Cuwa-cuwa a Jihar Borno?

Assalamu alaikum, Aminiya mai farin jini ku ba ni dama in yi kira ga Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno. A gaskiya yakamata ka sanya kwamitin bincike domin a kawo karshen cuwa-cuwar da wasu jami’an gwamnatinka suke yi wa kananan ma’aikata a kananan hukumomin jihar don shekaru biyu da suka wuce sun yi amfani da […]

Cuwa-cuwa a Jihar Borno?
Cuwa-cuwa a Jihar Borno?

Assalamu alaikum, Aminiya mai farin jini ku ba ni dama in yi kira ga Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno. A gaskiya yakamata ka sanya kwamitin bincike domin a kawo karshen cuwa-cuwar da wasu jami’an gwamnatinka suke yi wa kananan ma’aikata a kananan hukumomin jihar don shekaru biyu da suka wuce sun yi amfani da damar su wajen sayar da aikin gwamnati a kan Naira dubu 80 zuwa sama ba tare da sun fuskanci fushin gwamnati ba. 

Har ila yau yanzu sun sake fito da sabuwar hanyar azurta kansu cikin sauki wajen yin sama da fadi da kuma cuwa-cuwa. don haka muke sanar da kai don ka gaggauta dakile wannan zaluncin tun kafin ya zama jiki ga al’ummar Jihar Borno.
Rahin imanin da aka tafka na baya bayan nan shi ne yadda aka bankado wani jami’i a karamar Hukumar Damboa ya rage wa kananan ma’aikata Naira dubu daddaya daga cikin albashin su gabanin daurin aurensa.
Tambayata a nan ita ce an taba bada gudunmawar dole ne? Shin yin hakan sata ne ko kuwa cin hanci da rashawa?
Daga Adamu Aliyu Ngulde, karamar Hukumar Damboa A Jihar Borno 08032135939.

korafi ga ’yan sanda
Salam don Allah Edita ka ba ni dama in yi korafi akan ’yan Sanda. Don Allah ku rika tausayawa masu abin hawa, ko don wannan wata mai alfarma. Hakika masu ababenn hawa suna kokawa da ku musanman mu masu babur. Gaskiya ba ma jin dadin abin da kuke yi mana musamman wajen karbar na-goro.
Daga Shu’aibu Sarkin Fulanin Facebook

Aminiya ta cancanci yabo
Yabo da jinjina na musaman ga Jaridar Aminiya musamman a bisa yadda take kawo mana amintattun labarai masu nishadantarwa da ilmantarwa, da ban al’ajabi. Zan so a ce ku rika buga jaridar sau biyu ko sau uku a duk mako. Godiyata ga editoci da wakilai da marubutan jaridar Aminiya.
Daga Bilya Tukur Bakori 07030225194

Allah Ka kawo mana dauki
Ya Allah don albarkar wannan wata na Ramadan da kuma son Annabinka (SAW) Ka kawo muna karshen hare- haren ta’addanci da kungiyar Boko Haram ke kai wa al’ummar Najeriya.
Nazairu Abubakar Sabo Gusau 07033565999

Fatan alheri
Salam Editan Aminiya! Ya Allah! Ka sa mu gama da duniya lafiya.
Sako daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna 08024122559

Ga Gwamnan Bauchi
Aminiya don Allah muna son a mika mana sakonmu zuwa ga Gwamnan Bauchi da ya yi wa Allah ya biya wa ma’aikata albashin da suke bi har na tsawon watanni biyu su kuma masu aikin sharar hanya suna bin albashin watanni biyar.
Daga Abbati Nesta Azare

Ga ’yan majalisa
Salam, Aminiya ku gaya wa ’yan majalisa kan talaka ya waye. Tunda mun gane ungulu da kan zabo kuka yi mana ku saurari kiranye daga mazabunku. Kuma girma da kimarku ya zube, tun da ba ku girmama uwar jam’iyyar da ta kawo ku majalisar ba. Sai hadamar mulki wanda ba shi muka tura ku ba.
Daga Fatima daga Katsina

Solomon Dalung ya cancanta
Edita, ina son a baiwa Barista Solomon Dalung Shugaban Hukumar EFCC.
Daga Hassan Babayo Direban Tanka Gombe

Ga Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari mun yi murna da da fara aiki a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa (billa). Allah Ya taimake ka, Ya sa ka kawo mana karshen ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa a kasarmu Najeriya.
Daga Ibrahim (Bobo Sita) Bauchi 07037505701

Edita ban damu ba!
Salam Edita, ko ka buga sakona a wannan shafi ko kada ka buga, ban damu ba, zan cigaba da sayen kwafen jaridar Aminiya duk mako.
Daga Ahmad Zariya.

Ga Gwamna Ganduje
Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje muna mika kokon bararmu da ka yi mna gadar sama (Fly Ober) a Dangi. Hakika muna bukatar a yi mana gadar sama a randabawul (round about) na Dangi domin rage cunkoso abubuwan hawa. Allah Ya taimaki Gwamna da masu bashi shawarwari, amin.
Daga Musa Mohammed Hotoro APC Sak

Ga ’yan Najeriya
Salam Edita, ina kira ga ’yan kasata Najeriya da mu cigaba da yi wa shugaban kasarmu Baba Buhari addu’a. Mun shaida adali ne mai son kasarmu ta cigaba. Allah Ya kara masa basira da lafiya da kuma tsawon kwana.
Daga Abubakar Sodangi Kalfun-Kalfu, Majaloisar Tarayya Abuja.

Ruwa ba ya tsami banza!
Salam Aminiya Hausa. A gaskiya cece-ku-cen da ke faruwa a majalisar tarayya ruwa ba ya tsami banza. Ya kamata gwamnatin tarayya tayi kokari ta gano bakin zaren warware wannan matsalar domin a gudu tare a tsira tare.
Daga Alhaji Umar 4eber Gashua 08108003333

Jinjina ga Aminiya
Salam, Edita ka ba ni dama domin in yaba wa jaridarku mai farin jini, mai dauke da labarai masu kayatarwa musamman shafin wasanni na Ahmed Garba Mohammed. A gaskiya muna jin dadin yadda ake zakulo mana labaran wasanni masu dadi. A wasu lokuta a Aminiya ne kadai muke ganin wadansu labaran wasanni da ba kasafai muke ji ko ganinsu a wadansu kafafen watsa labarai ba.
Daga Sani Muhammad Shokin, 08165280193

Jinjina Ga Buhari!
Hakika yunkurin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake na kwato dukiyar al’umma ya yi daidai.
Daga Maccido Arzika, Jihar Sakkwato 07036938062

Allah wadai da masu auren jinsi
Assalamu Alaikum, Allah Ka ganar da batacce, shugaba Robert Mugabe a cigaba da tona tsakuwa don aya ta ji tsoro.
Daga Mamman Muhammad Jidda Sharada Kano.