Da cin kadangare da ungulu na rayu a lokacin Yakin Basasa – Dokta Andy Iheme
Dokta Andy Iheme dan kabilar Ibo, tsohon soja ne da ya yi Yakin Basasa. Yanzu shi ne Daraktan Watsa Labarai na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya kwashe sama da shekara 40 a Arewa, inda a ya shaida wa Aminiya cewa lokacin Yakin Basasa da cin kadangare da ungulu ya rayu: Yaya […]
Dokta Andy Iheme dan kabilar Ibo, tsohon soja ne da ya yi Yakin Basasa. Yanzu shi ne Daraktan Watsa Labarai na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya kwashe sama da shekara 40 a Arewa, inda a ya shaida wa Aminiya cewa lokacin Yakin Basasa da cin kadangare da ungulu ya rayu:
Yaya rayuwarka ta kasance lokacin da kake karami?
Ina gani ina da sa’a tun ina karami domin ni ne na fara zuwa kasar Indiya daga cikin al’ummar garin Ebu a Karamar Hukumar Owerri ta Arewa a Jihar Imo, kuma mahaifina shi ne mutumin da ya fara zuwa kasar Ingila a 1958. Mahaifina tshohon ma’aikacin gwamnati ne. Garin Ebu gari ne mai muhimmanci da tarihi, shi ne gari na biyu bayan garin Onitsha da Turawan mishan mabiya Anglican suka je kuma a nan ne aka fara fassara littafin Baibul da harshen Ibo. Bayan da mahaifina ya koma Fatakwal da aiki ne na fara makarantar firamare. Daga nan muka tafi Legas daga na sai aka fara Yakin Basasa, sai muka sake komawa Fatakwal, daga nan aka mai da mahaifina aiki a Delta. Ya yi ritaya a lokacin mulkin Janar Sani Abacha a mukamin Manajan Tashar Jiragen Ruwa.
Kuma lokacin da mahaifina ya tafin Ingila ina dan shekara hudu a 1948, ina tuna abubuwan da suka faru da mahaifina ya dawo mutanen garinmu suka dinka riguna iri guda suka tarbe su suka yi musu liyafar girmawa. Gidanmu a Ebu tamkar tashar mota ce saboda gida ne na jama’a don mun kai sama da 21. A lokacin yaki na shiga sojan Biyafara ina dan shekara 14. Abin muka gani ba kyau, yaya za ka ji idan ka ga yaro dan shekara 14 yana dauke da bindiga?
Wadanne abububuwa kake iya tunawa sun faru da kai a lokacin yakin da bayan yakin?
Ina iya tuna cewa ni soja ne, an kashe wadansu daga cikin sojojin da muke tare da su, lokacin da muke tsakiyar yaki, wadansu kuwa sun samu manyan raunuka. Ba ma samun abinci lokacin da muke yakin, wani lokaci muna cin kadangare da ungulu da ciyawa don mu rayu a cikin daji. Yau idan na gan su sai in yi dariya amma na ci su a matsayin abinci, kuma na sha ruwan da yake a kasa. Nakan shafe sama da kwana hudu ko wanka ban yi ba. Bayan da yakin ya kare na dawo gida duk garinmu kowa ya watse ba kowa kafin daga bisani mutane suka fara dawowa, na ga gawarwakin wadansu mutane a zube. Ba abinci haka dai na yi ta fama har Allah Ya raya ni. Lokacin da mutane suka fara dawowa sai na ga suman wani abokina Saje Adewale Allah Ya ja kwanansa ya kara masa lafiya ko a ina yake, ta yi yawa sai na ce masa gashin kanka ya yi yawa bayan ka yi ta fada a daji in kana so sai in yi maka aski, sai na masa aski mai kyau. Shi ke nan sai na fara yi wa mutane aski. Haka na ta yi har na tara kudi na bude karamin shago don biyan bukatar sojojinmu da ke cikin mutanen garinmu. A lokacin babana yana so ya koma Legas mu kuma muna so mu koma makaranta ba kudi, da kudin wannan shago babana ya samu kudin da ya koma Legas, daga bisani ya sake samun aiki ya mai da mu makaranta dukkanmu. Bayan shekara uku da kammala yaki a wannan lokacin ne aka fara ba da shaidar kammala makaranta daga watan Nuwamba zuwa Yuni a 1973, an cire wata shida ke nan daga cikin manhajar karatu, sai aka soke jarrabawar da aka yi a Gabashin Najeriya. Hakan ya sa dole sai da na sake rubuta jarrabawa a 1974 kuma na samu kyakykyawar sakamako mai daraja ta daya.
Ka shafe fiye da shekara 40 a Arewa ko za ka bayyana kadan daga cikin yadda rayuwarka ta kasance?
Daga fari lokacin da na kammala karatu a jami’a a 1978 ina da wata ’yar uwa da ke aiki a Hukumar NYSC, ta tambaye ni a ina nake so in yi wa kasa hidima na ce a inda Allah Ya kai ni. Sai ya zamo an fitar da masu yi wa kasa hidima ba sunayenmu mu uku, daga bisani muka samu, sai aka tura ni gidan jaridar Daily Times. Na so yin aiki da jaridar amma lokacin da muka je ba su ba mu wajen kwana ba, sai muka je ofishin ’yan sanda da ke Obalande a Legas, daga nan sai aka ce ’yan sanda na neman kwararru da za su taimaka musu aikin jami’in hulda da jama’a a Kano da Benin da Ibadan. Ni aka fara danka wa takardar sai na zabi Kano. Na isa Kano ranar Alhamis duk da cewa ba wannan ne zuwata Arewa na farko ba, don na taba zuwa ina karami. Garin Kano nan na fara bude ido a Arewa. Washegari na je sayen kayayyakin abinci da ’yan abubuwan da nake bukata sai na ga mutane gaba daya sun taru jingim sun nufi wuri guda, sai gabana ya fadi, na ce kada dai wani abu ya faru, sai suka ce Masallacin Juma’a za su je, sai hankalina ya kwanta. Magana da Hausa ta ba ni wahala amma Hausawa mutanen kirki ne sun nuna mini kauna sun nuna mini halin girma da karamci, wannan hali ya sa na yi sha’awar zama a Arewa. Daga bisani a 1979 sai muka je muka neman aiki a gidan talabijin na kasa (NTA) da ke Maiduguri sai aka ce mu zabi inda za mu je tsakanin Maiduguri da Bauchi da Yola, za a dauke mu aiki a matsayin editoci duk da cewa lokacin ina ci gaba da yi wa kasa hidima. Sai na zabi Maiduguri, amma sai aka ce an fi bukatata a Bauchi sai aka aka turo ni Bauchi. Kuma ka ga a lokacin Allah Ya nufa a Arewa ne zan zauna na samu aiki. Na samu aiki a Legas da Enugu amma na yanke shawarar in zauna a Arewa duk da cewa wadansu mutanenmu sun nuna damuwa kan zamata a Arewa gani suke a 1979, shekara tara kawai da gama yaki suna gani Arewa wuri ne da bai kamata dan kabilar Ibo ya zauna ba. Na samu nasarori da dama a gidan talabijin na NTA a nan ne na san jama’a da dama, a nan ne ma na hadu da matata bayan ta gama yi wa kasa hidima a 1979, kuma mun yi aure da ita a 1982. Tun lokacin ina Arewa kuma ina jin dadin rayuwata, don akwai yanayi mai kyau da yara za su tashi cikin tarbiyya.
Wadanne kalubale ka hadu da su a zamanka a Arewa?
