Da mai kama ake kota
Yanzu dai tusa ta kare wa bodari, Gwamnatin Malam Muhammadu Buhari ta bayar da sanarwar cewa tana da cikakken bayani game da wadanda suka daka-wawa kan dukiyar mai, har ma da wadanda suka tatike baitul-malin kasar nan, suka kai wasu wurare a nan cikin gida da kuma kasashen ketare, suka tsibe, ba su ci ba, […]
Yanzu dai tusa ta kare wa bodari, Gwamnatin Malam Muhammadu Buhari ta bayar da sanarwar cewa tana da cikakken bayani game da wadanda suka daka-wawa kan dukiyar mai, har ma da wadanda suka tatike baitul-malin kasar nan, suka kai wasu wurare a nan cikin gida da kuma kasashen ketare, suka tsibe, ba su ci ba, ba su bari kudin sun amfani jama’a ba, wasu ne can ke cin gajiyarsu. Shugaba Muhammadu Buhari ya ce dubun barayin arzikin kasar nan ta cika, asirinsu ya tonu, ya kuma lashi takobin zazzakulo wadancan kudin a dukkan wuraren da aka sakaya su.
Shugaba Buhari ya furta haka ne sa’ilin da yake ganawa da tawagar wakilan Majalisar Wakilai ta Amurka da suka ziyarce shi a Abuja a ranar Litinin. Ko da yake Shugaba Buhari bai fayyace sunayen bankunan da dukiyar da aka sace daga Najeriya ke tsibe ba, amma ya yi amanna cewa an san inda suke da kuma yawansu da sunayen wadanda suka ketare da su can. Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na samun nasarori masu karfafa zukata da faranta rai a fafutukarta na ganin an danke barayin arzikin kasar nan, an kuma yi musu hukunci daidai da ta’asar da suka tafka.
Malam Buhari kuma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na samun goyon baya daga kasashen duniya don ganin ta kwato kudadenta da aka sassace, tana kuma samun bayanai masu amfani da gamsarwa dangane da halin da kudin ke ciki a bankunan kasashen waje, da kuma irin kokarin da gwamnatocin kasashen da kudin suke yi don hana barayin da suka yi awon gaba su canja musu maboya. Tun daga hawan Shugaba Buhari karagar mulki, da kuma bayan komowarsa daga ziyarar da ya kai Amurka, sai kasashen Turai suka yi ta tuntubarsa da niyyar tona asirin barayin mai, da kuma fallasa masa sunayensu da kuma jiragen ruwan da suka yi amfani da su don sace danyen mai da kuma bankunan da aka shigar da kudin da aka sayar da su a kasuwannin bayan fage a kasashen ketare.
An kuma tona masa asirin wasu masu jiragen da kan jidi mai daga Najeriya, wadanda daga bisani suke karkata akalar jiragen a tsakiyar teku, sa’anan kuma su juye man da suka dauko cikin wasu jiragen da ke tsumayinsu a can, su kuma canja takardun iznin daukan man da na wadancan jiragen, su karasa kasuwannin Turai don sayarwa. Daga bisani sai a shigar da kudaden da aka sayar da man cikin ajiyar wasu mutane dabam ba na gwamnatin Najeriya ba. Gwamnatin Buhari ta dade da sanin inda wadancan barayin man ke adana kudin man da suka sace daga Najeriya, kuma kasar Amurka da wasu takwarorinta na Turai, sun dukufa don taimakon Najeriya kwato wadancan kudin, domin kuwa suna tausaya wa mutanen Najeriya dangane da kwarar da ake yi masu, hakan kuma na kara jefa jama’ar kasar cikin ukubar da bakin talauci ke haddasawa.
Wadannan al’amura kuwa na faruwa ne a daidai lokacin da wasu kungiyoyin tantance ingancin gwamnatoci da hukumomin kasashen duniya da ake kira International Transparency Group suka wanke hannu kan Hukumar Mai ta Najeriya, watau NNPC, wacce ta yi kaurin suna a gida da waje saboda tsabar ha’inci da rashawa da cin hanci. Dangane da haka ne shugaba Buhari ya kafa kwamitin wasu gwamnonin jihohi guda hudu, a karkashin shugabancin Gwamnan Jihar Edo, Adams Osiomhole don gano inda wasu kudin sayar da man fetur suka yi ta zurarewa, kuma badakalar da aka fara bankadowa ta daure wa kowa kai, domin kuwa tana da ban tsoro da ta’ajibi. Gwamna Oshiomhole ya yi zargin cewa an gano wani ko wata minista a Gwamnatin Goodluck Jonathan da yin sama da fadi da zunzurutun kudi sama da dalar Amurka har miliyan dubu shida!
A daidai wannan lokacin ne kuma sai ga Shugaba Buhari ya cire shugaban hukumar NNPC, Mista Joseph Dawah, ya kuma maye gurbinsa da wani kwararren ma’aikaci daga kamfanin Eddon Mobil (Afirka), Mista Emmanuel Ibe Ikachukwu, kuma dan asalin yankin Neja-Delta, wanda ya fahaminci tsari da dabarun satar mai da kuma yanayin hanyoyin da awalajar man da aka sayar a ketare suke bi, suna zurarewa. An yaba da wannan nadi da aka yi masa, saboda cancantarsa da kuma gogewarsa a harkar hakar man fetur da kuma dillancisa, kuma ba makawa sai da Shugaba Buhari ya yi cikakken bincike game da ingancinsa da kuma nagartarsa da gaskiyarsa da rikon amanarsa kafin ya amince, ya danka masa amanar tukunyar dukiyar Najeriya. Mr Ikachukwu dai ya yi galba ne bisa wasu mutane guda uku da aka gabatar da sunayensu gaban Shugaba Buhari don ya darje wanda ya tabbatar wuyansa ya yi kauri, za ta kuma iya jure nauyin shirgin da za a dora mata.
Ba tare da bata wani lokaci ba, Mista Ikachuckwu ya karbi ragamar gudanar da wannan muhimmiyar ma’aikata, bayan Shugaba Buhari ya fayyace masa wasu muhimman ayyukan da zai mayar da hankalinsa akai da zarar ya zauna bisa kujerarsa, ciki kuwa har da tabbatar da cewa ya hada kai da hukumar EFCC da kuma ta leken asiri, watau DSS domin kwato dukkan dukiyar man da aka sassace, aka tsittsibe a bankunan kasashen ketare da kuma na cikin gida. Shugaba Buhari ya bukace shi da ya sanya idanu akan sauran kananan kamfanonin da ke karkashin NNPC don duba aikace-aikacensu da kuma farfado da matatun mai guda hudu, ta yadda za su komo da aiki gadan-gadan ko da kuwa yin haka zai sa a a gayyato ma’aikata ne daga kasashen ketare.
Ba shakka yanzu ne hukumar NNPC ta samu warki daidai kugunta, shi kuma sabon shugabanta ya samu maigidan da zai dinga gara shi yadda ya kamata don tabbatar da cewa aikinsa na yin kyau, yana kuma tottoshe dukkan hanyoyin aikata ha’inci da hukunta wadanda suka zarme wajen gurgunta ayyukan hukumarsa don azurta kawunansu. Da ma dai gwanayen magana na cewa da mai kama ake kota. Yanzu ne ayyukan hukumar NNPC za su kankama, su kuma inganta, kowa da kowa ya ci moriyarsu.