Da bahaushe Buhari zai fafata a shekarar 2019 – Babatope

Wani wakili a Kwamitin Amintattu Jam’iyyar PDP ta kasa Cif Ebenezer Babatope, ya ce Shugaba Goodluck Jonathan ba zai tsaya takarar a zaben shekarar 2019 ba, inda ya ce jam’iyyar za ta nemo dan takara Bahaushe ko Bafulatani don fafatawa da Janar Muhammadu Buhari a zaben na shekarar 2019 in Allah Ya kai mu. Cif […]

Da bahaushe Buhari zai fafata a shekarar 2019 – Babatope
Da bahaushe Buhari zai fafata a shekarar 2019 – Babatope

Wani wakili a Kwamitin Amintattu Jam’iyyar PDP ta kasa Cif Ebenezer Babatope, ya ce Shugaba Goodluck Jonathan ba zai tsaya takarar a zaben shekarar 2019 ba, inda ya ce jam’iyyar za ta nemo dan takara Bahaushe ko Bafulatani don fafatawa da Janar Muhammadu Buhari a zaben na shekarar 2019 in Allah Ya kai mu.

Cif Babatope, wanda har ila yau wakili ne a kwamitin dattawan jam’iyyar ya bayyana haka ne a Legas lokacin da yake ganawa manema labarai a Legas a shekaranjiya Laraba.
Ya bayyana Shugaban kasa mai barin gado a matsayin jagora wanda ya yi bakin kokarinsa wajen daukaka martabar dimokuradiyyar kasar nan,inda ya ce Najeriya za ta ci gaba da tunawa da Jonathan a matsayin shugaba mai sadaukarwa da ya tabbatar da kasancewarta kasa daya duk da dimbin matsalolin da ke akwai.
Mai shekara 72, Babatope wanda tsohon Ministan Sufuri ya ce Shugaban kasar ba zai nemi tsayawa takara a zaben Shugaban kasa na shekara ta 2019 ba. “Duk da mutanen Kudu maso Kudu suna da ’yancin su gabatar da dan takara a zaben, ina da tabbacin Shugaban kasar ba zai tsaya takara ba. Zai jagorance mu wajen fafatawa da Jam’iyyar APC. Shugaban kasar ya mayar da kansa wani babban jagora a Najeriya wanda sadaukar da kansa don ganin Najeriya ta zama babbar kasar dimokuradiyya. Ya aza harsashi ga dimokuradiyyar kasar nan kuma za a ci gaba da tunawa da shi har abada.”
Ya kara da cewa: “Shugaban kasar ba zai tsaya takara a zaben Shugaban kasa na shekarar 2019 ba. PDP za ta nemo dan takarar Shugaban kasa Hausa/Fulani (dan Arewa) domin fafatawa da Manjo Janar Muhammadu Buhari. Muna da karfi a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, kuma muna da gwamnoni biyu a Kudu maso Yamma. Za mu sake fafatawa a Arewa a zaben 2019. Za mu fatattaki APC a shekarar 2019 domin za mu gyara kura-kuranmu mu sake kwato Gwamnatin Tarayya.”