Da ina da iko da cikin mako biyu zan magance matsalar tsaron Zamfara – Gwamna
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce da a ce yana da cikakken iko da jami’an tsaro, da zai iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar shi a cikin mako biyu.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce da a ce yana da cikakken iko da jami’an tsaro, da zai iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar shi a cikin mako biyu.
Gwamnan ya kuma ce ya san dukkan inda ’yan bindigar jihar suke buya.
Da yake jawabi a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, gwamnan ya ce babban kalubalen shi a yaki da ’yan bindiga a jihar shi ne rashin cikakken iko da jami’an tsaro.
- An ƙone ‘ɓarawon’ babur ƙurmus a Binuwai
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi
Ya ce shugabannin rundunonin tsaron da ke jihar suna karbar umarni ne kawai daga hedkwatocinsu da ke Abuja, bad aga wajen shi ba.
A cewar Gwamnan, “Na rantse da Allah na san duk inda wani shugaban ’yan bindiga yake a Zamfara, kuma duk inda ya fita ya je na sani.
“Yanzu da wayata zan iya nuna muku inda wadannan ’yan ta’addan suke a yau. Amma babu abin da za mu iya yi musu.
“Wallahi a yau da ina da iko da jami’an tsaro, ina mai tabbatar maka za mu iya kawo karshen ’yan bindiga a Zamfara cikin wata biyu.
“A lokuta da dama nakan zubar da hawaye ga mutanena ganin yadda matsalar take, amma ba ni da ikon da zan ba jami’an tsaro umarni su yi maganinta.
“Akwai lokacin da ’yan ta’adda suka taba kai hari karamar hukumar Shinkafi, kuma ina zaune a nan lokacin da aka ankarar da jami’an tsaro, amma suka ki zuwa saboda wai ba a ba su umarni daga Abuja ba. Wannan ce babbar matsalar da muka fuskanta, amma mun dogara ga Allah, zai kawo mana mafita.”
Gwamna Lawal ya ce amma duk da haka, gwamnatin jihar na ba jami’an tsaro tallafin kayan aiki da kudaden gudanarwa na yau da kullum, inda ya ce bayanan hakan na nan ga duk mai bukata.
Ya kuma ce ko a wata biyu da suka gabata, gwamnatin jihar ta raba motocin sintiri guda 150 ga jami’an tsaro na sojoji, ’yan sanda da DSS da kuma sibil difens domin su inganta ayyukansu.
Gwamnan ya kuma ce ya dauko hayar mafarauta sama da 2,000 daga jihohin Borno da Yobezuwa jihar domin tallafa wa kokarin jihar na yaki da ’yan fashin dajin.
Ya ce, “Ina yin duk wadannan ne duk da ba ni da cikakken iko da jami’an tsaro. Amma ina yi ne tun da hakkina ne na kare rayuka da dukiyoyin Zamfarawa a matsayina na babban jami’in tsaron jihar.
“Na sha fada cewa idan ’yan bindiga suna fada ne saboda ba su da muhimman abubuwan more rayuwa, zan samar musu da ko me suke bukata. Idan ruwa suke so, za mu ba su, idan makarantu ne, za mu gina musu, duk don a samu zaman lafiya,” in ji Lawal.
Gwamnan na Zamfara ya kuma ce duk da tarin kalubalen da gwamnatinsa ke fuskanta na yaki da matsalar tsaro, ba zai taba yin kasa a gwiwa ba, inda ya bukaci mutanen jihar da su kara hakuri saboda yana iya bakin kokarinsa na magance matsalar.
Sai dai ya koka da cewa babbar matsalar ita ce yadda ake siyasantar da harkar tsaron jihar, inda ya ce masu yin hakan jihar suke rusawa ba gwamnatinsa ba.
Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ya ce ko a yayin zaben cike gurbin da aka gudanar a jihar a kwanakin baya, an girke taron sojoji da sauran jami’an tsaro da kayan aiki a dukkan yankunan da aka yi zabe, amma ana kammalawa suka koma.
Jihar Zamfara dai na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ’yan bindiga da ke kasha mutane tare da sace wasu domin karbar kudin fansa.
Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka zama ’yan gudun hijira sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar.