Da Jonathan ya so da shi ne zai lashe zaben 2015 — Dakta Bello Halliru

Malamin ya ce a wancan lokaci Jonathan yana da karfin ikon da zai iya murde zaben 2015.

Da Jonathan ya so da shi ne zai lashe zaben 2015 — Dakta Bello Halliru

A wannan makon za mu kawo muku tattaunawar da Aminiya ta yi da dattijon Arewa kuma dan gwagwarmaya wato Dakta Bello Haliru, wanda dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama a matakan jiha da na kasa.

Bello Halliru Mohammed, wanda ya kasance Likitan Dabbobi, ya yi aiki a matsayin malami a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya kafin ya shiga siyasa da samun mukaman gwamnati.

Ya fara aiki ne a tsohuwar Jihar Sakkwato, inda ya kasance a matsayin kwamishina, sannan ya rike Ministan Sadarwa a lokacin mulkin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Sannan ya rike mukamin Ministan Tsaro a karkashin Goodluck Jonathan, sannan ya rike matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP har zuwa 2015.

Ya kuma yi aiki a matsayin Daraktan Kwastam a lokacin mulkin Shugaban Kasa Ibrahim Babangida. Yana rike da sarautar gargajiya ta Dan Galadiman Gwandu.

A cikin wannan tattaunawar, ya yi magana game da asalinsa, yadda ya shiga siyasa da halin da kasa take ciki:

Mu fara da tambaya game da asalinka.

Ni na fara aiki ne a matsayin Likitan Dabbobi, sannan na kare a matsayin dan siyasa.

An haife ni a Birnin Kebbi, wanda yanzu take a Jihar Kebbi. Ina daga cikin tsatso kuma zuriyar Abdullahi Fodio.

Kakana ya kasance dan sarkin Gwandu Halliru, kuma dan uwa ga sarki Haruna, sannan a matsayin kaka ko dan’uwa ga sarkin Gwandu na yanzu.

Kakan mahaifiyata shi ne Magajin Rafi, wanda ya kasance dan majalisar wakilai a lokacin Jamhuriya ta Farko.

Na taso a gidansa, don haka yana daya daga cikin mutanen da suka tasirantu wajen tarbiyyata.

Shi ne ya tura ni makaranta kuma ya ci gaba da karfafa ni. Bayan na gama firamare a Birnin Kebbi, na tafi makarantar sakandare ta tsohiwar Jihar Sakkwato, inda na rubuta jarabawar (WASC) kuma na fito da Mataki na 1.

Bayan haka, na tafi Kwalejin Barewa don samun Babbar Takardar Shaida ta (HSC) domin a wancan lokacin ba za ka je jami’a kai tsaye ba, dole ne ka fara yin ko dai A-level ko HSC.

Don haka, na bi ta HSC zuwa Jami’ar Ahmadu Bello, inda na karanta fannin Likitancin Dabbobi.

A cikin wannan tsari, na zama Shugaban Kungiyar Dalibai (SUG) a ABU a 1970 zuwa 1971.

Bayan na kammala karatuna a ABU, an dauke ni a matsayin malami a Sashin Likitancin Dabbobi kuma aka tura ni Jami’ar Minnesota, inda na karanta Kiwon Lafiyar Dabbobi a cikin Jama’a.

Bayan na dawo, na yi dan lokaci kadan ina koyarwa kafin Gwamnan Sakkwato na lokacin, Kanar Umaru Mohammed ya gayyace ni don taimakawa wajen tafiyar da al’amuran jihar.

Na shiga gwamnatinsa da niyyar komawa Jami’ar Ahmadu Bello, amma kaddara ta sa bayan na yi Kwamishina na Noma da Ilimi, aka yi mani tayin tsayawa takarar mataimakin gwamna a karkashin jam’iyyar GNPP.

Haka na tsinci kaina a siyasa ina tsammanin zai kasance na dan wani lokaci, amma hakan bai faru ba, kowane lokaci sabuwar gwamnati ta zo, mutane na dawowa gare ni don in shiga, in yi aiki tare da su.

Me ya sa ka zabi karanta Likitancin Dabbobi?

Masarautar Gwandu da tsohuwar Jihar Sakkwato su ne manyan wuraren kiwo a Najeriya, kuma kasancewata Bafulatani, na jima ina sha’awar kiwon shanu.

Sai kuma wani abu da ya tasirantu min shi ne lokacin da nake makarantar firamare, akwai wasu manyan mutane guda biyu da suka min tasiri wajen zabina, musamman Dakta Buka Shaib, babban likitan dabbobi na wancan lokacin a Birnin Kabi.

Akwai wata cibiyar kiwo, kuma Dakta Shaib yana wurin. Muna sha’awar ganin sa yayin da ya zo da motarsa tare da kyakkyawar matarsa. Suna zuwa kasuwa, gidan kakana. Don haka duk lokacin da Dakta Shaib ya zo, ina bin sa kasuwa.

Shin ya san ka ko kuwa kana bin sa ne kawai saboda sha’awa?

Kawai ina sha’awar sa ne a matsayin likita da kuma duk abin da yake yi. Daga baya kuma, wani cikin iyalina ya zama mai kula da dabbobi.

Shi ma ya karfafe ni wajen son abin da nake ganin likitoci suna yi, musamman tafiya da doki don yin allurar riga-kafin shanu a cikin daji da sauran abubuwa. Wannan shi ne abin da ya sanya ni yin karatun likitancin dabbobi.

Ka kasance shugaban dalibai a 1971, za ka iya bugar kirji ka ce wannan shi ne mafarin siyasa a gare ka?

Ban yi tunanin siyasa ba a lokacin. Domin ana karkashin mulkin soja ne, a lokacin mulkin Yakubu Gowon. Ina magana ne game da siyasar dalibai.

Me ya sa wani likitan dabbobi mai aiki tukuru kamar kai zai yi tunanin tsayawa takarar Shugaban Kungiyar Dalibai?

Kawai sha’awa ce. Ina tsammanin tun farko na kasance ina da sha’awar siyasa, saboda kakana wanda na tashi tare da shi, ya kasance dan majalisa a Arewacin Nijeriya kuma na karanta tarin takardu da ya kawo daga Kaduna.

Wannan shi ne farkon sha’awata ga siyasa. Ka gaya mana game da zamanka a Amurka.

A lokacin ba a saba ganin mutane daga yankinmu suna tafiya Amurka ba.

Tsawon wane lokaci ne ka yi a can kuma mene ne kwarewarka?

Kimanin shekaru biyu na yi a can kuma ya kasance zama ne mai kyau. Na yi sa’a na tafi Minnesota saboda a wancan lokacin babu wariyar launin fata a wurin, ba su da yawan baki masu launin fata.

Saboda haka, mun samu kyakkyawan tarba da kuma zama ni da matata. Saboda abokan karatunmu galibinsu sojojin Amurka ne.

Suna yin amfani da horon likitancin dabbobi don su tura su, su kula da tsabtace abinci a sansanonin soja daban-daban a duniya.

Kadan daga cikinmu fararen hula ne, mai yiwuwa daya ko biyu daga ciki sun kasance ne daga Nijeriya.

Na san wani daga kasar Indonesiya da wasu kadan daga Latin Amurka. Duk ‘yan asalin Amurka sojoji ne likitocin dabbobi.

Mun yi huldar zamantakewa sosai, muna gayyatar juna zuwa gidajenmu da shirya liyafa.

Wasu daga cikin malamanmu da suke Amurkawa suna da sassaucin ra’ayi kuma suna gayyatar mu zuwa gidajensu.

Wasu daga cikinsu suna da tafkuna a bayan gidajensu, kuma muna zuwa kan kwalekwale da abubuwa makamantan haka.

A takaice dai zama ne mai kyau sosai, kuma ya fadada min hangen nesa na.

Ka samu cikakken tallafi karatu ne?

Na samu tallafi daga Jami’ar ABU Zariya. Na kasance cikin kwanciyar hankali, dangantakata da kowa ta kasance mai kyau. Na yi amfani da wannan damar wajen yawon ziyartar jihohi da dama.

Na kasance a Jihar California kuma na je Jihar Tedas domin halartar taron Kungiyar Likitocin Dabbobi ta Amurka, da kuma Kungiyar Kiwon lafiyar Abinci ta Amurka, wadda na zama mamba kafin in baro kasar.

Har yanzu ni mamba ne a ciki, amma ka sani, zuwa Amurka don tarurruka ba abu ne mai sauki ba.

Ko da a matsayin minista ko Daraktan Kwastam?

