Da jami’an gwamnati nake zuwa tattaunawa da ’yan bindiga – Gumi
Malamin ya ce ba shi da burin da ya wuce a samu zaman lafiya a Najeriya.
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce jami’an Gwamnatin Tarayya suna masa rakiya a duk lokacin da zai gana da ’yan bindiga, saboda gudun zargi.
Gumi ya jima yana kira ga gwamnati da ta yi wa ’yan bindiga afuwa da kuma neman a tattauna da su don samun zaman lafiya.
A wata hira da jaridar PUNCH, malamin ya ce yana zuwa da sarakunan gargajiya da kuma jami’an gwamnati na jihohi a lokacin tattaunawa da maharan.
Ya ce, “Abin da ’yan Najeriya ya kamata su fahimta shi ne ba na zuwa wajen waɗannan mutane ba tare da jami’an gwamnati ba.
“Ina zuwa tare da ’yan sanda saboda mutum ba zai iya zuwa shi kaɗai ba, dole sai an raka shi.
“Wasu lokutan kuma suna gindaya sharuɗa kan da wanda za a je. A wasu lokutan kuma ina zuwa tare da sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati na jihohi.
“Burina kawai shi ne na sasanta don a samu zaman lafiya. Sun buɗe ƙofar zama da mu don tattauna batutuwa.”
Sai dai malamin ya musanta batun cewar ’yan siyasa ne ke ɗaukar nauyin ’yan bindiga a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
“Babu wani ɗan siyasa da ke ɗaukar nauyin waɗannan mutane. Mu duka muna fama da matsalar nan. Wannan wani yanayi ne na mutane da aka yi watsi da su tsawon shekaru.
“Yanzu sun samu damar ganin duniya kuma suna son ilimi. Waɗannan mutane suna amfani da Intanet kuma suna ganin yadda aka mayar sa su saniyar ware.
“Suna son ɗaukar fansa. Babu wanda yake jagorantarsu.
“Abun mamaki, a wata makaranta da aka gina wa makiyaya a wani ƙauyen da ke tsakanin Abuja da Kaduna, sama da mutum 600 daga cikinsu sun fara karatu a nan.
Suna faɗa mana cewa ba sa son ’ya’yansu su zama irinsu. Ka yi tunanin idan aka yi hakan a faɗin ƙasar.”