Cutar pneumonia ka iya kashe yara miliyan daya a Najeriya – MDD
Yara kusan miliyan 1.4 ne a Najeriya ka iya rasa rayukansu sakamakon cutar pneumonia mai alaka da sanyin yanayi a cikin shekara 10 masu zuwa, in ji Mjalisar Dinkin Duniya (MDD). A wani rahoto da asusun yara na MDD wato Unicef ya fitar, ya yi hasashen cewa Najeriya ka iya fuskantar mafi yawan mace-mace a […]
Yara kusan miliyan 1.4 ne a Najeriya ka iya rasa rayukansu sakamakon cutar pneumonia mai alaka da sanyin yanayi a cikin shekara 10 masu zuwa, in ji Mjalisar Dinkin Duniya (MDD).
A wani rahoto da asusun yara na MDD wato Unicef ya fitar, ya yi hasashen cewa Najeriya ka iya fuskantar mafi yawan mace-mace a duniya, wanda cutar ta pneumonia za ta haifar.
Yara miliyan 6.3 ne Unicef ya yi hasashen za su mutu a duniya baki daya daga cutar.
MDD ta yi hasashen kasar Indiya ce ta biyu da za a fi samun mace-macen, sai kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da za ta iya zama ta uku.
Asusun yaran ya ce yara miliyan 9 ne za su mutu daga pneumonia da kuma wasu manyan cutukan idan har ba a dauki matakan riga-kafi ba.
Unicef ya bayar da shawarar a kara yawan riga-kafin domin kauce wa mace-macen sannan kuma ya ce tuni Najeriya ta fara yin hakan.