Da ni ne INEC da na soke rajistar jam’iyyar APC-Galadima
Jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima ya ce in da a ce shi hukumar zabe ne ta INEC da tuni ya soke rajistar jam’iyya mai mulki saboda wadanda ke tafiyar da jam’iyyar sun kaucewa dokokin da suka kafa jam’iyyar. Buba Galadima wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC jiya […]

Jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima ya ce in da a ce shi hukumar zabe ne ta INEC da tuni ya soke rajistar jam’iyya mai mulki saboda wadanda ke tafiyar da jam’iyyar sun kaucewa dokokin da suka kafa jam’iyyar.
Buba Galadima wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC jiya ya ce in da a ce shi hukumar zabe ne da ya kwace shaidar rajistar jam’iyyar APC saboda shekaru uku bayan kafa ta jam’iyyar ta kasa yin taron kwamitin amintattu inda haka ya janyo ta kasa cika alkawuran da ta yi.
“Jam’iyyar APC ba ta cancanta ta zama jam’iyyar siyasa ba, dokokin jam’iyyar sun nuna cewa dole kwamitin amintattu da kwamitin gudanarwa da kuma kwamitin aiwatarwa su gana duk watanni uku. Amm har yanzu tun lokacin da aka yi wa jam’iyyar rajista, shin kwamitin amintattu ya taba zama? jam’iyyar bat a taba neman shawarar wadanda suka kafa ta ba don jin ko jam’iyyar na kan turba koko a’a”. Inji shi.