Da bindiga daya muke garkuwa da mutane a Jigawa – bingyal

Mataimakin shugaban matasan da ke garkuwa da mutane a yankin Basirka da ke karamar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa Abubakar Sani da ake yi wa lakabi da bingyal da ya shiga hannun ’yan sanda tare da wadansu abokan harkarsa uku ya ce da bindiga kwaya daya samfurin ribalba ta gargajiya da ake lankwasawa kuma take […]

Da bindiga daya muke garkuwa da mutane a Jigawa – bingyal
Da bindiga daya muke garkuwa da mutane a Jigawa – bingyal

Mataimakin shugaban matasan da ke garkuwa da mutane a yankin Basirka da ke karamar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa Abubakar Sani da ake yi wa lakabi da bingyal da ya shiga hannun ’yan sanda tare da wadansu abokan harkarsa uku ya ce da bindiga kwaya daya samfurin ribalba ta gargajiya da ake lankwasawa kuma take tashi kamar sau 10 da kuma sanduna da adduna da wukake suke aiwatar da aika-aikarsu.
bingyal ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a Dutse, inda ya ce idaa suka kama mutum ko ’ya’yansa sukan kai su ne wani kogon dutse a cikin daji a ksua da kauyen na Basirka su tsare su. “Da yake mu shida ne, uku suna kwana da wadanda muka yi garkuwa da su ne, su kuma uku daga ciki suna tafiya cikin gari su kwana su sayo mana abinci mu da wadanda muka yi garkuwa da su,” inji shi.
bingyal, ya ce shugabansu ya gudu tare da makamansu da suke fashi da yin garkuwa da mutane da su.
Ya ce suna tare hanya ne ko daji inda Fulani suke yin kiwon shanu su kama yara su buaaci iyayensu su kawo musu fansa ta makudan kudi kafin su saki yaran ko kuma su yi wa rigar Fulani da suke zaton suna da kudi su yi musu fashi kuma su tafi da iyalansu ko har sai an kawo musu wasu makudan kudi.
 bingyal ya ce idan suka yi garkuwa da mutanen sai su dawo cikin gari su wuni da wadanda aka yi garkuwa da danginsu, haka suke yi har sai an kai fansar.
Ya ce, babu wanda yake saka su face shugabansu mai suna Isa Abdu wanda yanzu haka ’yan sanda suke nemansa. Ya ce babu abin da suka sani da ya wuce kiwon shanu.
Ya ce akwai wani mai suna Umar wanda shi ma ya gudu, yana cikin wadanda suka koya  musu wannan muguwar harka ta yin garkuwa da mutane.
Sai ya nemi afuwar ’yan sanda da alkali kan su duba karancin shekarunsu su yi musu sassauci wajen yanke musu hukunci.
Shi kuwa Sani Alhaji Amadu ya ce idan suka yi garkuwa da mutanen ko fashi da makami, Isa Abdu yana ba su abin da ya ga dama ne ya kwashe sauran kudin kuma babu wanda ya isa ya yi musu. “Kuma ana raba kudin ne bisa girma-girma kuma ya danganta da irin rawar da mutum ya taka wajen bayar da bayanai kan wanda aka yi garkuwa da shi ko aka yi masa fashi,” inji shi.
Sani Amasu ya ce shugaban nasu bai fada musu inda ya samo makaman da yake ba su suna aikata fashi da garkuwa da mutanen ba, kuma ya ce a iyaka saninsa bindiga daya suke amfani da ita ita ma shi ne yake rikewa su kuma su dauki wukake da adduna da sanduna su tsare hanya ko shiga gidajen mutane su yi musu fashi.
Sani Amadu, ya ce bai san wannan muguwar harka ta garkuwa da mutane ba, sai da Isah Abdu ya saka su a ciki, kuma sau daya aka yi da shi, ita ce wannan da ta tashi bayan sun yi fashi a wata rugar Fulani suka kama yara suka tafi da su suka yi garkuwa da su.
Ya ce sun je cikin gari sayen abinci ne aka kama su asirinsu ya bayyana.
Kuma Naira dubu 250, suka samu daga iyayen wadansu yara da suka bukaci fansar Naira miliyan daya, amma kafin a kawo sauran kudin ne asirinsu ya tonu.
 Kakakin Rundunar ’Yan sanda, SP Audu Jinjiri ya ce gaskiya ne sun damke mutum hudu da ake tuhumarsu da laifin yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami kuma tuni suka gurfanar da su a gaban Kotun Majistare ta daya da ke Dutse, wadda ta tura su zaman jiran shari’a a gidan wakafi.
Ya ce Sani Alhaji Amadu yana zuwa ci-rani a Fatakwal kuma akwai alamun a can wajen ci-rani ya koyo wannan muguwar sana’a.