A matsayin Daraktan Kwastam na ziyarci Amurka, amma wannan ya bambanta saboda na kasance tare da Daraktan Kwastam na Amurka.

Na ziyarci wasu tashoshinsu da wuraren ayyukansu, amma ban samu lokacin halartar ayyukan likitancin dabbobi ba.

Bari na dawo da kai ga ABU.

Na yi imanin cewa tsammanin da ake yi shi ne lokacin da ka dawo daga karatu a waje, za ka zauna a makaranta ka koyar, amma da alama ba ka yi hakan ba.

Wannan bai fusata jami’ar ba?

Wannan shi ne yarjejeniyar. A lokacin farkon gwamnatin soja ne don haka dukkanin cibiyoyin suna da sassauci dangane da yadda ma’aikatan su ke gayyatar su domin taimakawa gwamnati.

Lokacin da na sami wannan gayyatar, na sanar da ABU kuma ba su tada wani jijiyar wuya a kai ba. Na samu amincewa nan take.

Ta yaya gayyatar ta zo?

Gaskiya abin ya ban dariya saboda wani Kanar Umaru Mohammed ne da ban taba haduwa da shi ba.

Lokacin da na dawo daga Amurka, daya daga cikin abokan karatuna, Lawali Bungudu, shi ne shugaban Operation Feed the Nation a Sakkwato.

Ban kasance a kasar ba lokacin da aka nada shi, don haka na tafi zuwa ma’aikatar da ke cikin ginin ma’aikatar noma inda ofishinsa yake, don ganinsa. Ya yi farin ciki da ganina.

Yayin da nake zaune a gabansa, gwamna ya kira shi, kuma ya ce in bi shi don mu tafi tare, kuma na yarda tun da ni dan jiha ne kuma na dawo daga karatu. Don haka na tafi gidan gwamnati tare da shi.

Lokacin da muka hadu da gwamnan abin ya burge shi cewa akwai wani daga Sakkwato da ke da shaidar digiri a fannin likitancin dabbobi domin a lokacin, babban likitan dabbobi na jihar mutumin Masar ne.

Ni ne farkon likitan dabbobi daga Jihar Sakkwato. Ba da dadewa ba abokina Bungudu ya zo Zariya. Shi ma malami ne a can.

Ya zo gidana kuma ya ce min gwamnan yana son gani na. Na tambaye shi me ya sa yake son ganina, ya ce ya ba shi umarnin ya kawo ni da kansa domin gwamnan ya tattauna da ni.

Ka yi tsammanin abin da kiran yake nufi?

Ban yi tsammani ba. Duk da haka, idan akwai abin da na yi tunani, shi ne watakila yana son in zama babban likitan dabbobi na jihar.

Washe-gari da safe, na tuka mota zuwa Sakkwato kuma na tafi gidan Bungudu, sai ya kai ni zuwa gidan gwamnati.

Mun tattauna game da kasar da ci gaban Jihar Sakkwato. Ya tambaye ni ko zan taimaka wajen habaka abubuwan da muka tattauna, na ce, “me zai hana?”

Na je jami’a a karkashin tallafin Jihar Sakkwato, don haka nauyi ne a kaina in taimaka ta duk wata hanya da yake so in taimaka. Bayan wasu ’yan kwanaki Bungudu ya sake zuwa ya ce, gwamnan yana son ganina.

A nan ne ya tambaye ni ko zan amince da mukamin kwamishinan noma tun da ni likitan dabbobi ne.

A matsayin saurayi mai shekara talatin da wani abu da aka nada a mukamin gwamnati yaya ka iya jurewa?

Na yi tunanin cewa na dace sosai domin bayan wani lokaci da na dauka a matsayin kwamishinan noma, an nada ni kwamishinan ilimi, wanda ita ce babban ma’aikata.

Wannan shi ne dalilin da ya sa, na yi tunanin cewa, ina yin aiki mai kyau.

Bayan ka yi kwamishina a ma’aikatun noma da ilimi, lokacin da mulkin farar hula ya dawo, ka yi kokarin zama mataimakin gwamna, me ya sa ba ka koma jami’a ba?

Shiri na shi ne in koma jami’a, amma mutanen masarautata sun sake zuwa, suka roke ni in shiga Jam’iyyar NPN, in tsaya takarar mataimakin gwamna, amma na ki.

Su wane ne suka zo?

Mambobin GNPP, galibi ’yan kasuwa. Lokacin da Waziri Ibrahim ya kafa jam’iyyar, ya fi hulda da ’yan kasuwa. Duk inda ya je, zai dauki manyan ’yan kasuwa ya nemi su zama shugabannin jam’iyyar.

Amma ka san yawancin ’yan kasuwarmu ba su da ilimi sosai, don haka suna neman wani da yake da karin ilimi don zama dan takara.

Lokacin da rukunin farko suka zo, na ki kuma na gaya musu cewa ban kai shekaru 35 ba, wanda shi ne karancin shekarun tsayawa takarar gwamna.

Sun tafi cike da takaici. Ko lokacin da NPN ke taro don zabar dan takara, wani ya jefa sunana a ciki. Kuma ban kasance memba na jam’iyyar ba don har lokacin ina kwamishina ne.

Don haka, an zabi Garba Nadama da Shehu Kangiwa a matsayin ’yan takarar gwamna da mataimakin gwamna.

A wancan lokacin na kasance wani bangare na jagorancin masarautarmu.

Sakkwato ce babbar masarauta, don haka mun yarda cewa idan sun dauki kujerar gwamna, to Gwandu, kasancewar ita ce masarauta ta biyu, za ta samu kujerar mataimakin gwamna.

Amma sun yi biris da mu gaba daya suka dauke komai. Argungu suka ba da gwamna, yayin da Sakkwato suka ba da mataimakin gwamna, Gwandu kuma aka yi watsi da ita.

Tun da ni ne kwamishina daga wannan yanki, suka ce in yi wani abu a kai.

Na tafi na gana da jagororin NPN na lokacin, amma suka ce min na makara, domin sun riga sun gama shirye-shiryensu.

Wannan amsar ta bata min rai sosai, sai na gaya wa dattawanmu irin su Mallam Idris Koko cewa wadannan mutane sun yi watsi da mu, don haka muna bukatar nemo wata mafita.

Don haka, muka je wajen shugabannin GNPP. Wannan shi ne dalilin da ya sa GNPP ta yi karfi sosai a Jihar Sakkwato duk da cewa mun yi asarar zabe saboda magudi.

Ba ka so ka koma jami’a ba?

Sannnan ai lokaci har ya kure. Na riga na rasa matsayina saboda bayan na zama kwamishina, wanda aka bar ni da shi, ya kamata in koma.

Amma saboda na shiga siyasa, dole na yi murabus domin ba za ka iya zama ma’aikacin gwamnati kuma dan siyasa a lokaci guda ba, saboda mulkin soja ne.

Don haka dole ne na yi murabus kuma ba zan iya komawa ba. kai ne mai kula da kwastam a karkashin mulkin Janar Babangida.

Yaya aka yi hakan?

To, ni ne Janar Manajan RIMA na Sakkwato lokacin da Babangida ya nada Janar Gado Nasko a matsayin minista. Abokai ne kuma ’yan aji daya.

Babangida ba ya jin dadin Hukumar Shige da Fice ta Kwastam a lokacin don haka ya ce ba zai nada kowa daga cikin ma’aikatan hukumar ba.

A lokacin, Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa shi ne wanda aka fi tsammanin zai karbi aikin.

Kowa yana tsammanin shi ne zai karbi ragamar, amma Babangida bai son ya nada wani daga hukumar ta Kwastam don yana son ya yi gyara.

Don haka yana neman wani mai gaskiya don ya nada shi. Sai abokinsa, Janar Nasko, wanda ya san ni a matsayin kwamishina, ya fada wa Babangida cewa, ya san wani a Sakkwato, wanda ya yi aiki da shi, amma matsalar ita ce ba za a iya sarrafa shi ba. Babangida ya ce irin mutumin da suke nema ke nan.

Nasko ya ce, ba za a iya sarrafa ni ba saboda kwarewar da ya yi da ni lokacin da nake shugaban kwamitin tsare-tsare na jiha, lokacin da muka ba wa wani kamfani daga Kano kwangilar gina majalisar dokokin jiha.

Masu neman kwangilar da suka zo daga Legas suna son su umarce mu, amma na ki. Ya yi alfahari sosai cewa zai samu kwangilar saboda ya zo daga Legas. Ya yi girman kai, don haka muka ba wa wani mutum daban kwangilar. Kwangilar dole ta je majalisar zartarwa don amincewa.

Lokacin da muka je majalisar, kwamandan (Nasko) ya shiga rudani saboda daya daga cikin manyan shugabanninsa daga Legas ne ya aiko da wannan mutum, kuma yanzu, kwamitin tsare-tsare ya ce ba za su ba shi aiki ba.

Shekaru nawa ka yi a matsayin shugaban Kwastam?

Na yi shekaru shida. Mun tara adadin kudade daga miliyoyi zuwa biliyoyin Naira a karon farko kuma kowa ya yi mamaki.

Yaya Atiku ya ji ganin cewa an hana shi wannan damar?

Gaskiya ya yi iyakar kokarinsa don yin aiki tare da mu. Ya kasance mataimakina amma ina tsammanin ba ya jin dadi da yanayin.

Akwai wasu matsaloli tsakaninsa da wasu daga cikin mutanen Adamawa wato jiharsa, wadanda suke cikin Majalisar Koli ta Soji shi ya sa bai samu aikin ba.

Ka kasance minista a karkashin Obasanjo da Jonathan, ta yaya za ka kwatanta wadannan shugabanni biyu?

Mutane biyu ne daban-daban. Abu daya kawai mai muhimmanci game da Obasanjo shi ne yana da karfin yanke hukunci a matsayin shugaban kasa.

Me za ka ce game da Jonathan?

Gaskiya Jonathan mutum ne mai kirki, amma bai da irin karfin yanke hukunci da na gani a wurin Obasanjo.

Jonathan mutum ne mai kirki. Idan ka ce masa wani abu ba zai yiwu ba, ba zai matsa maka ba.

Idan ka tuna, ya ce zabensa ba shi da darajar jinin ‘yan Najeriya.

’Yan siyasa suna yawan yin irin wadannan maganganun, kana ganin Jonathan yana tsayawa kan maganarsa?

Yana nufin abin da ya ce da gaske, shi ya sa ya rasa zaben. Idan ya fito da karfin ikon shugabancin don lashe zaben, babu abin da zai hana shi, amma bai yi ba.

Ya nace kan tsayawa takara a 2011 kuma yawancin mutane suna cewa daga nan ne matsalar tsarin karba-karba ta fara.

A matsayinka na shugaban jam’iyya ka goyi bayansa, me ya sa?

Mafi yawan gwamnonin Arewa ba su so ya tsaya takara ba, amma mutanensa sun karfafa masa gwiwar tsayawa takarar.

Amma kai ka goyi bayansa a matsayin shugaban jam’iyya?

A’a. Na kasance a Birtaniya lokacin da gwamnoni suka ce idan Jonathan yana son ya tsaya takara sai ya yi wa’adi daya kacal, kuma za su rubuta yarjejeniya.

Don haka, an rubuta wata yarjejeniya. Sakatarena a wancan lokacin, Abubakar Baraje, ya kira ni ina Birtaniya ya fada min abin da ke faruwa.

Shin ya shirya tsaf don tsayawa takara a 2015?

Tabbas.

Kuma ya ketare yarjejeniyar wa’adin sau daya?

Gaskiya ce.

Don haka, yarjejeniyar ba ta tabbata ba ke nan?

A’a.

A tsawon aikinka, ka taba fuskantar matsaloli. Ka ambaci gaskiya a matsayin jigon da ka dogara da shi, ko za ka iya yi mana bayani kan binciken da Hukumar EFCC ta yi maka?

Wannan lamari ne mara dadi sosai.

Kamfanin Siemens da wani kamfani Ericson daga kasar Sweden, su ne manyan ’yan kwangilolinmu.

Zabe yana zuwa, kuma jam’iyya tana neman tallafin kamfen daga manyan ’yan kwangiloli, kuma an tuntubi Siemens kan haka, sun kuma ba da gudunmawarsu, amma ba zan ce ga wanda suka ba wa ba.

Don ba su ba ni ba ni dai.

Amma kai kake shugaban jam’iyya, ko ba haka ba?

A cikin rubutunsu, sun rubuta cewa, sun ba ni a matsayin shugaban jam’iyya, amma hakikanin gaskiya, sun tura shi asusun wani ne ba ni ba.

Na san asusun wanda aka tura wa, amma lokacin da lamarin ya taso, bana son in bayyana.

Hukumar EFCC ba ta taba tambaya ko tuhuma da cewa ga wani mutum da ya bani kudi ko ya karbi kudi a madadi na ba. Amma na san abin da ya faru.

