan mako biyu da samun labarin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihar Kano, jama’ar jihar suna ci gaba da cin naman kaji ba tare da wata fargaba ba.
Binciken da Aminiya ta gudanar a gidajen sayar da abinci a Kano ya gano cewa masu sayen abinci na ci gaba da sayen naman kaji kamar yadda suka saba.
Jami’in kula da gidan abinci na Jalingo Restaurant, Maustapha Abubakar ya ce, “Mu dai a nan abokan cinikinmu ba su daina cin naman kaji ba, duk wanda ya saba yana saye ba tare da nuna shakka ko tsoro ba.
Mafi yawan mutanen da suke cin naman kajin da Aminiya ta tattauna da su sun ce suna sane da batun bullar cutar murar tsuntsaye sai dai hakan ba zai hana su cin naman kajin ba, saboda a cewarsu dama can kaji suna rashin lafiya a lokacin hunturu kuma bai hana
mutane cin namansu ba.
Muhammad Sani Aminu ya ce “Abin da ya sa ban daina cin naman kaji ba duk da na ji labarin bullar cutar murar tsuntsaye a jihar nan shi ne ganin dama tuntuni kaji sukan yi ciwo a lokacin hunturu har ma su yi ta mutuwa, don haka ina ganin babu wani abu da
zai same ni don na ci gaba da cin naman kaza a wannan lokaci.”
Binciken Aminiya a kasuwar kaji ta Kasuwar Rimi a birnin Kano ya gano cewa bullar cutar ta jawo rashin cinikin kaji, kuma farashinsu ya yi kasa kadan.
Malam Abubakar Malami mai sayar kaji ne a kan titin Gidan Zoo ya ce cinikin kaji ya ja baya, sakamakon bullar cutar, “Kafin bullar murar tsuntsaye ina sayar da kaji kamar 20 a kullum, amma a yanzu da kyar nake sayar da 10. Idan muka kira abokan cinikinmu cewa za mu kai musu kaji gida sai su ce sai bayan annobar ta lafa,” inji shi.
Darakta kula da dabbobi a Ma’aikatar Gona ta Jihar Kano Dokta Shehu Bawa ya shaida wa Aminiya cewa duk da babu laifi ci gaba da cin naman kaji, amma akwai bukatar a
tabbatar da lafiyarsu. “Ba mu ce kada a ci kaza ko kwai a yanzu ba, amma akwai bukatar jama’a su kula ta hanyar tabbatar da lafiyarsu,” inji shi.
Dokta Bawa ya ce, “Abin da gwamnatin jihar ta fara yi shi ne shiga kasuwanni, inda ake kawo kaji daga wurare daban-daban, a nan muka gano cewa kaji na mutuwa. Daga nan muka tabbatar cewa akwai matsala. Mataki na gaba sai gwamnatin ta shirya bita inda muka gana da masu kiwon tsuntsaye da kaji don wayar musu da kai a kan cutar da kuma neman hadin kansu don a gudu tare a tsira tare.”
Ya yi kira ga masu kiwon kaji a duk lokacin da suka ga kajinsu na mutuwa fiye da kima, to kada su tsaya sayen magani su hanzarta zuwa asibitin dabbobi domin daukar matakin da ya dace.