Da daukar nauyin tafsiri da ciyar da mabukata, wanne al’umma suka fi bukata?
Azumin watan Ramalan na daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar da Allah (SWT) Ya umarci Musulmi da yi na adadin wasu kwanaki kayyadaddu.Gudanar da tafsiri a cikin watan na Ramadana ya zamo abu ne da ake gabatarwa a akasarin masallatan kasar nan da kasashen Musulmi, saboda irin tarin falala da yin tafsirin ke da shi […]
Azumin watan Ramalan na daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar da Allah (SWT) Ya umarci Musulmi da yi na adadin wasu kwanaki kayyadaddu.Gudanar da tafsiri a cikin watan na Ramadana ya zamo abu ne da ake gabatarwa a akasarin masallatan kasar nan da kasashen Musulmi, saboda irin tarin falala da yin tafsirin ke da shi ga al’umma. Baya ga tafsiri, akwai wata garabasa ga duk wanda ya ciyar da mai azumi kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar. Wannan ne ya sa wadansu ke ganin ciyarwa ta fi daukar nauyin tafsiri. Wakilan Aminiya sun zaga domin jin ra’ayoyin mutane, ga kuma abin da suke cewa:
Ciyarwa ta fi falala –Ustaz Tahir Zubairu
Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan
Ustaz Tahir Zubairu: “Daukar nauyin ciyar da mabukaci a cikin irin wannan lokaci na watan Ramadan ya fi muhimmanci fiye da daukar nauyin wa’azin tafsiri a masallaci. Domin idan ka ciyar da mutum daya a cikin wannan wata na Ramadan, to ka samu ladan mutumin da ya yi azumin yini daya, ba tare da an rage ladarka ba, ko ladansa. Saboda haka ciyarwa a cikin azumi ta fi muhimminci fiye da daukar nauyin tafsiri.”
Ciyar da mabukata ne mafi alheri –Danlami Mai Aya
Daga Hussaini Isah, Jos
Danlami Mai Aya da Dabino: ‘’Ciyar da mabukata ta fi a dauki nauyin tafsiri lokacin watan azumin Ramadan. Domin idan ba ka ciyar da mutum ba, ba zai fahimci karatu da tarbiyyar da za a koya masa ba. Don haka babban abu mafi mahimmanci shi ne a ciyar da mabukata maimakon a dauki nauyin karatun tafsiri lokacin azumin watan Ramadan. Ba a ce daukar nauyin masu tafsiri ba ya da kyau ba ne amma ciyar da jama’a shi ne ya fi alheri’’.
Tafsiri na da muhimmanci, amma –Jamilu Mai Kayan Kwalliya Kasuwar Wuse
Daga Muhammad Aminu Ahmad
Jamilu Mai Kayan Kwalliyya: Ni a ganina ciyarwa ta fi, domin za ka ga mutum ya fito daga gidansa, amma abin da zai bar wa iyalansa don su yi buda-baki, ya zama matsala gare shi. Al’umma sun fi bukatar ciyarwa, domin yanzu idan ka bai wa mutum Naira dubu zai yi murna sosai, saboda halin da muke ciki, domin zai taimaka wa iyalansa. Domin Allah Ya shigar da wata karuwa Aljanna don ta shayar da kare, to ka ga muhimmancin ciyarwa. Shi ma Tafsiri na da muhimmanci, to amma gara ciyarwa don ta fi lada”
Gara a ciyar da mabukata –Salisu Mai Kananzir
Daga Hussaini Isah, Jos
Alhaji Salisu Adamu Mai Kananzir: “Gaskiyar ciyar da mabukata a lokacin watan azumin Ramadan ne jama’a suke bukata, ba daukar nauyin masu tafsiri ba. Domin a halin da ake ciki mutane suna fama da rashin kudin da za su sayi abincin da za su ci. Kuma kowa ya sani idan mutum bai ci ba, ba zai samu damar sauraron karatu cikin natsuwa ba. Wannan shi ne gaskiyar magana. Don haka gara a ciyar da mabukata, maimakon a dauki nauyin tafsiri a rediyo ko talabijin lokacin watan azumin Ramadan. Amma idan mutum yana da hali, to ya ciyar da mabukata kuma ya dauki nauyin tafsirin yana da kyau.’’
Ciyarwa ta fi, idan aka yi lakari da halin da ake ciki – Abdullahi Kafinta
Daga Muhammad Aminu Ahmad
Abdullahi Kafinta: “A gaskiya ciyarwa ta fi muhimmanci a halin da muke ciki, a kasar nan. Domin idan kana fama da yunwa ko da ka je wajen tafsirin ba za ka fahimci komai ba, saboda hankalinka na tunanin idan lokacin buda-baki ya yi, me za ka ci? Don haka ni a ra’ayina ciyar da mutane shi ne babban abin da ya kamata masu hali a tsakanin al’umma su yi, maimakon daukar nauyin sa tafsiri a rediyo ko talabijin.”