Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?3

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin […]

Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?3
Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?3

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan a ce kai ne Al-mustapha, ko za ka iya yafe wa wadanda suka yi sanadiyyar jefa ka cikin wannan ukuba? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka bayyana dangane da haka:

Da ni ne, yafewa zan yi
– Muhammad Sani
Muhammad Sani: “Da ni ne Hamza Al-mustapha, ba zan rike abin da aka yi min ba, yafewa zan yi, tunda kuwa ni ne da nasara, tunda ma Ubangiji Ya wanke ni daga laifi kuma daga zargi duk duniya an gani ba ni da laifi.
“Na farko dai wanke Al-mustapha da aka yi daga laifin da ake zarginsa na kisan kai, wata daukaka ce da daraja a gare shi. Haka nan kuma zaman shekaru da dama da ya yi a cikin ukuba ta zaman kurkuku a kan zargin da ba na gaskiya ba, wata daukakar ce daban. Sannan kuma idan
ya yafe zai sake kara samun wata daukakar a wajen mutane da kuma wajen Ubangiji. Yafewar ita ce ta fi tunda abin da ya faru ya riga ya faru.”

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50