Da misalin karfe biyu za a yi jana’izar Bello Isa Bayero

Ya rasu a Asibitin Aminu Kano yana da shekara 87, bayan fama da jinya

Da misalin karfe biyu za a yi jana’izar Bello Isa Bayero

Fitaccen dan siya a Jihar Kano, kuma na hannun daman Shugaba Bauhari, Alhaji Bello Isa Bayero ya riga mu gidan gaskiya.

A ranar Alhamis Alhaji Bello Isa Bayero ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano yana da shekara 87, bayan fama da rashin lafiya.

Ya rasu ne ya bar mata biyu da ’ya’ya takwas kuma za a yi masa Sallar Jana’iza ranar Juma’a da misalin karfe biyu na rana a Kofar Kwaru, Fadar Sarkin Kano, bayan Sallar Juma’a.

Kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Kungiyar Magoya Bayan Jam’iyyar APC, kuma tsohon Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ne.

ِAlhaji Bello Isa Bayero tsohon dan kwamitin tsara komawa mulkin farar hula ne kuma tsohon dan jam’iyyun NCPN da UNCP a zamanin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha.

Ya taba takarar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya a 2011 amma aka kayar da shi.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatin Jihar sun mika ta’aziyya ga iyalai da abokan arzikin mamacin da kuma Masarautar Kano game da rasuwar dattijon.

Sun kuma yi addu’ar Allah Ya jikan sa, Ya kuma kyautata makwancinsa, Ya kuma ba wa iyalansa hakurin jure rashin.