Don haka na dauki alhaki kuma lamarin ya gushe saboda masu mulki a lokacin sun san wanda ya karbi kudin.

Ba ka jin cewa hakan zai iya yi maka illa a idanun jama’a?

Wannan shi ne nauyin jagoranci ai. Idan ka karbi aiki, kai ne ke da alhakin duk abin da ya faru. Wannan irin abun ya faru da ni a Hukumar Kwastam ma. Kuma na dauki alhakin duk abin da ya faru.

Shin ka yi murabus daga siyasa?

Ban yi murabus ba. Har yanzu ni mamba ne a kwamitin kula da amintattu na Jam’iyyar PDP.

Mene ne kake yi yanzu?

To, na taba samun hawan jini, amma yanzu ina murmurewa kuma ina halartar tarurruka. Ni ne Shugaban Kungiyar Dattawan Jihar Kebbi. Don haka zan ce har yanzu ina cikin siyasa.

Ba za ka taba yin murabus daga siyasa ba, saboda mutanen da ka taimakawa da wadanda kake jagoranta za su ci gaba da zuwa wurinka.

Me kake ji game da abubuwan da ke faruwa a kasa tun bayan da Gwamnatin APC ta karbi mulki?

APC ta kasance masifa ga wannan kasa tun daga kan Buhari. Sun zo ne kamar kura da fatar akuya.

Ci gaban da muka gani lokacin da Buhari ya kasance shugaban mulkin soja duk Tunde Idiagbon ne ke jagoranta, ba shi yana labewa ne a bayan Tunde.

Tunde ne ke kan gaba wajen jagorantar kasa. Don haka, lokacin da ya dawo ba tare da Tunde ba, babu wanda zai rika kama hannunsa yana jan ragamarsa. Mutane sun ce bai san abin da ke faruwa ba sunan yana kan kujera ne kawai.

Ba a taba ganin cin hanci da rashawa mai yawa a wannan kasar kamar yadda muka gani a lokacin mulkin Buhari ba. Mutanen da ba su da komai sun zama miloniyoyi cikin dare daya. Sannan kuma, Tinubu ya riga ya bayyana cewa zai ci gaba daga inda Buhari ya tsaya, saboda haka lokacin da ya hau, abin kara munana ya yi.

Ta yaya za ka bayyana wata 15 na mulkin Tinubu?

Yana da matsala sosai, ci gaba ne daga abin da Buhari ya yi. Na san ma ya fi muni domin yana da wani rukunin sirrin Lagos da ke kewaye da shi.

Za ka ga cewa yawancin mutanen da ke da manyan mukamai, musamman na kudi, sun fito ne daga majalisarsa ta Legas lokacin da yake gwamna.

Don haka ya zama lamari na cikin gida na yanke shawara kan inda tattalin arziki zai tafi da wanda zai samu.

Kana ganin PDP za ta iya dawowa ta karbi mulki?

Abin takaici shi ne, manyan jam’iyyun adawa da sauran jam’iyyu suna rarrabuwa. Babu wanda ya yi tsammanin PDP za ta sake farfadowa bayan wa’adin Buhari na biyu, amma muka dawo garau kuma muka fafata da Tinubu.

Don haka, dabaru da mutanen da suka farfado da PDP bayan faduwar Jonathan, har yanzu suna aiki. Za mu ga abin da zai faru a 2027.

Me za ka gaya mana game da Dakta Bello a matsayin mutum mai zaman kansa. Yaya rayuwar iyalinka take?

Ina da mata da ’ya’ya shida, amma babban dana namiji ya rasu ba da jimawa ba. Wannan wani abu mawuyaci da ba za mu manta da shi ba, amma muna kokarin yi masa addu’a.

Yarana sun girma. Na biyun namiji ya dauki abin da Abba ya bari, yana gudanar da kasuwancin kadarori.

Na ukun yana wakiltar al’umma a Majalisar Tarayya. Wasu daga cikin ’ya’yana mata sun yi aure kuma wasu suna aiki. Ina da likita daya a cikinsu da kuma mai aikin gudanarwa.

Ina da wata diya wadda ta yi aure, amma har yanzu ba ta da wani aiki na dindindin, tana dai aiki da wata kungiya ce mai zaman kanta. Zan ce ina da iyali masu cike da kwanciyar hankali da lafiya.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano