Da na ga dama da an cafke Peter Obi a Kaduna —El-Rufai 

El-Rufai ya ce ’yan Arewa wayayyun mutane ne, don haka babu bukatar ya rama abin da Peter Obi ya yi masa.

Da na ga dama da an cafke Peter Obi a Kaduna —El-Rufai 

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce da ya ga dama ya ya rama abin da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya yi masa a lokacin da ya ziyarci jihar domin sa ido kan zabe. 

Wannan na dauke ne cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, inda El-Rufai wanda ke jawabi ga Kwamitin Hadin Gwiwa na Arewa a Jihar Kaduna, ya zargi Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, da sanyawa a tsare shi na tsawon sa’o’i 48 a gida a Jihar Anambra a lokacin zabe.

Ya ce da yana so da ya sa an kama tsohon gwamnan wanda zai ziyarci jihar domin yakin neman zabensa na shugaban kasa a 2023, wanda kuma zai shafe ’yan kwanaki a jihar.

El-Rufai inda ya jaddada cewa yana da karfin ikon sojoji a karkashinsa a Kaduna wanda zai iya amfani da su wajen tsare Peter Obi.

Sai dai El-Rufai ya ce ba zai kama Obi ba, domin ’yan Arewa mutane ne wayayyu.

Ya ce, “Kafin na karasa ina so na fadi wani abu, ina sanar da cewar na je Jihar Anambra domin sa ido a zaben jam’iyyata, amma Peter Obi wanda gwamna ne ya sa aka tsare ni na tsawon sa’o’i 48.

“Yau ni ne Gwamnan Jihar Kaduna kuma yana zuwa Kaduna don yakin neman zabe.

“Baya ga tarin jami’an tsaro, ina da runduna ta musamman ta sojoji a Kaduna, amma ba zan kama shi ba saboda mu ’yan Arewa mutane ne wayayyu.