Da alama Shugaba Assad ne zai lashe zaben Siriya

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya kama hanyar samun nasara a zaben da aka gudanar ranar Talata, wanda kuma shi ne zaben farko da ’yan takara suke fafatawa tun fara mulkin jam’iyyar Ba’ath a kasar.Kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ruwaito cewa, an rufe rumfunan zabe a daren Talata kuma jami’an hukumar zabe sun fara […]

Da alama Shugaba Assad ne zai lashe zaben Siriya
Da alama Shugaba Assad ne zai lashe zaben Siriya

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya kama hanyar samun nasara a zaben da aka gudanar ranar Talata, wanda kuma shi ne zaben farko da ’yan takara suke fafatawa tun fara mulkin jam’iyyar Ba’ath a kasar.
Kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ruwaito cewa, an rufe rumfunan zabe a daren Talata kuma jami’an hukumar zabe sun fara aikin tantance yawan kuri’un da aka kada da yawan mutanen da suka yi rijista da ita don tabbatar da daidaito.
Wannan zaben shi ne na farko a kasar a cikin shekara 50. Duk da cewa a lokuta daban-daban a baya, Shugaba Assad da mahaifinsa Hafez suna kiran zaben jin ra’ayin jama’a ne don samun karin wa’adin mulki.
Amma mayakan ’yan tawaye da kasashen Yamma da kuma kasashen yankin tekun Fasha duk sun bayyana cewa zaben ba sahihi ba ne, domin wani bangaren kasar ne kawai yake karkashin ikon gwamnatin Assad. A dai dai lokacin da miliyoyin jama’a suka kaurace wa muhallinsu saboda rikici. Gwamnatin Amurka ta ce zaben abun kunya ne, kuma Assad bai da kimar gudanar da shi.
A ranar zaben, gidan talabijin din gwamnati ya nuna Shugaba Assad a lokacin da yake kada kuri’arsa tare da mai dakinsa, Asma, a wata makaranta da ke babban birnin kasar, Damascus kusa sa garin al-Malikiyah. Ya na dai takara ne da wasu ’yan takara biyu wato Maher al-Hajjad da kuma Hassan al-Nuri. kasashe kawayen gwamnatin Assad kamar su: Koriya ta Arewa da Iran da kuma Rash, su ne wadanda suka sa ido a zaben.