Da jami’an gwamnati ake gudanar da ta’addanci a Zamfara – Bashir IMAD

Alhaji Bashir Adamu IMAD ya jima ana damawa da shi wajen kafa gwamnatoci a jiharsa ta Zamfara da kuma Jihar Sakkwato, sai dai a yanzu ya yanke shawarar neman kujerar Gwamnan Jihar Zamfara, ya kuma bayyana wa Aminiya dalilinsa na daukar wannan mataki: Aminiya: Wane ne Bashir IMAD?IMAD: Da farko sunana Bashir Adamu Gusau, wanda […]

Da jami’an gwamnati ake gudanar da ta’addanci a Zamfara – Bashir IMAD
Da jami’an gwamnati ake gudanar da ta’addanci a Zamfara – Bashir IMAD

Alhaji Bashir Adamu IMAD ya jima ana damawa da shi wajen kafa gwamnatoci a jiharsa ta Zamfara da kuma Jihar Sakkwato, sai dai a yanzu ya yanke shawarar neman kujerar Gwamnan Jihar Zamfara, ya kuma bayyana wa Aminiya dalilinsa na daukar wannan mataki:

Aminiya: Wane ne Bashir IMAD?
IMAD: Da farko sunana Bashir Adamu Gusau, wanda a kafi sani da suna IMAD, an haife ni a 1970 a garin Gusau ni dan Malam Adamu Bauchi da Hajiya Sa’a Adamu ne, na yi firamare a Sabon Fegi Gusau da Sakandare a danchadi da Kwalejin Kanta da ke Argungu, na samu digiri daga Jami’ar Usuman dan Fodiyo da ke Sakkwato a 1991, bayan nan na kama aikin banki a Legas, na ajiye aikin, na ci gaba da zama a can inda nake kasuwanci a yanzu.
Aminiya: Me ya ba ka sha’awar shiga siyasa har kake neman matsayin Gwamna?
IMAD: Abin da ya ba ni sha’awar shiga siyasa shi ne don na kawo sauyi, kusan ba abu guda da yanzu haka a ke gudanarwa a jihata ta Zamfara don amfanar talaka, jama’a na fama da rashin aikin yi, harkoki sun sukurkuce.
Aminiya: Wannan ne karo na farko da kake neman mukamin siyasa, kana ganin za ka iya fafatawa da wadanda suka dade suna yin ta?
IMAD: Gaskiya ne wannan ne karo na farko da nake neman wani mukami na siyasa, sai dai na jima ana damawa da ni wajen gwagwarmayar siyasa, a Zamfara da Sakkwato, na fara haka ne tun a 1999. Kuma kafofi da muka yi amfani da su wajen kafa gwamnatocin jiya da na yanzu, suna nan, da su ne kuma in Allah Ya yarda za mu yi amfani wajen ganin mun kai ga nasara a yanzu.
Aminiya: Jiharka Zamfara, jiha ce da ke karkashin Jam’iyyar APC, me ya ba ka kwarin gwiwar neman kujerar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP?
IMAD: Na farko dai saboda Gwamna mai mulki a yanzu bai yi wa jama’a aiki ba, na biyu kuma ai gabanin wannan Gwamnan, PDP ita ke mulkin Zamfara, Mahmuda Shinkafi wanda wannan Gwamna ya amshi mulki daga wajensa dan PDP ne, kuma muna nan tare da shi. Sai dai maimakon Gwamna ya maida hankalinsa wajen yi wa jama’a aiki, sai ya maida hankali a kan wasu abubuwa daban. Dubi misalin karatu da ya koma a yanzu haka wanda yake yi a Landan, saboda Allah yaya zai yi da sauran yaranmu da ke karatu a nan gida, ko zai sama musu makaranta ne su ma a can ko a Kanada don samun kyakykawar kulawa wanda ya gaza samarwa a nan.
Aminiya: Jihar Zamfara na cikin jihohi da ke sahun gaba wajen albarkar ma’adinai, wane tsari gare ka idan ka kai ga nasara don inganta su jihar ta iya rike kanta ba tare da dogaro da Asusun Tarayya ba?
IMAD: Harkar ma’adinai na cikin abubuwan da nake gudanarwa don yanzu haka muna da wuraren hakarsa da suka kai 14. Na san sirrinsu a kasuwannin duniya na kuma san kasashen da suka ci gajiyarsu har suka dogara da su. Idan Allah Ya ba mu nasara za mu gayyato masu ruwa da tsaki a wannan harka mu hada su da ’yan kasuwarmu na gida, don inganta masu harkar tare da samar da dimbin ayyukan yi ga jama’armu da kuma kudin shiga ga gwamnati.
Aminiya: Zamfara ta yi fama da matsalolin ’yan fashi masu kai hare hare, me kake jin ya hana kasa shawo kan wannan matsalar, kuma wane shiri kake da shi a kai da zai magance ta?
IMAD: Daga cikin dalilan da suka aka gaza shawo kan wannan al’amari da farko akwai talauci, sai rashin tallafa wa jami’an tsaro da karfafa masu gwiwa wajen ba su kayan aiki da alawus da kuma neman goyon bayan al’umma wajen samar da bayanai da za su taimaka wajen yakar al’amarin.
Aminiya: Ba ka ganin gwamnatin da ke mulki na yin duk wadannan abubuwa?
IMAD: Koda yake ban so na yi magana a kan wannan al’amari ba, amma gaskiyar al’amari shi ne, da jami’an wannan gwamnatin ake aikata wasu abuwan da suke faruwa, akwai hujja na hotuna kuma an baza su a yanar gizo da suke nuna wasu daga cikin jami’an gwamnatin tare da ’yan fashi suna rike da makamai, akwai kuma masu irin wannan hali da wannan gwamnatin ta ba su gudunmawar Naira miliyan talatin da baburan hawa. Tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya wanda dan Jihar Zamfara ne Allah Ya saka masa da alheri ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya magance wannan al’amari, ya sa an kama su an kawo su nan Abuja, amma wasu daga cikin jami’an wannan gwamnati suka yi ta kai-komo, suka tabbatar an ba da belinsu, suka dawo gida suna yi mana gwalo.