Da gaske Lalong zai ajiye kujerar Minista don karɓar ta Sanata?
Shin zai sauka daga kujerar Ministan ne don ya hau ta Sanata?
Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka, Simon Lalong, a ranar Alhamis ya karɓi takardar shaidar lashe zaɓen Sanatan Filato ta Kudu a hedkwatar Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) da ke Abuja.
Lalong, wanda tsohon Gwamnan Filato ne har karo biyu, ya nemi kujerar ƙarƙashin jam’iyyar APC, a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, amma ya sha ƙasa.
- Legas na asarar tiriliyan 4 duk shekara sakamakon cunkoson ababen hawa
- Jami’an tsaro sun hana ’yan NNPP yin sallar neman nasara a Kano
INEC dai a lokacin ta ayyana ɗan takarar PDP, Napoleon Bali, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
To sai dai Lalong ya garzaya kotun sauraron ƙararrakin zabe, wacce ta soke wancan sakamakon, sannan a kwanakin baya kotun daukaka ƙara ita ma ta jaddada hukuncin.
Sai ga shi a ranar Alhamis, Lalong ya je hedkwatar INEC ta ƙasa tare da wasu makusantan shi, inda ta karbi takardar daga hannun Kwamishinan hukumar na ƙasa, Mohammed Haruna.
Bayan karbar takardar, Lalong ya wallafa sako a shafinsa na X (Twitter) da ke cewa, “Yau na karbi takardar lashe zabe daga hedkwatar INEC daga hannun Kwamishina Mohammed Haruna.”
Hakan dai na nuna akwai yiwuwar ya ajiye aikinsa na Ministan Ƙwadago, wanda dama yake ta fama da ƙalubale daga ƙungiyoyin ƙwadago.
Sai dai abin mamaki, a watannin baya takwaransa tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya ajiye kujerar Sanatan domin karɓar ta Minista.