Da farko na raina Boko Haram – Shugaba Jonathan
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce ya raina da farko ya raina al’amarin kungiyar Boko Haram ne wadda take cin karenta babu babbaka a yankin Arewa maso Gabas, inda ya kare dage zaben kasar nan. Jonathan wanda ya bayyana haka a tattaunawa da jaridar Thisday ta ranar Lahadi yana fuskantar barazana daga babban abokin […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce ya raina da farko ya raina al’amarin kungiyar Boko Haram ne wadda take cin karenta babu babbaka a yankin Arewa maso Gabas, inda ya kare dage zaben kasar nan.
Jonathan wanda ya bayyana haka a tattaunawa da jaridar Thisday ta ranar Lahadi yana fuskantar barazana daga babban abokin takararsa Janar Muhammdu Buhari a kokarinsa na neman a sake zabensa karo na biyu.
Shugaba Jonathan yana kuma shan suka kan dage zaben inda masu suka suka ce an dage zaben ne domin a ba shi dama ya karfafa kamfe dinsa.
Sojoji ne suka nace sai an matsa da zaben zuwa mako shida kan yadda aka tsara zuwa ranar 28 ga Maris mai zuwa inda suka ce hakan zai ba su damar fuskantar mayakan Boko Haram ta yadda za a iya gudanar da zaben ba tare da matsala ba.
Shugaba Jonathan ya ce, “Hakika daga farko mu, ina nufin ni da mukarrabaina, mun raina karfin kungiyar Boko Haram din.”
Y ace, sojoji sun samu makamai da harsasai a baya-bayan nan don fafatawa da mayakan Boko Haram, inda ya sha alwashin murkushe su tare da kamo shugaban kungiyar cikin kankanen lokaci.
“Da yardar Ubangiji za mu kamo (Abubakar) Shekau kafin zaben,” inji shi. Da aka tambaye shi yaya mako shida zai bambanta da shekarun da aka dauka ana fafatawar da aka kashe dubban mutane, sai Jonathan ya ce sojoji za su samu nasara mai yawa a wannan lokaci.
“Ba muna cewa za mu gama da Boko Haram gaba daya don gudanar da zaben ba ne, amma za mu samu wata dama da ba za su iya jawo barna ba koda sun yi wani yunkuri,” inji Jonathan.
“Ina da yakinin nan da 28 ga watan gobe lokacin da za a gudanar da zabe, Boko Haram ba su da karfin da za su iya kai hari a wani gari da yardar Ubangiji.”
Babbar jam’iyyar adawa ta APC ta yi zargin cewa Jonathan da PDP na shirin fitar da wani jabun Shekau a yankurinsu na makala wa ’yan adawa musamman dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Janar Muhammadu Buhari alhakin daukar nauyin Boko Haram din.
Mahukutan sojin Najeriya sun ce sun kwato garuruwa da dama ciki har da garin Baga mai samar da mafi yawan kifin da kasar nan ke bukata, sai dai babu wata kafa da ta tabbatar da da’awarsu.
Fiye da mutum miliyan daya hare-haren Boko Haram y araba da muhallinsu tun fara fafatawa da su a shekarar 2009.