Cutar Zazzabin Lassa ta kashe mutum 80 a Najeriya —NCDC
Lassa fever ta kashe mutum 80 a fadin Najeriya.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta ce mutum 80 ne suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar Zazzabin Lassa, ya zuwa ranar Alhamis.
NCDC ta bayyana wa taronta na bayar da rahoto kan barkewar cutar a Abuja cewa kawo yanzu an samu mutum 434 da suka kamu da cutar a fadin Najeriya.
- An bankado almundahanar N8.5bn a Majalisar Dokoki ta Kasa
- Najeriya A Yau: Yadda ’yan Najeriya ke rayuwa a kan Naira 1000
“Daga wawan Janairun 2021 zuwa yanzu, mutum 434 sun kamu da cutar, sannan mutum 80 sun mutu daga jihohi 17 da kananan hukumomi 63 da ke Najeriya,” a cewar sanarwar NCDC
Ta kara da cewa, “Irin wannan cutar a Najeriya kamar sauran kasashe ta fi bayyana ne a lokacin sanyi, kamar daga watan Nuwamba zuwa watan Mayu a duk shekara.”
Hukumar ta bayyana cewa Jihar Edo na da mutum 192, Ondo 150, Taraba 21, Ebonyi 17, Bauchi 15, sai Benuwai mutum takwa.
Filato na da mutum takwas, yayin da Kaduna ke dauke da mutum bakwai da suka kamu.
Sauran jihohin sun hadar sa Enugu da mutum biyar, Nasarawa na da uku, Kogi na da uku, Kuros Riba na da mutum daya, Imo na da mutum daya, Anambra na da mutum daya, Delta na da mutum daya, sai jihar Abiya mai mutum daya ita ma.