Da kudin N-Power na yi karatun digiri —Aminu Madaci

Wasu ba su gane amfanin shiirn N-Power ba sai da aka daina biyan su kudin

Da kudin N-Power na yi karatun digiri —Aminu Madaci

Shirin N-Power da na Anchor Browers da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kaddamar a zangonta na farko, shirye-shirye ne da aka bullo da su don tallafa wa marasa karfi a cikin al’umma su samu damar tsayawa da kafafunsu.

Sai dai abin da akasarin mutane suke son ji ina aka kwana da wadannan shirye-shirye?

Aminiya ta yi kokarin zakulo wadansu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin don jin inda suka kwana bayan da aka kawo karshen shirin N-Power.

Shin sun mike ne ko sun ci sun cinye ne ba tare da tsinana wa kansu komai ba?

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, Aminu Haruna Madaci wani matashi da ya fito daga kauyen Madaci a Karamar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara, ya shaida wa Aminiya yadda ya amfana da shirin N-Power ta hanyar daukar dawainiyar kansa da karatunsa a jami’a mai zaman kanta ya kuma tallafa wa ’yan uwa.

Shi kuwa Mustapha Ibrahim da ke Kano cewa ya yi bayan bude kyamis biyu da kudin shirin N-Power, ya kuma dauki nauyin karatun kannensa biyu, inda daya ke jami’a daya kuma ke makarantar koyon kiwon lafiya.

A bangaren shirin Anchor Browers kuwa, Malam Dalhatu Abu Darda’i mazaunin garin Jingir a Jihar Filato ya ce, a shekarar farko ta shigarsa shirin ya noma buhun shinkafa 120, kuma hakan ya sa ya dogara da kansa har ya ki sake karbar bashin ya ce a ba wani.

Ya ce a shekara ta biyu ya noma fiye da buhun shinkafa 350 kuma yanzu yana hadawa da noman rani a biyo mu:

 

Yaya ka samu kanka a cikin wadanda suka ci gajiyar shirin N-power?

Bayan na kammala karatun sakandare a shekarar 2010 a garin Sakkwato na yi sha’awar aikin dan sanda na kuma nemi aiki na rasa.

Da na yi, na yi, ban samu aiki ba, sai na koma Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Sakkwato na ci gaba da karatun neman Shaidar Malanta ta Kasa (NCE).

Bayan na kammala na ci gaba da neman aiki, a wancan lokaci na nemi aikin tun daga na dan sanda zuwa sojan ruwa da sojan sama da na kasa da NDLEA da ayyuka da dama inda na cike fom din nema amma ban samu ba.

Daga nan na tafi garin Abeokuta a Jihar Ogun na fara sana’a.

A shekarar 2016 na samu labarin ana daukar masu shiga shirin N-Power, ban yi kasa a gwiwa ba na cike fom na nema, cikin ikon Allah da aka kafe sunayen wadanda aka dauka sai na ga akwai sunana a ciki.

Nan na biya kudin mota na tafi garinmu a Jihar Zamfara na shiga aka tantance mu, daga nan na koma inda nake sana’a ta a Jihar Ogun, muka ci gaba da jira.

Ana nan aka sake neman mu koma a sake tantance mu, daga nan na sake komawa bakin sana’ata har zuwa lokacin da aka kira mu aka ba mu takardar shaidar an dauke mu a N-Power.

Aka kai ni makarantar firamare ta kauyenmu, wacce a ita na yi karatun firamarena, nan na yi aikin koyarwa na tsawon shekara biyu na aikin N-Power.

Duk wata ana ba ni Naira dubu 30, kawai sai dai in ga sun shigo asusun ajiyata na banki.

Kuma duk sa’ar da na samu hutu sai in koma garin Abeokuta in ci gaba da sana’a, wannan Naira dubu 30 a duk wata sun ba ni gudunmawa kwarai sun kuma yi tasiri a rayuwata.

Ta yaya tallafin da kake samu daga shirin N-Power ya yi tasiri a rayuwarka?

Alal hakika kudin da aka yi ta ba mu na Naira dubu 30 na shirin N-Power ya yi tasiri a rayuwata, domin bayan da na kammala karatu na yi aure na kuma tafi ci-rani Kurmi, a lokacin da na fara aikin N-Power albashin farko na same shi ne a daidai lokacin da matata ta haihu.

Da wannan Naira dubu 30 na sayi ragon suna na Naira dubu 25 kuma na sayi kayan miya da ragowar.

Bayan nan kuma a duk wata idan na samu kudin nakan sayi kayan abinci da su, wanda zan ci a gidana da wanda iyayena za su ci, abin da ya hada da shinkafa da gero da makamantansu.

