Da alama Real Madrid za ta zura klwallaye masu yawa a raga – Gareth Bale
dan klwallon Real Madrid Gareth Bale ya ce da alama kulob din zai zura klwallaye masu yawa a raga a kakar wasa ta bana. dan klwallon ya ce duk da yake kulob din ya tashi canjaras (0-0) da kulob din Sporting Gijon a gasar rukunin La-Liga a ranar Lahadin da ta wuce, hakan ba zai […]
dan klwallon Real Madrid Gareth Bale ya ce da alama kulob din zai zura klwallaye masu yawa a raga a kakar wasa ta bana. dan klwallon ya ce duk da yake kulob din ya tashi canjaras (0-0) da kulob din Sporting Gijon a gasar rukunin La-Liga a ranar Lahadin da ta wuce, hakan ba zai hana kulob din lashe kofin da ma wadansu kofuna a kakar wasa ta bana ba. Hasalima dan klwallon ya ce yana da yaklinin kulob din Madrid zai zura klwallaye masu yawa a kakar wasa ta bana.
“A kullkum muna samun cigaba musamman wajen gane kanmu, kuma ina da tabbacin za mu zura klwallaye masu yawa a raga a kakar wasa ta bana. A gaskiya za mu rikla kai wa abokan hamayya munanan hari amma sai dai muna buklatar mu klarfafa ’yan klwallon da ke tsare mana baya. Duk da yake mun fara yin wasan farko ba tare da mun zura klwallo a raga ba amma ina da yaklinin za mu zura klwallaye masu yawa a gasar da ma a wadansu wasanni da za mu yi nan gaba”.
Daga nan sai dan klwallon ya klaryata rade-radin da ake bazawa cewa ya ji rauni a wasan. “Komai ya tafi daidai sai dai na dan samu matsala ce kurum a klafa amma tuni Likitanmu ya ce ciwon zai sabe kafin wasa na gaba”, inji Bale.