Cutar Zika ta bulla a Amurka

Mahukunta a Jihar Tedas ta kasar Amurka sun ce a karon farko kwayar cutar Zika, wacce sauro ke yadawa, ta bulla a jihar.Sun ce akwai yiwuwar an samu yaduwar kwayar cutar ne ta hanyar jima’i, saboda wanda ya kamu da ita bai yi tafiya zuwa kasar waje ba, amma kuma ya yi mu’amala da mai […]

Cutar Zika ta bulla a Amurka
Cutar Zika ta bulla a Amurka

Mahukunta a Jihar Tedas ta kasar Amurka sun ce a karon farko kwayar cutar Zika, wacce sauro ke yadawa, ta bulla a jihar.
Sun ce akwai yiwuwar an samu yaduwar kwayar cutar ne ta hanyar jima’i, saboda wanda ya kamu da ita bai yi tafiya zuwa kasar waje ba, amma kuma ya yi mu’amala da mai dauke da cutar a lokacin yana wajen kasar ta Amurka.
Har ila yau, sun kara da cewa akwai bukatar kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a kan cewa ana iya yada cutar ta Zika ta hanyar jima’i.
Sauro ne dai aka sani da yada kwayar cutar, wacce ake dangatawa da annobar haihuwar yara masu tawaya a kasar Brazil.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce annobar ta zama wacce ke neman daukin gaggawa a duk fadin duniya.