Da na fi kowa arziki… (1)

Kasancewata haifaffen Birnin Kano, iyaye da kakanni, da na gaji Kasuwanci da Harkar Masana’anta da Noma da Kiwo, da Allah ya sa na fi kowa kudi a Najeriya tsawon shekaru 20 ko 30 zuwa yanzu da tuni na raya duk sana’o’inmu na gargajiya da aka sanmu da su: noma da  kiwo, jima da dukanci, sakar […]

Da na fi kowa arziki… (1)

Kasancewata haifaffen Birnin Kano, iyaye da kakanni, da na gaji Kasuwanci da Harkar Masana’anta da Noma da Kiwo, da Allah ya sa na fi kowa kudi a Najeriya tsawon shekaru 20 ko 30 zuwa yanzu da tuni na raya duk sana’o’inmu na gargajiya da aka sanmu da su: noma da  kiwo, jima da dukanci, sakar farin Kano/gwado/luru/zare da rini da dinki da kirar bakin karfe da farin karfe (aluminium da zinare da azurfa) da sassaka da  gini da sauransu. Da sai na zuba jari a kowacce sana’a, yadda zai mayar da ita masana’anta ta zamani, kowa ya samu aikin da zai yi, mu wadata kasa da duk abin da muke bukata na daga sana’o’in namu, yadda ba sai mu shigo da komai ba daga kowacce kasa a Duniya, sai dai idan mun wadata mu rika fitar da rara zuwa wasu kasashe masu bukata (muna samun kudin musaya – kari a kan na gurbataccen mai), maimakon yin almubazzaranci da kudin gurbataccen man wajan shigo da abubuwan da za mu iya yin fiye dasu wajan inganci da kiwon lafiya. Da tuni na kafa matatar mai a Kano wacce tafi duk Matatun Mai da muke dasu a Najeriya. Duk wani nau’in kayan abinci zan wadata kasa da shi, kowanne irin nama na dabbobi da tsuntsaye da kifi da madara sai na wadata Najeriya da shi, haka kwai na zabi da kaji da jimina sai dai wasu kasashe su saya a gurin mu. Haka dukkan bishiyoyi da tsirrai da muke dasu a Kano, misalin dorawa (da ake yin gaskami da kunun zaranya da shafen makuba da dabe, uwa-uba dadddawa da ake yi da kalwa – wato kwallon dorawar), zan rinka yin Daddawa a zamanance, a wadace, a ingance – ba tare da chemicals ba. Maimakon yadda makiya suka cimu da yaki wajen maye gurbin daddawa da ababen da ke kunshe da chemicals masu cutarwa; kamar ka fi-zabo, maggi da sauransu birjik. Muke fama da cututtuka marasa iyaka, marasa kan gado, ba cin tozarta masu yin daddawar ta kalwa, aka bar su babu abin yi sai bara.

Da kuma sai na samar da wutar lantarki mai inganci wacce za ta wadaci Jihar Kano da makwaftan jihohi yadda duk masana’antunmu za su wadata da ita awa 24 kullum, tsawon shekaru masu yawa ba tare da tsayawa ba (in samar da masu kula da sabunta duk abin da ya lalace – a kodayaushe).

A gefe daya kasancewata Musulmi zan kafa WAkAF, wanda zai kula da mabukata na lalura bacin mabukata zakka wadanda duk shekara zan fitar musu da daya cikin arba’in (1/40), kamar yadda Allah Ya yi umarni, a samu kwamitin zakka karkashin kulawar Malaman Sunnah da za su tabbatar duk wadanda suka cancanta su ci zakka su za a rika bai wa zakkar. Kuma zan kula da makwafta na shari’a, gidaje arba’in-arba’in; Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, da ‘Yan uwa na kusa da na nesa, da abokai.

Da tuni matsalar ma’aikatan Gwamnatin Jiha ta ta Kano ta kare, saboda kusan duk ma’aikatan za su kasance ma’aikatan kansu masu masana’antu ko ma’aikatan matatar mai, maimakon na gwamnati, sai dan abin da ba za a rasa ba. Maimakon kowa ya dogara da gwamnati, da sai dai ita Gwamnatin ta dogara da harajin da masana’antun za su rika biyanta, domin samar mana da tsaron rayuka da dukiya da lafiya da mutunci da uwa-uba addininmu, yadda ba za mu fuskanci kowacce irin barazana ba daga ko’ina; kusa da nesa, a Kiwon Lafiya da Harkar Ilimi Mai Zurfi, sannan Gwamnati ta shige mana gaba wajen tallata dukkan kayan da muke samarwa daga masana’antun namu idan muka samar da sama da abin da ake bukata a gida Najeriya. 

Da duk sauran bishiyoyi da tsirrai da fulawoyi da ake iya sarrafawa a yi magunguna da abinci mun hada gwuiwa da masana da gwamnati don a shigo da injina, tun daga kanana masu saukin sarrafawa (Cottage Industry) zuwa matsakaita (medium) da manya (large) zuwa sophisticated, yadda za mu rinka sarrafa ganyayyaki irin su; zogale da rama da yakuwa da makamantansu, a rika yin magunguna ko wadanne iri, maimakon shigo mana da na jabu da wadanda suka lalace (edpired) da ababen sa maye da haukatarwa. A rungumi masu magungunan gargajiya a yi musu horo na musamman, yadda za su tafi bai daya da ma’aikatan lafiya na zamani. Jami’o’inmu su dukufa wajen bincike da kere-kere, yadda nan gaba kadan ba sai mun shigo da kowanne irin injin masana’anta ba. Hatta jiragen sama da na kasa da na ruwa da motoci da babura da kekuna da kayan gyaransu (Spare Parts) da motocin noma da sauransu da maganin feshi, musamman idan muna tace gurbataccen man, za mu samu bye-products tun daga kwalta zuwa grease da abin yin tabarmar roba da takin zamani da sabulu da man shafawa da sauransu. 

Idan muka farfado da kamfanin Ajaokuta duk karfen da ake bukata za a samu, maimakon yanzu da ko allura ba ma kerawa, hatta tsinken sakace (toothpick) sai an shigo mana da na roba da na itace, duk yawan robar da Allah Ya bamu da itatuwa da tsinken kwa-kwa, amma saboda almubazzaranci da kudin mai ake shigo da wadannan abubuwan da muma za mu iya yinsu cikin sauki. Saboda tsabar wauta, muke fitar da gurbataccen mai muke kuma shigo da tatacce, ba cin da muna tacewa a gida Najeriya, yaya ba zai yi tsada sama da lokacin da ake tacewa a Najeriya ba? Lokacin da ba’a fara hako mai a Najeriya ba, ana shigo da fetur da kananzir da gas da duk sauran dangoginsu, ba mu taba ji ya yi tsada ko karanci ba, balle a ce babu! Sai da makiya Najeriya suka bayyana, suka kama kasa, suka yi agar, suke ganin kamar Allah ma bai isa ba, to mu bayin Allah ma mun fi karfin su da karfin Allah. Mun yi imani mulki na Allah ne, kuma laifin da muka yi wa Allah mun tuba, Allah muna rokonKa Ka yafe mana.

Lalacewar Shugabanci: Mu tuna Allah (SWT) Shi ne Ya yi umarni da a yi shugabanci da jami’an tsaro da alkalai da kotu da kurkuku, a dinga yin hukunci na adalci a kan kowa da kowa, ba tare da kowane irin bambanci ba, kamar yadda na sani tunda aka kashe Shugabannin Jamhuriyya ta Farko (su Sir Abubakar Tafawa balewa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato) a 1966 shugabanci ya fara tabarbarewa a Najeriya, zalunci ya kunno kai kamar da nufaka, mulkin soja ya yi kaka gida, aka yi sa a aka samu Janar Murtala Muhammad, wanda ya sadaukar da duk abin da ya mallaka, ban da gida daya da ya bar wa magadansa, sai dai bai yi tsawon rai ba, wata shida da fara mulkin sa aka kashe shi. Kamar yadda aka yi amfani da Janar Muhammadu Buhari da aka yi wa juyin mulki bayan wata 20 da fara mulkinsa, aka tsare shi tsawon wata arba’in (40), aka lalata komai, aka sace komai, aka tsiyata kasar, masu mulki suka azurta kansu. Har kwanan yau arzikin kasar nan yana hannun barayin shugabanni da suka yi wa Buhari juyin mulki a 1985, wanda ya haifar da halin da muke ciki har yanzu. Ba cin shekaru takwas na mulkin sojan da ya yi wa Buhari juyin mulki, shi ne ya fito da Obasanjo daga kurkuku ya zama shugaban kasa na farar hula na tsawon shekaru takwas.

A karshe har da neman kari (ta zarce). Duk da gargadin da Olu Falae ya yi a kan kada abar Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa, dan kungiyar asiri ne. Sai ga matsalar Boko Haram, wacce Janar Azazi ya ce PDP ce ta tsara ake kashe mutane, kafin shi ma ya mutu a hadarin jirgin sama. 

Yanzu kuma ga Dattijon Arziki Kanar Hameed Ali mai ritaya – Shugaban Kwastam na Najeriya ya gaya wa duniya, sama da kashi hamsin cikin dari (50%) na Jami’an Gwamnatin Tarayya ‘yan PDP ne, shi ya sa abubuwa suke cakudewa aka kasa ci gaba. Alhamdulillahi dama rashin samun masu karfin zuciya da imani irinsu Hameed Ali, wadanda za su fito su fadi gaskiya domin a gyara shine silar tabarbarewar al’amuran mulkin, sabanin yadda aka san Muhammadu Buhari a da. Kanar Hameed Ali ya tabbata dan kishin kasa, mai kaunar Muhammadu Buhari na farko a Gwamnatin APC. Ba a makara wajen aikata alkhairi (It is better late than neber).

Alh. Abdulkarim Daiyabu  Shugaban Rundunar Adalci Ta Kasa (Mobement for Justice In Nigeria – MOJIN) Tsohon Shugaban kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu, Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano (Kano Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture – KACCIMA) Tsohon Shugaban Jam’iyyar Alliance for Democracy (AD) na Kasa. Tel: 08023106666; 08060116666, 

[email protected]

 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa