Cututtukan zamani ishara ce gare mu

Edita don Allah ka ba ni dama  in yi tsokaci dangane da cutar da ta fara addabar wasu kasashe, musamman kasashen Afirka, wato cutar Ebola. Hakikka wannan cuta abin tsoro ne ganin yadda take kisan mutane farad daya, don haka nake shawartar ‘yan uwa da mu dage da addu’a Allah ya yi mana maganin ire-iren […]

Cututtukan zamani ishara ce gare mu
Cututtukan zamani ishara ce gare mu

Edita don Allah ka ba ni dama  in yi tsokaci dangane da cutar da ta fara addabar wasu kasashe, musamman kasashen Afirka, wato cutar Ebola. Hakikka wannan cuta abin tsoro ne ganin yadda take kisan mutane farad daya, don haka nake shawartar ‘yan uwa da mu dage da addu’a Allah ya yi mana maganin ire-iren wadannan cututtuka, tare da jan hankulanmu da mu koma ga Allah hakan zai sa Allah ya jikanmu, Ya kuma yaye mana wadannan cututtuka.

Ga Gwamna Lamido
Edita kowa da gwaninsa, ni ma ga gwanina, Gwamnan Jihar Jigawa, Mai alfarma, Allah Ya taya riko; Allah Ya sa ka gama lafiya; Allahumma amin. Daga Garba Kyari Kafin Hausa 08062297756.

Ta’aziyya ga Sheikh el-Zakzaky
Assalam. Don Allah ku ba ni dama in mika sakon ta’aziyya ga Sheikh Ibrahim el-Zakzaky game da mutuwar ’ya’yansa, uku maza. Allah Ya gafarta musu, Yasa mutuwa ta zama hutu garesu. Daga Jamilu Gambo Takai 08166835313

Ga Salihu Sagir Takai
Aminiya ina so ku ba ni dama in mika sakon shawara ga Malam Salihu Sagir Takai, day a bar jam’iyyar PDP, ya koma APC. Domin wallahi mun gane cewa yaudararsa ubangidansa ke yi. Daga Alhaji Gambo Takai 08094571634.

Jana’izar APC a Sakkwato
Mu talakawa ba ma son wannan jam’iyya, ba ma tare da ita. Bafarawa muke yi jam’iyyar PDP. Fatarmu kawar da azzaluma daga Sakkwato. Daga Musty Sok 08034068363..

An kai wa kowa hari
Salam. Don Allah Edita ka isar min da sakona ga Musulmin Najeriya. Al’amarin ya zama babu dan darika ko izala ko sjhi’a, kowa kai masa hari ake yi.. Sai mu duba, Allah Ya kiyaye mu. Daga Ibrahim Sarki, Kawanar Lami, KD. 07039057451

Na dawo Edita
Ina tare da ku. Na dawo daga tafiya karatu da na yi, kuma zan ci gaba da sayen wannan jarida mai farin jinni. Allah Ya kare ku. Daga naku Salim Abubakar Bauchi 08078484343. 07087278714.

Ga Ajiyan Bakori
Edita ka dubi girman Allah ka ba ni dama in yi godiya da addu’a  ga Ajiyan Bakori, Ibrahim Turkur, saboda koyi da yake yi da Gwamna Shema. Yana taimakon bayin Allah da dora matasan Bakori da danja kan tarbiyya. Mun gode. Allah Ya kai likafa gaba. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086/ 07068147933.

A yi sitta shawwal
Aminiya ina yi wa ‘’yan uwa Barka da Salla, da fatan ba za a manta d asita shawwal ba. Daga Amina Jibril Kano 07054808734.

Ga Aminiya
Aminiya aikinku yana kyau. Allah Ya kare ku daga makiya Najeriya, ku ci gaba da tona musu asiri. Daga Sani Ya Malam Kano 08126466663.

Gwamnati ta san ’yan ta’adda
Asslamu alaikum. Aminiya, sakona ’yan Najeriya su daina danganta Boko Haram da addini, tunda idan Gwamnati ba ita ke yi da kanta ba, ai ta san masu yi. Gwamnati ta san wadanda ke kashe al’umma ba tare da hakkinsu ba, amma saboda son rai an kasa yin maganin matsalar. To Allah Ya kawo wa al’umma dauki. Amin. Daga Babangida U. Dikko 07068814721.

Jaje ga Kanawa
Edita Dan Allah ka ba ni dama  in mika jajena dangane da hare haren da aka dinga kaiwa a wasu gurare da ke Kano. Hakika addu’a ce ta hana tasirin tashe-tashen bama-bamai a Kano muna addu’ar Allah ya kara kiyaye, Allah ya kawo mana karshen tashe tashen hankula a ko’ina. Daga Fatima Shu’aibu Attahir(One Lobe Family Kalfu Sokoto).

Murnar ’yanci shekara 50 ga Nijar
Ina taya Gwamnati da alummar jamhuriyar Nijar murnar cikar kasar shekaru 50 da samun ‘yancin kan kasar. Da wannan nake kira ga: ‘Yan siyasar kkasar da su koyi darasi da irin wannan rana wajen hada kawunansu, tare da kauda duk wani bambance-bambancen siyasa, don cigaban kasarsu. Kamar yadda mutanen da suka yi fafutikar ganin kasar ta samu ‘yanci suka yi. Daga karshe nake addu‘ar Allah ya kawo mana zaman lafiya, da karuwar arziki a kasashenmu na Afrika baki daya. Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.

Ta’aziyya ga Isyaka Rabi’u
Salam Edita don Allah ka mika min ta’aziyyata ga Malam Isyaka Rabi’u, game da rasuwar matarsa Sa’adatu, allah Ya gafarta mata; Allah Ka sa ta huta amin. Daga Saadu (Baffa) Funtuwa 08078535480.

Ebola jarrabawar Allah ce
Ina kira  ga jama’ar Najeriya da ma Afirka baki daya da mu koma ga Allah, don wannan cutar Ebola jarrabawa ce daga Allah. Da fatan za mu gyara halayenmu. Amin. Daga Isah Diwaala, Abuja 08059044449/08025257920.

Ga Sule Lamido
Zuwa ga Sule Lamido, dangane da bayar da tallafin nakasassu, wato hancap, a Jigawa. Gaskiya ya yi kadan. Ana bai wa nakasassu Naira dubu 10-10, biyar-biyar. Dalili kuwa a cikin kananan hukumomi 27, mutum 10-10 aka diba, sabanin Gwamnatin Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso yana kokari da gaske. Daga Alhaji Muhammad dababa Kowa, Kurma Sarkin Ruwa 09025961595.

Ga hukumomi
Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. A madadin daiban Jami’a, muna kira ga hukumomi, domin daukar mataki, bisa kisan gillar da aka yi, a Zariya da ya rutsa da Mahmud da Hamid da Ahmad Ibrahim el-Zakzaky. Allah Ya jikan magabatanmu. Daga Salisu Saidu, A.B.U. Zaria. 08023666517.

Adamu Mu’azu alheri ne
Zuwa ga  shugaban PDP Adamu Mu’azu, alheri ne domin tunda ya zama shugaba PDP da wuya ka ji an fita daga PDP, sai dai fita daga wata jam’iyyar a koma PDP. Daga Masoyin Tsohon Gwmanan Kano, Tsohon dantakarar Shugaban kasa, Sardaunan Kano, Kuma Sabon Ministan Ilimi, M. Ibrahim Shekarau, Isyaku Captain Kofa 08067226769.

Ta’aziyya ga mutanen Zariya
Salam Edita ka ba ni dama in mika ta’aziyya ga ’yan uwa wadanda suka yi shahada a Zariya. Daga Arsenee Zamawee, Birniwa Jigawa 08164443292.

Ta’aziyya ga Zariya da Kano
Salam Edita ka mik amin ta’aziyya ga mutanen Zariya da Kano. Daga 07039057451.