Da Jonathan ya zarce da Boko Haram ta wargaza Najeriya – Dogara
Shugaban Majalisar Dattawa Barista Yakubu Dogara, ya ce da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zarce a mulki da mayakan Boko Haram sun wargaza kasar nan, inda ya ce kayar da gwamnatinsa ne ya ceto Najeriya daga rugujewa.Barista Yakubu Dogara ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu […]
Shugaban Majalisar Dattawa Barista Yakubu Dogara, ya ce da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zarce a mulki da mayakan Boko Haram sun wargaza kasar nan, inda ya ce kayar da gwamnatinsa ne ya ceto Najeriya daga rugujewa.
Barista Yakubu Dogara ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana samun nasara a yakin da take yi da maharan Boko Haram, inda ya yi kira ga Shugaban kasar ya hanzarta kiran taron masu bayar da tallafi na duniya kan yankin Arewa maso Gabas, inda ya ce kudaden da aka samu a wajen taron za a yi amfani da su ne domin sake gina yankin da yakin Boko Haram ya ruguza.
Shugaban Majalisar ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da ke Uhogua a karamar Hukumar Obia ta Arewa maso Gabas da ke Jihar Edo.
Yakubu Dogara wanda ya girgiza da yawan ’yan gudun hijirar da ke sansanin ya shaida musu cewa, gwamnatin PDP ta gaza magance yakin kamar yadda aka sanya rai. Ya ce wannan ne ya jawo rikicin da ake ciki a yanzu a kasar nan, kuma ya yaba wa gwamnatin Jihar Edo da babban mai kula da sansanin Fasto Folorunsho Solomon kan kula da tafiyar da sansanin.
Ya yi alkawarin cewa Majalisar Tarayya za ta bayar da tata gudunmawar wajen tabbatar da ana kula da ’yan gudun hijirar. “Ina godiya ga Ubangiji kan kawo mana dauki a cikin al’amuranmu da Ya kawo wannan canji. Da mun ci gaba kamar yadda yake a baya, tabbas mayakan Boko Haram za su cimma wurare irin su Jos zuwa yanzu. Da ’yan gudun hijira sun kai miliyoyi, amma sai Ubangiji Ya karbi addu’o’inmu Ya kawo mana canjin gwamnati. Kuma nan da nan wannan gwamnati ta tashi haikan wajen kawo karshen wannan yaki,” inji Dogara.
Yakubu Dogara ya ce “Mun ga yadda hare-haren suka ragu sosai, kuma muna fata nan kusa ko nan da karshen wannan shekara mafi yawanmu da muke nan a yau da suke son komawa garuruwansu za su iya yin haka.”
Ya ba ’yan gudun hijirar buhunhunan shinkafa da na alkama da sukari da sauransu, inda ya yi alkawarin biyan kudin jarrabawar NECO da WAEC ga dalibai ’yan gudun hijira. Ya ce su a majalisa suna kokarin amincewa da wani kudirin doka na kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas domin tabbatar da an samar da kudi don sake gina garuruwan da aka lalata bayan kawo karshen yakin.