Da da uba
Da da uba Wani Bakano ne ya kira dansa da yake karatu a jami’a. Ga yadda hirarsu takasance: Baba: Musa, kana ina ne yanzu haka? Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance. Baba: Madalla! Na ji ana cewa dalibai suna ta zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kar ka kuskura ka bi su ka […]
Da da uba
Wani Bakano ne ya kira dansa da yake karatu a jami’a. Ga yadda hirarsu takasance: Baba: Musa, kana ina ne yanzu haka? Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance. Baba: Madalla! Na ji ana cewa dalibai suna ta zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kar ka kuskura ka bi su ka san dai irin tarbiyyar gidanku. Yaro: Idan Allah Ya yarda ba zan bisu ba baba.” Baba: Yauwa dan arziki sai an jima. Bayan minti 15, ya sake kiran yaron ya ce da shi: “Wai mene ne dalilin yin wannan zanga-zangar? Yaro: Wai saboda hukumar makaranta ta kara mana kudin makaranta daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 300. Baba: Iye! Yanzu kai kana ina? Yaro: Ina kwance a daki. Baba: Ashe kai mahaukaci ne? Tashi ka bi su!
Daga Malam Babaji Na Ummi Hadeja, 08108484300