Da albashina nake taimakon al’umma – Barista Kaloma Mustapha
Ka gabatar da da kanka? Suna na Kaloma dahiru Mustapha, dan takarar Majalissar Wakilai a Jam’iyyar APC kuma Mai bai wa Gwamna Shawara kan harkokin gwamnati da gwamnati . Jam’iyyar APC ta ce a gudanar da zaben fid-da-gwani ’yar tinke, a matsayinka na dan jami’yya kuma dan takara yaya kake kallon al’amarin? Ni na soki […]
Ka gabatar da da kanka?
Suna na Kaloma dahiru Mustapha, dan takarar Majalissar Wakilai a Jam’iyyar APC kuma Mai bai wa Gwamna Shawara kan harkokin gwamnati da gwamnati .
Jam’iyyar APC ta ce a gudanar da zaben fid-da-gwani ’yar tinke, a matsayinka na dan jami’yya kuma dan takara yaya kake kallon al’amarin?
Ni na soki lamirin zaben ’yar tinke. A ganina an makara saboda zaben ’yar tinke al’amari ne da yake bukatar lokaci da kayan aiki. A ganina da a ce lokaci ’yan Najeriya da su kansu ’yan siyasa da shugabanin jam’iyya sun tsara kimanin wata shida baya kafin zaben amma yanzu rana-tsaka a ce za a yi zaben babu wani shiri, gaskiya an makara.
Ina tabbatar maka babu magudi a cikinsa amma inda matsalar take wannan katin na jam’iyya ba ya da wani tsaro domin kowa na iya shiga daki ya buga ya raba wa mutanen da yake bukata idan haka ne kuwa babu yadda za ka hana yin magudi.
Ta yaya za a yi magudi bayan abin a file yake?
Kamar yanzu a halin da ake ciki jihohi da yawa suna da matsala sakamakon sauya sheka da wadansu ’ya’yan jam’iyyar suka yi zuwa wata jam’iyyar. Wadanda suka bar jam’iyyar da iyayensu za a iya amfani da su a matsayin sojojin haya wajan zaben fid-da-gwani na ’yar tinke kuma hakan na iya haifar da rigima.
Da me kake amfani wajen tallata kanka a siyasa?
Daga lokacin da na zama Mai ba Gwamnan Jigawa shawara har yanzu ban taba daukar kwabo daga albashina ba, na ajiye ne ina tallafa wa jama’a ta hanyar bai wa mata da matasa jari. Na bude gidauniya, inda na fara da Naira miliyan 20 domin taimakon mutane marasa galihu.
Mutum nawa suka amfana da gidauniyar taka?
Wannan gidauniyar ta agaza wa mata sama da 440 masu kananan sana’o’in hannu a daukacin mazabun siyasa 22 da ke yankin babura da Garki inda na ba wasu Naira 5000 zuwa 10,000 bisa la’akari da irin sana’ar. Sai guragu 20 da aka ba keke. Daga fara ba da tallafin na kashe sama da Naira miliyan 5 wajen tallafa wa mutanen. Yanzu haka gidauniyar ta ta samar da kananan masana’antu a yankuna biyu da nufin tallafa wa matasa kuma yanzu haka gidauniyar tana shirin samar da gonakin noman rani domin tallafa wa matasa a aikin gona inda za a haka rijiyoyin da za su rika amfani da su wajen noman rani.
Ka yi batun noman rani, kamar hekta nawa aka ware kuma rijiyoyi nawa aka tona domin aikin?
Tuni muka ware fili kuma aka samar da rijiyoyi a cikin daji, wanda a karshen wannan daminar idan rani ya fara za mu debi matasa mu raba musu gonakin da akwai rijiya domin su rika yin noman rani da nufin inganta rayuwarsu.