Da mu za a yi zaɓen ƙananan hukumomin Kaduna — NNPP

Za mu fito da ’yan takarar ciyamomi 23 da kansiloli 225 a yayin zaɓen.

Da mu za a yi zaɓen ƙananan hukumomin Kaduna — NNPP

Jam’iyyar NNPP ta sanar da aniyarta ta shiga zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kaduna da za a gudanar a bana.

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kaduna, Muhammad Lawal Sultan ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis.

Yayin ƙaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar, Sultan ya ce sun shirya tsaf domin shiga a damu da za su a zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar a ranar 19 ga watan Oktoban 2024.

Sultan ya ce jam’iyyar ba wai iya shirin shiga zaɓen take yi ba, tana kuma shirye-shiryen karɓe akalar jagoranci daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

“Za mu shiga a dama da mu a zaɓen a dukkanin kujerun takara a ƙananan hukumomi 23 da ke jihar.

A cewarsa, “Jam’iyyar NNPP za ta tunkari APC a jihar kuma za mu fito da ’yan takarar ciyamomi 23 da kansiloli 225 a yayin zaɓen.

“A wannan Juma’ar za mu rufe sayar da fom ɗin shiga takara. Kuma muna alfahari da cancantar waɗanda za su riƙe tikitin takarar jam’iyyar a yayin zaɓen.

“Ina mai tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP na ƙara bunkasar da ke zama abin barazana wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC a jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.

“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun samu nasara la’akari da cewa a yanzu muna da cikakken goyon baya saboda al’ummar Nijeriya sun kai matakin intaha sanadiyyar ƙuncin rayuwa da suke fuskanta a wannan gwamnati.”

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta