Da Jam’iyyar PDP ta ci gaba da mulki da Najeriya ta ruguje – Sanata Muhammed

Tsohon dan Majalisar Dattawa daga Bauchi ta Tsakiya Sanata Muhammed Alhaji Muhammed ya ce da Jam’iyyar PDP ta ci gaba da mulki a Najeriya tabbas da kasar ta ruguje baki daya, saboda yadda ta gagara kare rayuwa da dukiyoyin al’umma musamman a jihohin Arewa maso Gabas.Sanata Muhammed ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa […]

Da Jam’iyyar PDP ta ci gaba da mulki da Najeriya ta ruguje – Sanata Muhammed
Da Jam’iyyar PDP ta ci gaba da mulki da Najeriya ta ruguje – Sanata Muhammed

Tsohon dan Majalisar Dattawa daga Bauchi ta Tsakiya Sanata Muhammed Alhaji Muhammed ya ce da Jam’iyyar PDP ta ci gaba da mulki a Najeriya tabbas da kasar ta ruguje baki daya, saboda yadda ta gagara kare rayuwa da dukiyoyin al’umma musamman a jihohin Arewa maso Gabas.
Sanata Muhammed ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Bauchi, inda ya ce Jam’iyyar PDP ta shekara 16 tana mulki a kasar nan amma abubuwa da dama sun lalace ga kuma sace dukiyoyin al’umma. Ya ce “Tun lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi ragamar shugabancin kasar nan ake toshe mafi yawan hanyoyin da cuwa-cuwa da kudaden jama’a. Gwamnatin Tarayya tana taka rawar gani wajen magance matsalar masu ta da kayar baya a jihohin Arewa maso Gabas. Kuma Shugaba Buhari ya zo da manufofi masu kyau na inganta rayuwar mata da matasa amma wajibi ne sai an ba shi lokaci kuma a rika yi masa addu’o’i na musamman don ya cimma nasara.”
Da ya juya kan yadda kayan abinci ya yi tsada a kasar nan ya ce ya kamata ’yan Najeriya su koma noman kayan abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan abinci masu gina jiki. Ya ce duk kasar da ba ta iya noma abin da za ta ciyar da kanta, tabbas ba ta daga cikin kasashen da za a ce sun ci gaba a duniya.
Ya ce babbar matsalar da take addabar mafi yawan ’yan siyasar Arewa ita ce ta a ba su kudi su zuba a aljihunsu kuma sun gagara fahimtar cewa yanzu ba lokacin PDP ba ne.
Sai ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin kasar nan domin shugabanci abu ne mai matukar wahala da ba kowa zai fahimci haka ba sai wanda ya samu kansa a shugabancin.