Cutar Zazzabin Lassa ta kashe mutum 156 a wata 4 a Najeriya —NCDC
An samu bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi 103 a jihohi 26 Najeriya
Cutar zazzabin Lassa ta kashe mutum 156 a jihohi 26 a cikin wata hudu da suka gabata a Najeriya.
Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce kawo yanzu, mutum 897 ne aka tabbtar sun kamu da Zazzabin Lassa, banda wasu mutum 4,908 da ake zargin suna dauke da kwayar cutar.
- Yau NAFDAC za ta fara bincikar Indomie kan ‘hadarin cutar kansa’
- Motar kwashe ’yan Najeriya ta yi gobara a hanyar Port Sudan
Ta bayyana cewa jihohin Ondo da Edo da Bauchi ke dauke da kashi 72 cikin 100 na masu cutar, sauran jihohi 23 kuma ke da ragowar kashi 28.
Rahoton da hukumar ta fitar ya bayyana cewa, “Kawo yanzu a shekarar 2023 an samu bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi 103 a jihohi 26 Najeriya.”
Amma ta rahoton ya nuna an samu raguwar mace-mace sakamakon cutar, idan aka kwatanta da wata hudu na farkon shekarar 2022, duk da cewa an samu karuwar wadanda ake zargin suna dauke da kwayar cutar.
Yankunan da aka samu bullar cutar har da babban birnin Tarayya Abuja, sai jihohin Kano da Jigawa da Bauchi da Gombe da Taraba da Nasarawa da Filato da Binuwai da Kogi da Ondo da Edo da Ebonyi da Enugu da sauransu.