Babban kalubalen da na samu kuma ya tayar mini da hankali shi ne rikicin da aka yi a 1991 (a Bauchi). Wannan rikici ya girgiza ni kwarai da gaske. Na biyu kuma akwai wani lokaci da na nemi zama magatakardan wata jami’a a 2008, a wannan lokaci mu 12 ne muka nemi wannan kujera kuma na fi sauran samun sakamako mai kyau, washegari har mutane suna ta taya ni murna, can sai Shugaban Masu Tsaron Makarantar ya kira ni ya ce min in bar makarantar da gaggawa. Na ce me ya sa sai ya ajiye wayar, sai na ji hayaniya na kara yawa ya sake kirana ya ce in bar wajen don in tsira da lafiyata. Sai ga dalibai da wadansu malamai sun je suka ta da hankali a wajen taron Majalisar Gudanarwar Jami’ar don kada a amince a ba ni wannan mukami. Na yi mamakin yadda suka nuna mini kin jini don ni dan Kudu ne. Na yi mamaki daga baya da na samu kofe na takardar koken da aka yi a kaina na ga wadansu manyan malamai ne da kuma dalibai suka yi zarge ni kan abin da ba ni da iko a kai, don ba ni na zaba wa kaina in zama kabilar Ibo kuma Kirista ba, sun dai nuna mini tsana da kiyayya ne kawai. Amma Allah Ya sa komai ya wuce yanzu Bauchi gari ne mai dadin zama, ina son garin kwarai da gaske nan ne garin da arzikina yake. Idan ’ya’yana sun tafi hutu in suka ce za su koma gida suna nufin za su koma Bauchi. Batun rashin tsaro shi ne kawai matsalar da ke damun Arewa amma akwai zaman lafiya a nan sosai, lokacin da ’yata ta farko ta zo, tana auren Bature ne ba inda na yi tunanin in sauke su sai a nan Bauchi. Ka ga garin Bauchi ya zame min gida.
Ga shi kai dan kabilar Ibo ne kuma kana auren Bayarbiya yaya zaman takewarku take?
Na yi aiki a gidan talabijin na kasa na bar aikin cikin bacin rai kuma ba ni da wani aiki. Lokacin da na samu aiki da Kwalejin Koyon Sana’o’i ta Gwamnatin Tarayya da ke Bauchi, wata rana muna kallon labarai a talabijin a dakin saukar baki kawai sai ga mace kyakykyawa tana karanta labarai. Washegari muka je neman inda take, muka fara abota da ita muna tadin yadda aiki yake da sauransu, har lokacin da na ce zan aure ta. A lokacin iyayena sun gaji da zamata a Arewa sai babana ya turo mota a dauke ni ya mai da ni gida. Da mutumin ya zo sai ya ga Moji da ya lura da natsuwarta da nisan hankalinta da tarbiyyarta, sai ya koma gida ba tare da ya fada min abin da ya kawo shi ba. Ya ce wa mahaifina ya ga dalilin da ya sa ba zan koma gida ba. Don na samu mata sai iyayena suka ce in kawo ta gida. A lokacin kwalejin da nake sun ba mu rancen kudin sayen mota, na sayi mota kirar fijo 504, lokacin da muka je wadansu daga cikin magabatanmu suna ganin zai yi wuya mu yi aure, amma mu kuma muna godiya ga Allah yau shekararmu 37 muna tare mun yi ’ya’ya da jikoki. Ta tashi a Arewa ne a Jos. Lokacin da suka zo suka gan ni sai suka fashe da dariya na ce me ya sa suke dariya suka ce sun dauka tunda ni Ibo ne za su gan ni na daura zane amma ba su ga haka ba. Muna godiya don mahaifanmu suna da fahimta sosai.
Ko kana da wani da-na-sani a rayuwarka?
Eh! Na farko dai shi ne iyayena ba su more ni kamar yadda nake so su more ni ba. Na biyu kuma akwai ’yar uwata da ba ta da lafiya da nake so in samu isassun kudi in kai ta asibiti a kasar waje. Kuma daga cikin abubuwan da suka bata min rai a rayuwa akwai wannan soke jarrabawa da aka yi a 1973 don ran mutane da yawa ya baci. Sai batun neman zama magatakardan jami’ar da Allah bai sa na samu ba.