Da rancen Naira 2,500 na fara kasuwanci- Sani Mai Kayan Wuta

Alhaji Muhammad Sani Sulaiman matashi ne da ya yi fice a kan harkar kasuwancin kayayyakin wutar lantarki a yankin Saminaka. Wakilin Aminiya ya tattauna da shi inda ya bayyana yadda ya fara kasuwanci, matsalolin da ya fuskanta da kuma nasarorin da ya samu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Aminiya: Yaya ka fara kasuwanci?Sani Sulaiman: Na […]

Da rancen Naira 2,500 na fara kasuwanci- Sani Mai Kayan Wuta
Da rancen Naira 2,500 na fara kasuwanci- Sani Mai Kayan Wuta

Alhaji Muhammad Sani Sulaiman matashi ne da ya yi fice a kan harkar kasuwancin kayayyakin wutar lantarki a yankin Saminaka. Wakilin Aminiya ya tattauna da shi inda ya bayyana yadda ya fara kasuwanci, matsalolin da ya fuskanta da kuma nasarorin da ya samu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Yaya ka fara kasuwanci?
Sani Sulaiman: Na koyi harkar kasuwancin sayar da kayayyakin wuta ne a wurin mahaifina. A lokacin da na fara yana sayar da rediyo, ni kuma ina sayar da kayayyakin gyaran rediyo da talabijin. A takaice na yi shekara 18 da fara cin gashin kaina a wannan kasuwanci.
Aminiya: Daga lokacin da ka fara gudanar da wannan kasuwanci zuwa yanzu wadanne nasarori ne ka samu?
Sani Sulaiman: A gaskiya na gode Allah domin na samu nasarori da dama a harkokin kasuwancin da nake yi. Na fara ne da zuwa garin Jos ina sayo kaya in zo nan garin Saminaka na sayar ne. Da haka cikin yardar Allah har na koma ina zuwa Kano, daga nan na fara zuwa Legas. Harkokin kasuwancina suka bunkasa har na fara zuwa kasashen waje.
Da farko na fara zuwa Dubai, sai China. Akalla daga lokacin da na fara fita kasashen waje zuwa yanzu na je kasar China kamar sau 25 ina sayo kayayyakin wuta da nake sayarwa.
Aminiya: Yaya za ka kwatanta harkokin kasuwanci a Najeriya da kuma China?
Sani Sulaiman: A gaskiya babu yadda za a kwatanta harkokin kasuwanci a tsakanin Najeriya da kasar China, domin a China akwai gaskiya da amana wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu. Duk abin da ka saya a wajensu za su gaya maka gaskiya ba za su gaya maka karya ba. Kuma idan kuka yi alkawari da su ba za su saba ba. Sun riki sana’a da matukar mahimmanci, amma mu babu irin wadannan abubuwa a cikin harkokin kasuwancinmu.
Aminiya: Daga lokacin da ka fara gudanar da harkokin kasuwanci zuwa yanzu akalla ka yaye yara nawa?
Sani Sulaiman: A gaskiya ba zan iya sanin yawan yara da na koyawa kasuwanci ba. Domin na koyar da yara masu yawa, kuma a halin yanzu ma wasu sun zama wani abu.
Aminiya: Wanne kira za ka yi wa ’yan kasuwa musamman wadanda suke zuwa kasashen waje?
Sani Sulaiman: Idan har mutum zai je kasashen waje don sayo kayayyakin harkokin kasuwanci, ya kamata ya kawo kayayyaki ingantattu, kuma wadannan kayayyaki su kasance gwamnati ba ta hana shigowa da su ba, sannan ya kawo kayayyakin bisa ka’ida.
Aminiya: Ko kana da kira zuwa ga bangaren gwamnati don ta rika taimaka wa ’yan kasuwa?
Sani Sulaiman: Ina kira ga gwamnati ta rika taimaka wa ’yan kasuwar da ke zuwa kasashen waje, ta hanyar saukaka masu harajin shigowa da kayayyaki. Idan ta yi musu haka kayayyaki za su yi sauki, sannan ya kamata gwamnati ta rika taimaka wa kananan ’yan kasuwa da basussuka. Yin haka zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan.
Aminiya: Shawara ga matasa dangane da muhimmancin kasuwanci da sana’o’i fa?
Sani Sulaiman: Mutum ya kasance yana da sana’ar da yake yi ko kuma yana da aikin da yake yi shi ne mutuncinsa. Zaman banza ba shi da kyau. Kuma shi sha’anin harkar kasuwanci ko sana’a ko kuma aiki dole ne sai mutum ya hada da hakuri. Yanzu ka ga kamar ni da rancen Naira 2,500 na fara kasuwanci. Mahaifiyata ce ta ba ni rance. Amma cikin yardar Allah da na hada da hakuri na samu ci gaba har na kawo wannan matsayi.
Don haka yana da matukar mahimmanci matasa su tashi su rungumi sana’a da harkokin kasuwanci kuma su rike gaskiya tare da hadawa da hakuri. Kada su raina sana’a don farkon fara kasuwancina wasu abokaina ma dariya suke yi mani, saboda kankantar jarina. Ba fara kasuwanci da babban jari ne samun daukaka a kasuwanci ba. Sai ka ga mutum ya fara kasuwanci da karamin jari a hankali har sai ka ga Allah Ya albarkaci abin.