da kuma kanin tsohon shugaban Amurka yana neman shugabancin kasar
A ranar Litinin da ta gabata ne tsohon Gwamnan Jihar Florida, wanda dan tsohon Shugaban Amurka kuma kanin tsohon shugaban kasar Amurka, ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar. da ga tsohon Shugaban Amurka George H.W Bush kuma kanin Shugaba George W. Bush, Jebb Bush ya bayyana wa magoya bayansa cewa: “Abin da gwamnatin […]
A ranar Litinin da ta gabata ne tsohon Gwamnan Jihar Florida, wanda dan tsohon Shugaban Amurka kuma kanin tsohon shugaban kasar Amurka, ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar.
da ga tsohon Shugaban Amurka George H.W Bush kuma kanin Shugaba George W. Bush, Jebb Bush ya bayyana wa magoya bayansa cewa: “Abin da gwamnatin Amurka ta yi a shekaru bakwai da watanni da suka gabata, bashi ne Amurkawa suka sa rai su gani ba,” inji shi.
Ya ce: “Fatana shi ne na ga habbaka tattalin arziki Amurka. Kana masu matsakaicin karfi a sakar musu mara, ba abin da suke fuskanta ba a wannan lokacin musammam ma ta fuskar yawan haraji.” Daga nan ya bayyana cewa tattalin arzikin yana fuskantar rashin bunkasa saboda tafiyar hawainiya tare da dimbin bashi sabanin abin da zai samar.
“Wani abu kuma da gwamnati mai ci ta yi shi ne yadda ta kwashe tsawon lokaci tana kashe makuddan kudi wajen yake-yake a kasashen ketare.”
Sai dai Mista Jebb zai fuskanci ’yan takara har guda 10 wadanda za su gwabza tsakanin su kafi a fidda mutum daya daga cikinsu a karkashi jam’iyyarsu ta Republican, inda wasu masana suke ganin akwai wasu fitattun ’yan takara biyu da ake ganin za su iya taka masa birki. Irinsu sanatan daga Jihar Florida, Marco Robio da Gwamnan Jihar Winscosin wato Scott Walker. Masu kula da harkokin siyasar kasar ta Amurka sun ce Jebb ya tara miliyoyin daloli domin tunkarar wannan zaben. Sai dai Mista Jebb ya sa an cire sunan babansa a duk wani rube-rubuce na kanfen dinsa, abin da ake ganin ya yi hakan ne saboda batun kaucewa amfani da sunan gidansu.
A cikin watan Janairun shekara mai zuwa ne dai za a gudanar da zaben fidda gwani na jamiyyun nan biyu da suka fi tasiri a Amurka wato Republican da kuma Democrat.