Da arzikin garin wasu…

Manyan kasashen nahiyar Turai da Amurka sun yi alkawarin taimakawa Shugaba Muhamadu Buhari kwato dukiyar kasar nan da aka ce wasu jami’an gwamnatocin da suka shude sun sassace, sun tsibe a can, kamar yadda kasar Siwizilan ta maido da wasu kudi har Naira miliyan dubu 65 da aka yi zargin tsohon Shugaban kasa, Janar Sani […]

Da arzikin garin wasu…
Da arzikin garin wasu…

Manyan kasashen nahiyar Turai da Amurka sun yi alkawarin taimakawa Shugaba Muhamadu Buhari kwato dukiyar kasar nan da aka ce wasu jami’an gwamnatocin da suka shude sun sassace, sun tsibe a can, kamar yadda kasar Siwizilan ta maido da wasu kudi har Naira miliyan dubu 65 da aka yi zargin tsohon Shugaban kasa, Janar Sani Abacha ya sace, ya boye a kasar, kuma tsohuwar minista a zamunan Cif Olusegun Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan, watau Ngozi Okonjo Iweala ta ce an zuba su cikin kasafin kudin shekarun 2004 da kuma  2005,  an kuma yi wasu ayyukan ciyar da kasa gaba da su  sa’annan kuma  talakawa ba su gasgata haka ba, domin ba su gani a kasa ba.
Haka nan kuma Shugaba  Muhammadu Buhari ya yi wani furuci, a kasar Iran, yana cewa, wasu manyan jami’an Gwamnatin Goodluck Jonathan, wadanda suka yi rub da ciki bisa dukiyar jama’ar kasar nan, da wadanda suka sassace ta, suka tsibe ta a bankunan kasashen ketare, sun ga haza, sun fara komowa da ita zuwa asusun Babban Bankin Najeriya, bakinsu kanin kafarsu. Hakan ya tayar da kura, ana ta ka-ce-na-ce a ko’ina a fadin tarayyar kasar nan.  Wasu na cewa a tona asirin wadanda suka fara maido da kudin, wasu na cewa, a bari tukuna sai sun kammala dawowa da su, sa’annan idan an gurfanar da su gaban alkali, sai dubunsu ta cika.
Shugaba Buhari, wanda ya yi wannan bayanin da zuciya guda, yana mayar da martani ne ga wadanda ke ganin cewa har yanzu babu wani abin da ya wakana game da hukunta wadanda suka handame dukiyar jama’a tun bayan hawansa mulki, watanni shida da suka shude, kuma hakan ya nuna ke nan  cewa, bai nakalci tsananin bukatar jama’a na ganin an gaggauta daukan matakan yin haka ba, musamman ma a tsari irin na dimokuradiyya. A ganin ‘yan Najeriya dai tilas ne Shugaba Buhari ya fahimci cewa, yana aiwatar da wannan yakin ne a madadin jama’ar Najeriar da aka sassace wa dukiya, saboda haka nan wajibi ne ya yi masu cikakken bayani game da halin da ake ciki dangane da kokarinsa na kwato masu hakkinsu da aka wafce. Wai shin  su wane ne ne ma suka sassace dukiyar har hakan ya kai ga kuntata wa bayin Allah, suke kuma maido da ita a boye?
Hakkin Shugaban kasa, Muhamadu Buhari ne ya yi amfani da hukumomin gwamnati  da suka dace domin gano ainihin yawan dukiyar da aka sassace da kuma wadanda suka yi sanadiyyar salwantarsu. Bai kamata ba a ce za a kyale barayin dukiyar su ce ga yawan dukiyar da za su maido, kuma a lokacin da suka ga damar yin hakan ba. Sanin kowa ne dai almubazzaranci da dukiyar jama’a, ko kuma wadaka  da ita haramun ne, kuma dole ne a hukunta wanda aka samu da aikata haka, ko shi wane ne, kuma ko dan wa. Babu wanda ya fi karfin doka, kuma a  tsari irin na Muhammadu Buhari wanda duk ya yi, za a yi masa, saboda haka nan wanda duk ya debo da zafi, bakinsa. Ashe kuwa idan haka ne ya wajaba a hukunta wanda aka zarga da batun handamar dukiyar talakawa, ya kuma maido da wani kaso daga cikinta a kotuna. Don hakan ya hana wasu sha’war kwatawa nan gaba. Ta haka ne za a tabbatar ana yakar rashawa yadda ya kamata.
A nan ya kamata a nemi gwamnati ta yi bayanin asusun da ake cewa wadancan barayin dukiyar kasar nan na maido da kudin. Hakan shi ne mafi a’ala, domin kuwa a zamunan da suka shude an rasa inda kudin da aka ce wasu shugabannin kasar nan, sun jida zuwa ketare, aka ce kuma wai an maido su, ba a san inda suka shige ba, sun bi ruwa, ba su, ba labarinsu. Haka nan kuma ko a wannan marrar ma ai mun ji yadda aka zargi  wasu shugabannin hukumomin bincike game da  yadda suka yi rub da ciki bisa dukiyar da suka kwato daga hannun azzaluman da suka garkame.
A yanzu dai  babu abin da ya rage wa Shugaba Buhari game da tsare-tsarensa na magance matsalolin da ke janyo cikas ga habakar tattalin arzikin kasa, sai danko azzalumai, a gurfanar da su gaban shari’a, tun da dai ya rigaya ya kammala nannada ministoci da wasu manyan jami’an da za su taimaka masa, yana nan kuma yana shirin nada wasu mataimakan. Saboda haka nan tilas ya gwada musu cewa, ba fa zai sassauta kwazonsa na yaki da rashawa da zalunci ba, zai ci gaba da yi musu jagora game da haka don dakile dukkan kafofin aikata almundahana  a ma’aikatunsu, da kuma tona asirin wadanda suka tattafka ta’asa kafin zuwan gwamnatinsa. Hankoron da ake yi na tsabtace tabargazar da manayan jami’an gwamnatin da ta shude suka tattafka ba abu ne da za a zura wa Shugaba Buhari ido don ya aiwatar shi kadai ba, hakkin kowa da kowa ne ya taimaka a kai ga nasara,  domin idan ta yi kyau gaba daya ne za a dara, idan kuma ta baci, kowa da kowa zai ji a jikinsa.
Dangane da haka, wajibi ne ‘yan Najeriya su tashi haikan wajen yi wa kasarsu hidima, ta hanyar kulawa da sanya idanu kan abubuwan da ke wanzuwa a tsakaninsu. A game da haka ne kuma ake kira ga dukkan wadanda suka bayar da gudummawa don kafuwar gwamnatin Buhari , a ko ina suke a fadin Najeriya, da su daddage ainun wajen ba shi gudummawa ta yadda zai samu sukunin kwato dimbin dukiyar da aka tsibe ta a wuraren da take agazawa ci gaban tattalin arzikin wadancan kasashen, tamu kasar da jama’arta kuma na kara nutsewa cikin koramar fatara da talauci. Babu abin da zai fi faranta wa talakawan Najeriya rai illa a ce ga shi can ana ta daddaure mahandaman dukiyarsu, ana kuma kwato ta ba kakkautawa, har an fara yin ayyukan da za su daga martabar kasar da inganta rayuwar al’ummomin cikinta da ita. Ai da arziki a garin wasu, gara a garinmu.