Ana nan haka da dan abin da na samu a sana’ata sai in hada da na N-Power har na kai ga na sayi babur ana yi min acaba da shi a Abeokuta ni ma in an yi hutu ina yi ina kuma taba sana’a har Allah Ya hada ni da wani aminina ya ba ni shawarar in ci gaba da karatu.

Takwarorin Aminu a lokacin bikin shigarsu jami’a don fara karatun digiri

Da kudin N-Power na shiga Jami’a

Daga nan na fara karatun digiri a jami’a mai zaman kanta ta Crescent University da ke Abeokuta, kuma a lokacin farkon karatun cikin kudin N-Power da nake tarawa na biya kudin makaranta.

Yanzu haka ina zangon karatuna na uku a makaranta saura zangon karatu daya in kammala digiri.

Duk da dai yanzu ba na samun kudin N-Power tunda na kammala shekara biyu a shirin, amma da dan abin da na tanada lokacin da nake samun wannan kudi da kuma sana’ar da nake yi, nake ci gaba da biyan kudin makaranta da dawainiyata da ta iyalina da ta iyaye da sauransu.

Tabbas matasa da dama sun shaida tasirin shirin N-Power, wadansu ba su kai ga gano amfanin shirin ba, sai bayan da kudin da suke samu duk wata ya yanke, aka daina ba su, a lokacin suka gane ashe kudin na da matukar muhimmanci.

To yanzu me kake tsammani bayan kammala shirin N-Power?

Aminu Madaci da abokan karatunsa lokacin da ya fara karatun digiri da kudin N-Power

Eh akwai kudin sallama da muke sa rai, ko kuma tallafin bashi daga Babban Bankin Najeriya (CBN), idan mun samu wannan zai taimaka mu ci gaba da gudanar da al’amuranmu yadda ya kamata, masu kasuwanci su dora a kai, masu niyyar ci gaba da karatu su samu damar daukar nauyin karatunsu.

Na bude kyamis biyu da kudin N-Power

Shi kuwa wani matashi da ya ci gajiyar shirin na N-Power a zango na biyu a Jihar Kano, mai suna Mustapha Ibrahim ya bayyana wa Aminiya cewa daga kudin da ya samu na N-Power ya samu damar bude kyamis guda biyu inda yake hada-hadar sayar da magunguna.

Mustapaha wanda ya kammala aikinsa na N-Power ya bayyana wa Aminiya cewa a yanzu jarinsa ya kai Naira dubu 450.

“Daga kudin da ake biya na na Naira dubu 30 a wata na rika cire wani kaso ina ajiyewa, sai ga shi kudin sun taru har na bude kyamis inda nake sayar da magunguna,” inji shi.

Likkata ta ci gaba

A cewarsa baya ga kyamis a yanzu ya bude wurin hada-hadar kudi na POS inda yake samun kudin shiga ta wannan hanya.

Mustapha ya ce a yanzu haka yana da yara biyar a karkashinsa da suke taimaka masa wajen gudanar da kasuwancinsa na harkar magaunguna da kuma POS.

“Wadanan yara nawa da suke taimaka min ina iya biyansu albashi a wata.

“Muna lissafa cinikin da muka yi a wata, dama akwai tsarin da muka yi yarjejniya a kai na yadda za a rika biyan su,” inji shi.

Da kudin N-Power nake daukar nauyin ’yan jami’a

Da yake lissafa nasarorin da ya samu daga kasuwancinsa wanda ya samu dalilin shirin N-Power ya ce, “A yanzu haka kin ga ina daukar nauyin karatun kannena biyu wadanda daya daga cikinsu ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, daya kuma yana karatu a Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya ta Kano. Kuma dukkasu suna yin abin da ya kamata dangane da harkar karatunsu.”

Kwalliya ta biya kudin sabulu

Haka a cewarsa, “A yanzu haka na yi aure ina tare da iyalina alhamdulillah.

“Ni ina ganin shirin N-Power kwalliya ta biya kudin sabulu.”

Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa irin wadannan shirye-shirye da take samarwa don tallafa wa rayuwar matasa a kasar nan.

“A gaskiya dole in gode wa gwamnati domin na ci gajiyar shirin N-Power.

“Alhamdulillah, ba don da shirin N-Power ba da yanzu ina fama da rashin aikin yi. Amma a yanzu alhamdulillah ina samun kudin shiga har ma wadansu suna samun nasu a karkashina,” inji shi.

Mustapaha ya yi kira ga gwamnati ta kara bullo da wasu shirye-shirye makamantan na N-Power don dimbin matasan kasar nan su amfana.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos