Da gangan Isra’ila ke kashe yara a Gaza — MDD
Rahoton ya kuma nuna cewa halin jin ƙai a Gaza na ci gaba da taɓarɓarewa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
FILE – Palestinians run for cover during an Israeli airstrike on a high-rise building in Gaza City, Friday, Sept. 5, 2025, after the Israeli army issued a warning. (AP Photo/Yousef Al Zanoun, File)
Wani bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta gudanar ya zargi hukumomin Isra’ila da jami’an tsaronta da kashe yara a Zirin Gaza da gangan, tare da bayyana hakan a matsayin wani shiri da ke barazana ga makomar Falasɗinawa.
Rahoton ya ce akwai ƙwararan hujjoji da ke nuna cewa jami’an tsaron Isra’ila na kai hare-hare kan yara ta hanyar amfani da makamai masu linzami, jirage marasa matuƙa da kuma harbin bindiga kai tsaye.
- An kafa dokar hana zirga-zirga a ƙananan hukumomi 10 na Oyo
- Majalisar Dattawan Amurka ta kaɗa ƙuri’ar haramta wa Trump yaƙi da Iran
A cewar binciken, yawan da tsananin hare-haren sun kai matsayin laifukan yaƙi, laifuffuka kan bil’adama da kuma abin da ya bayyana a matsayin kisan ƙare dangi da ke barazana ga rayuwa da makomar Falasɗinawa a Gaza.
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila ta yi watsi da rahoton, tana mai cewa zarge-zargen ba su da tushe kuma wani nau’in farfaganda ne, tare da jaddada cewa ƙasar na kare kanta ne daga hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Rahoton ya kuma nuna cewa halin jin ƙai a Gaza na ci gaba da taɓarɓarewa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Hukumomin MDD, ciki har da OCHA, sun ce al’ummar Gaza na ci gaba da fuskantar matsaloli masu tsanani na rayuwa, musamman a fannonin abinci da lafiya.
A cewar rahotannin, adadin motocin ɗauke da kayan abinci da magunguna da ke shiga Gaza ya ragu matuƙa, inda a halin yanzu motoci tsakanin 50 zuwa 60 ne kawai ke shiga a kullum, maimakon kusan motoci 600 domin biyan buƙatun al’ummar yankin.