Cuwa-cuwar IPPIS: ICPC za ta hukunta ma’aikata 3,657
Akalla ma’aikatan gwamnati 3,657 ne aka kai karar su ga Hukumar Yaki da Rashawa da Sauran Laifuka Mai Zaman Kanta (ICPC) don a hukunta su saboda rashin kin shiga Tsarin Biyan Albashi na Bai Daya (IPPIS). Da take sanar da hakan, Shugabar Ma’aikatan Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ta ce an gano ma’aikata 1,618 da suka yi […]
Akalla ma’aikatan gwamnati 3,657 ne aka kai karar su ga Hukumar Yaki da Rashawa da Sauran Laifuka Mai Zaman Kanta (ICPC) don a hukunta su saboda rashin kin shiga Tsarin Biyan Albashi na Bai Daya (IPPIS).
Da take sanar da hakan, Shugabar Ma’aikatan Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ta ce an gano ma’aikata 1,618 da suka yi amfani da wasikun daukar aiki na bogi, sannan an dakatar da wasu 874 daga tsarin IPPIS.
- Kotu ta daure wani matashi shekara 1 kan satar waya a Kano
- Buhari na duba yiwuwar biyan tallafin mai na N6.7trn a 2023
Ta shaida wa ’yan jarida a Abuja ranar Alhamis cewa ma’aikata 61,446 daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban ne aka tantance a tsarin na IPPIS.
A cewarta, albarkacin amfani da IPPIS, gwamnati ta samu rarar miliyan N180 a duk wata, kimanin Naira biliyan biyu a shekara.
Folashade ta ce hatta malaman jami’o’i tsarin IPPIS zai iya daukar su, maimakon tsarin UTAS da suke so a bari su yi amfani da shi wanda bai riga ya tabbata ba.