Da dan gari akan ci gari
‘Yan Najeriya sun cika da mamaki matuka ganin yadda al’ummomin kudancin kasar nan suka yi ta yayata al’amarin da ba shi da tushe balle makama game da hare-haren da aka kai a garin Agatu a Jihar Binuwai da kuma Ukpabi Nimbo a Jihar Enugu, aka kuma dora laifin afkuwar haka kan Fulani makiyaya. Abubuwan da […]
‘Yan Najeriya sun cika da mamaki matuka ganin yadda al’ummomin kudancin kasar nan suka yi ta yayata al’amarin da ba shi da tushe balle makama game da hare-haren da aka kai a garin Agatu a Jihar Binuwai da kuma Ukpabi Nimbo a Jihar Enugu, aka kuma dora laifin afkuwar haka kan Fulani makiyaya. Abubuwan da suka bayar da mamaki game da haka kuwa suna da yawa, musamman ma ganin cewa tun fiye da shekaru aru-aru Fulani ke gudanar da harkokinsu a wadannan wuraren, ana kuma samun sabani tsakaninsu da manoma, mazauna yankunan, musamman ma saboda da ta’adin da ake cewa dabbobin makiyayan na yi wa amfanin da manoman suka shuka da kuma irin ramuwar gayyar da manoman ke yi wa Fulanin, ciki kuwa har da sassare dabbobinsu da kuma sanya guba cikin ruwan rafukkan da dabbobin makiyaya ke sha. Irin haka ya sha faruwa sau shurin masakI an kuma sha daukar matakan sasantawa, sakamakon haka kuma ana samun salama da zaman lafiya.
To, amma a ‘yan shekarun baya sai dangantaka tsakanin Fulani makiyaya da kabilun manoman da a kan kiwata dabbobin a yankunansu ta fara tsami, musamman ma a yankunan Binuwe da Pilato, inda aka dinga sassare shanun Fulanii a dukkan wuraren da aka gan su suna kiwo, daga bisani kuma aka shiga sassace su, Fulanin na ji, suna gani, ana kai wa kasuwanni, ana sayarwa. Baicin haka nan kuma sai aka shiga kuntatan wa Fulanin, ana hana su ‘yancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su na kasancewa ‘yan kasa, alhali kuwa a nan ne aka haifi kakannin-kakanninsu. Abin har sai da ya zamanto ba su samun damar karbar magani a asibitocin hukuma, ba a daukar ‘ya’yansu a makarantun gwamnati, ba a kuma ba su damar karo ilmi a manyan makarantun gaba da Sakandare. Ba wani abu ne ba kuwa ya haddasa haka illa tsananin gabar siyasa da ta bayar da damar yin amfani da bambancin addini da kabilanci don muzguna musu.
Wannan ba sabon abu ba ne, kowa na sane da yadda aka yi ta gumurzu da Fulani a Jihar Pilato, ana muzguna musu, ana kyararsu, ana yi musu kisan gilla, amma sauran ‘yanuwansu, ‘yan Najeriya ba su yi ta karaji, suna kwarmato ba game da kisan gillar da ake yi masu, wanda hukumomi ba su hana ba, maimakon haka nan ma sai kara taimakawa suke yi a kaikaice, ana ta kassara su. Gwamnatocin Jihar Pilato da suka shude sun ki nuna damuwarsu game da mugun abin da ake yi wa Fulanii makiyaya, ba su kuma kafa kwamitin binciken yadda ake muzguna musu ba, ba a kuma dauki matakan hana tabarbarewar al’amarin ba, domin kuwa ba kabilun Jihar ne ake muzgunawa ba, Fulanin da ba a so ne ake takurawa.
