Da a ce yadda shugabannin Arewa suka tashi tsaye haka na Kudu maso Gabas suka tashi da ba a kai ga haka ba

  Da a ce masu fada ajin shiyyar Kudu maso Gabas din kasar nan, shiyyar da ta kunshi jihohin Anambara da Abiya da Ebonyi da Enugu da Imo, jihohin da su ne na `yan kabilar Ibo, sun mayar da hankali tun a ranar 14-07- 2015, lokacin da shugaban kungiyar tabbatar da kasar Biyafara Mista Nnamdi […]

Da a ce yadda shugabannin Arewa suka tashi tsaye haka na Kudu maso Gabas suka tashi da ba a kai ga haka ba
Da a ce yadda shugabannin Arewa suka tashi tsaye haka na Kudu maso Gabas suka tashi da ba a kai ga haka ba

 

Da a ce masu fada ajin shiyyar Kudu maso Gabas din kasar nan, shiyyar da ta kunshi jihohin Anambara da Abiya da Ebonyi da Enugu da Imo, jihohin da su ne na `yan kabilar Ibo, sun mayar da hankali tun a ranar 14-07- 2015, lokacin da shugaban kungiyar tabbatar da kasar Biyafara Mista Nnamdi Kanu ya kaddamar da tashar Radiyonsa (daga wata kasar Turai), da ya sanya wa suna MURYAR BIYAFARA, da bayan ba da belinsa da wata babbar kotun tarayya ta yi a ranar 25-04-17, bayan ya shafe sama da shekara daya da rabi yana fuskantar zargin cin amanar kasa da neman a raba kasar, kamar yadda shugabannin Arewa suka yi bayan gamayyar kungiyoyin matasan Arewa sun ba `yan kabilar Ibo mazauna Arewa wa`adin 1 ga watan Oktoba mai kamawa da su tattatara yanasu-yanasu su bar Arewa, har suka shawo kansu suka janye waccan barazana, to kuwa hayaniyar da aka shiga a kasar nan a tsakanin ranaikun Talata zuwa Juma`ar makon jiya da ba a shige ta ba.

Amma sai masu fada ajin na shiyyar Kudu maso Gabas suka yi biris da Kanun, a gefe daya ma an ta zargin wasunsu suna taimaka masa da goyon baya iri-iri da tsammanin hayaniyarsa za ta kai fagen hakarsu ta cimma ruwa wajen samun manya-manyan madafun iko da ayyukan raya kasa a shiyyar ta su, bisa ga koke-koken da suke ta yi na Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da su saniyar ware, ba ta yi musu komai, kuma ba ta yin komai da su.

Shugabannin na shiyyar Kudu maso Gabas, ba su fara magantuwa ba da babbar muryar da kasa za ta shaida da gaske suke kuma ba sa tare da Mista Kanu da kungiyarsa ta IPOB, balle aikace-aikacenta, sai a tsakanin Talata zuwa Juma`ar makon jiya, bayan rikici ya barke, shiyyar ta nemi kamawa da wuta. Shaidun gani da ido sun fada wa manema labarai cewa rikici ya barke a unguwar Afara Ibeku da ke garin Umuahia, lokacin da sojojin da suke sintiri a garin na Umuahia, bayan sun gangaro waccan unguwa da gidan su Mista Kanu yake cikinta, sai suka ci karo da gungun wasu matasa `yan kungiyar IPOB, da suka tare hanyar, kafin ka ce kwabo, an ce matasan sun fara jifar sojojin da duwatsu da fasassun kwalabe da sauran makamai, abin da ya sa sojojin suka yi harbi a sama, suka tarwatsa matasan. Rahotonnin waccan taho mu gama da aka yi, sun tabbatar da cewa an jikkata wata mata da take kan hanyar wucewa da kuma wani soja mai suna Kofur Kolawole Mathew.

Farkon barkewar rikicin da ya watsu zuwa wasu shiyoyin Kudu maso Gabas din da Kudu maso Kudu, irin su Fatakwal, da Jihar Delta, inda aka yi zargin an kashe wasu mutane hudu, ciki har da wata mace. A Jos babban birnin Jihar Filato da ke cikin shiyyar Arewa ta tsakiya, inda aka dan samu tashin hatsaniya bisa ga zargin neman daukar fansa, bayan da aka rinka baza jita-jitar cewa an kashe `yan Arewa a shiyyar Kudu maso Gabas din. Ana  kyautata zaton an kashe mutum daya a Jos din, sai da ta kai Gwamnan jihar Mista Simon Lalong ya kafa dokar takaita zirga-zirgar jama`a.

Bayan barkewar tarzomar kungiyar gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas din sun yi wani taron gaggawa a Enugu, inda suka ba da umarnin haramta kungiyar ta IPOB da aikace-aikacenta a dukkan fadin jihohin shiyyar biyar, bayan sun ji cewa Hedkwatar tsaro ta sojojin kasar nan ta bayyana kungiyar ta IPOB, da cewa kungiyar `yan ta`addace, bisa ga irin miyagun makaman da ta bayyana tana amfani da su. A wancan taro kungiyar gwamnoni ta nemi gwamnatin tarayya da lallai ta janye sojojin da ta jibge a shiyyar ba tare da bata lokaci ba.

Amma kuma kwana daya bayan wancan taro, a wani taron manema labarai da ya sake yi a ofishinsa da ke Abakaliki babban birnin Jihar Ebonyi, gwamnan jihar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar, Cif Dabe Umahi, ya bayyana cewa sun haramta IPOB, ce, ganin ta kauce daga manufofin da suka sa aka kafata na ainahi, wato gwagwarmaya cikin lumana, ta yadda za a rinka damawa da `yan kabilar Ibo cikin harkokin tafiyar da kasar nan, sannan kuma ga shi ta fara kawo koma baya cikin harkokin zuba jari da kasuwanci na shiyyar. Gwamnan Ebonyin ya kuma fadi cewa yanzu sun samu cikakkiyar shaida da take tabbatar da cewa `yan kungiyar ta IPOB, su, suka fara kai farmaki ga sojojin, sabanin rahotannin baya da suka nuna masu akasasin hakan. Shi kansa mahaifin Kanu, wanda kuma shi ne Basaraken yankin, Eze Israel Kanu, duk wannan abu da ake bai yarda dansa yana da laifi ba, ballantana ya tsawata masa. Don kuwa Eze Kanu ya fada wa manema labarai cewa kutsen da sojoji suka yi a fadarsa marar dalili ce, kuma mai firgitarwa, har ya kara da cewa dansa bai aikata wani laifi ba da har zai bukaci sojoji su kutsa kai cikin fadarsa ba.

Mai karatu wannan tufka da warwara da na iya kawowa da wadanda ma ban iya kawo wa ba, saboda karancin fili ta shugabannin `yan kabilar Ibon za ta iya tabbatar maka da zargin da Ministan Yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya yi a wani taron manema labarai a Abuja karshen makon jiya, cewa wasu da ya kira barayin kasar nan da gwamnatin take yaka, su ke amfani da irin kudin da suka sata don ganin ta  kowane hali sai sun kunyata Gwamnatin Shugaba Buhari, su ke iza Mista Kanu da `yan kungiyarsa na su tada fitina don kasar nan ta  yamutse, gaskiya ne.

Sanin kowane shugabannin Arewa kama daga kan gwamnonin jihohi zuwa Sarakunan da Maluman manyan addinan nan biyu da kungiyoyinsu da sauran masu fada aji na jihohin, duk sun tashi haikan ba dare ba rana wajen yin kiraye-kiraye da addu`o`i da hudubobi ga mutanensu akan su zauna lafiya, kar su kuskura su dauki fansa, a kan mutanen kudancin kasar nan, musamman na shiyyar Kudu maso Gabas da suke zaune a ko ina a Arewa.

kokarin da gwamnan Jihar Barno kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa Alhaji Kassim Shattima ya yi na ganin lallai sai gamayyar kungiyoyin matasan Arewa su janye  wa`adin 1 ga watan Oktoba mai kamawa da irin yadda a ranar Litinin da ta gabata ya jagoranci ayarin takwarorinsa na jihohin Kebbi da Katsina da Sakkwato da Filato, wajen kai ziyara ga wasu gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas da na Kudu maso Kudu da shugabannin al`ummomin `yan Arewa mazauna wadancan shiyyoyi da sunan a zauna lafiya, duk sun nuna irin yadda Arewa ta ke son a zauna lafiya. Da a ce tun farko su ma gwamnoni da shugabannin wadancan shiyoyi, sun nuna haka cikin tsawata wa Kanu da mabiyansa, to kuwa da ba a kai inda aka kai ba yanzu. Duk da haka ba su makara ba, yanzu ya kamata su kara tashi tsaye, rashin tashinsu zai   tabbatarwa da `yan kasar nan da ma duniya baki daya, cewa ba su da sha`awar ci gaba da zaman kasar nan kasa daya.