DA DUMI DUMI: Anga Sabon jinjirin watan Shawwal
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi sanarwar ganin Sabon jinjirin watan Shawwal na Shekarar 1440 a wurare daban-daban da ke fadin kasar nan. Wuraren da aka ga watan sun hada da: Shehu Borno da Sarkin Gwandu Sarkin Jama’a a Kaduna da Sarkin Damaturu da Macina da Sarkin Nguru Yobe da Sarkin […]
Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi sanarwar ganin Sabon jinjirin watan Shawwal na Shekarar 1440 a wurare daban-daban da ke fadin kasar nan.
Wuraren da aka ga watan sun hada da: Shehu Borno da Sarkin Gwandu Sarkin Jama’a a Kaduna da Sarkin Damaturu da Macina da Sarkin Nguru Yobe da Sarkin Dutse a Jigawa da wasu garuruwa a jihar Sakkwato.
Sarkin ya ce, Sun samu rahoton ganin watan Shawwal ne, daga Sarakuna da shugabannin kungiyoyin addinin musulunci, wadanda kwamitin tantancewar duban wata na kasa da jiha suka yi su kuma suka aminta.
Mai martaba Sarkin Musulmi ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da ibadodi, tare da aiki da koyarwar addinin musulunci domin samun Zaman lafiya a cikin al’umma.
Haka kuma ya yi kira da a kaucewa kabilanci da nuna bambancin addini.