Da gaske Buhari ya ce bai san an tube Sarkin Kano Sanusi II ba?

Wani shafin intanet mai suna exclusive103.com ya ruwaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari bai san da maganar tube tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ba daga gadon sarauta. Shafin, ya rubuta labarin da cewa: “Ban san cewa an tube Sarki Sanusi II ba, wane ne ya tube shi? – Buhari ya tambaya”. Sai dai babu wani […]

Da gaske Buhari ya ce bai san an tube Sarkin Kano Sanusi II ba?

Shugaba Buhari da Muhammadu Sanusi II

Wani shafin intanet mai suna exclusive103.com ya ruwaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari bai san da maganar tube tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ba daga gadon sarauta.

Shafin, ya rubuta labarin da cewa: “Ban san cewa an tube Sarki Sanusi II ba, wane ne ya tube shi? – Buhari ya tambaya”.

Sai dai babu wani karin bayani ko da layi daya da shafin ya rubuta a cikin labari in ban da kan labarin.

Jaridar Aminiya ta gano cewa har yanzu, bayan sama da sa’a 24 da tube sarkin daga gadon sarautar Kano, Shugaba Buhari bai ce komai ba, kazalika mukarrabansa ma ba su ce komai ba in ban da karyata wannan labari da suka yi.

Mai taimaka wa shugaban na musamman kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa a Twitter cewa, “Ku ji wannan kan labarin, labarin kanzon kurege ne tsagwaro”.

Bincike ya nuna cewa, masu yada labaran karya sun fi son yin jirkita wani labari na gaskiya zuwa na karya sama da kirkirar sabuwar karya fil, kuma dubban mutane kan yada su da gangan ko bisa rashin sani a shafukan sada zumunta.

Aminiya na kira ga mutane da su kula sosai da abin da suke karantawa a shafukan intanet sannan kuma su bi matakan tantance su kafin yadawa a shafukan sada zumunta.