Matsi da tsangwama da kuma kisan mummuken da ake yi wa Fulanin daji a sassan kasar nan da yawa, sun sa su daukan matakan kare kan su da dukiyoyinsu, tun da dai babu wata gwamnatin da ta damu da abin da ake yi musu. Wannan ne dalilin da ya sa Fulanin ke yawo da bindiga don tsorata masu sassace masu shanu, ko sassare su, ko kuma neman su halaka masu kulawa da su. Amma duk da haka nan masu kuntata musu ba su damu da haka ba, suna ci gaba da gallaza musu, har idan tura ta kai bango, sai su ma su yunkura don kare kawunansu. To, idan haka ya faru ba za a ga laifin wadanda suka tunzura su ba, sai dai na Fulanin ne za a gani, domin su ba su da galihu ko wani mai tsaya masu, sai Allah.
Ashe ke nan artabu, ko markabu tsakanin Fulani da makiyaya abu ne da ya kamata a dora laifin aukuwarsu kan dukkansu, ba a ware wani bangare ba, a yi ta tsangwamarsa, domin kuwa an ce karfe guda daya ba I yin amo, sai da abokin gaminsa. A yanzu ne dai da ake son tayar da wata gagarumar Fitina don a takurawa gwamnatin Muhamadu Buhari, a kawar da hankulan jama’a daga kyakkyawan aikin da take yi na maganin rashawa, sai aka nemi kawo wani rikicin addini da na kabilanci, inda za a yi amfani da wannan damar a bata dukkan kabilar Hausa/Fulani, a mayar da su abin kyama, ana masu kallon makasa da marasa kaunar zaman lafiya a fadin tarayyar kasar nan, don a ji dadin far masu da sunan ramuwar gayyar kashe-kashen da ake yi da sunansu.
Wannan ne dalilin da ya sa wani takadarin dan siyasa, Farfesa Wole Soyinka, wanda ya shahara wajen nuna bakar kiyayya ga dukkan wani dan Arewa da ke mulki ya ce wai Fulani na takama danuwansu ne ke bisa karagar mulki, shi ya sa suke kashe mutane ba kakkautawa, kuma wai a sabili da haka ne Shugaba Buhari ya ki daukar kwakkwaran matakin magance su ba a kan lokaci. Haka nan kuma wani babban jami’in kungiyar da ke neman farfado da kasar Biafura da ake kira MOSSOB, ya ce wai wasu dakarun Islama ne, hade da Fulanin da suke samun goyon bayan wadanda ke son murkushe ‘yan kabilar Ibo, suka kai hare-hare a kasar Inyamurai. Hakan ya nuna mana dalilan da suka sa aka kai harare-haren da ake dora wa Fulani da kuma wadanda suke son tayar da fitanar da za ta kai su ga biyan bukatunsu sakamakon haka.
Babu yadda za a yi a ce Fulanin daji da suka kasance ‘yan tsiraru a yankunan da ake cewa sun yi kashe-kashe, za su iya barin dabbobinsu, su kutsa cikin garuruwan manoma, su yi musu kisan gilla, su kuma yi ficewarsu, ba tare da an gane su ba, ba a kuma kakkame su ba. Ina manyan jami’an tsaro, da Gwamnan Jihar Enugu, da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar suke har aka kai wancan mummunan harin a Nimbo? Sakaci ne ya sa suka kyale, wasu suka kai harin, alhali rahotannin jami’an tsaro sun nuna musu cewa za a kai mummunan hari a garin? Ai an ce Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya yi wani taro da manyan jami’an tsaron jihar game da wannan rahoton, sun kuma karfafa masa gwiwa cewa, soja da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a shirye suke su magance dukkan abin da zai faru, to yaya aka yi har aka kai farmakin, alhali jami’an tsaro na shirye don gudun ko-ta-kwana?
Tsohon Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Enugu, Mista Nwodibi Ekechukwu ya fito fili ya nuna cewa, ba ruwan Fulani da wadancan munanan hare-haren da aka kai da miyagun makamai akan al’umman Akpabio Nimbo, amma sai aka muzanta shi. Watakila kulba ce ta yi barna ake cewa jaba ce. Haka nan kuma sauran jami’an tsaron sun nuna cewa kutsawa cikin dazuzzukan Jihar Enugu don kai irin wannan harin sai da wanda ya san dajin sosai, domin ai da dan gari ne akan cin gari.