Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
El-Rufai ya ce yana yawan tuntuɓar Buhari kafin ɗaukar kowane irin mataki game da siyasarsa.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya fice daga jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
- ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina
- ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja
Ya ce bai gamsu da yadda ake tafiyar da APC ba cikin shekaru biyu da suka gabata.
Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya sanar da Buhari kafin ya fice daga APC.
“Na faɗa masa game da shawarar da na yanke a ranar Juma’a. Ina yawan tuntuɓarsa kan harkokin siyasata,” in ji shi.
El-Rufa’i ya kuma tuna cewa lokacin da yake gwamna, ya taɓa miƙa wa Buhari jerin sunayen kwamishinonin da zai naɗa domin ya duba su, don tabbatar da cewa babu wanda ya taɓa zaginsa.
Da aka tambaye shi ko yana da shugabannin siyasa da yake bi, El-Rufa’i ya ce, “Ina da mutanen da nake tuntuɓa kafin na yanke hukunci, kuma Buhari shi ne na farko a cikinsu.”
Game da ko yana nadamar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sai ya ce, “Ba na nadama, amma wasu abubuwa sun ba ni mamaki.
“Na goyi bayan Tinubu ne saboda wasu shugabannin Musulmi na Yarbawa sun faɗa min cewa an mayar da su saniyar ware a siyasa, kuma na yi imanin cewa dole a bai wa Kudancin Najeriya mulki domin yin adalci da daidaito.”