Da rashin kira…

Talakawa dai na sane game da yadda aka samu koma baya a dukkan harkokin raya kasa da iganta rayuwar jama’ar cikinta, musamman ma a fannin samar da wutar lantarki, abin da karancinsa ya kawo durkushewar masana’antu da karuwar rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da na rufin asiri. Wadannan ne manyan dalilan da […]

Da rashin kira…
Da rashin kira…

Talakawa dai na sane game da yadda aka samu koma baya a dukkan harkokin raya kasa da iganta rayuwar jama’ar cikinta, musamman ma a fannin samar da wutar lantarki, abin da karancinsa ya kawo durkushewar masana’antu da karuwar rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da na rufin asiri. Wadannan ne manyan dalilan da suka jawo rashin zaman lafiya a kasa, domin kuwa matasa, har ma da magidanta sun rungumi ta’addanci da aikata masha’a, talauci da fatara kuma suka mamaye ko’ina, lalaci ya yi katutu a zukatan jama’a, har ta kai shugabannin siyasa na sheke ayarsu yadda suke so, suna koya wa mabiyansu saka da mugun zare bisa akidojin kiyayya da tayar da husumar kabilanci da na addini.

Ta haka ne matasa suka lalace, da yawa daga cikinsu suka shiga fadace-fadace da juna; wasunsu suka koma sace-sace; aka samu gwanaye a harkar kashe-kashe; zaman lafiya da lumana suka gagara, aka komo kamar ba masu tsawatawa, tamkar ba wata kwakkwarar hukuma a kasar. To, amma ba wadannan ne kadai illolin da suka dade suna addabar jama’a ba, kuma gwamnatocin baya suka kasa magance su, sai dai ana iya cewa duk wadannan masifun abu guda ne ya jawo su, watau koma bayan karayar tattalin arziki, sakamakon rashin wutar lantarki, kamar yadda sauran ma akwai dalilan da suka assasa su.
Tun farkon komowar mulki hannun farar hula a 1999, Shugaba Olusegun Obasanjo ya sha alwashin magance matsalar wutar lantarki kwata-kwata a kasar nan, abin da ya danganta da rashin turzawar gwamnatocin baya da ‘yan arewar da suka danka masa mulki suka jagoranta, wajen tunkarar matsalar tun tana ‘yar karama har sai da ta gawurta. Kafin kiftawa da bisimilla sai ga sabon minista na wutar lantarki a wancan zamanin, Cif Bola Ige ya ce, cikin watanni shida za a samar da ingantacciyar wutar lantarkin da ba za a rika dauke ta ba a ko’ina a fadin tarayyar kasar nan.
Amma me ya faru? Me kuwa in ban da sakaci irin wanda ya dara na sojojin da ake zaton su ne suka hana ruwa gudu? Wasa-wasa dai sai ga wankin hula ya kai gwamnatin Obasanjo maraice, kuma sai da aka yi shekaru takwas, aka kuma narkar da makudan kudi na fitar hankali, amma duk da haka nan wutar ba ta samu yadda ake bukata ba, domin kuwa wadannan kudin zurarewa suka yi zuwa aljiffan shugabannin da aka kasa hukuntawa, wadanda aka tabbatar suna da hannu dumu-dumu wajen salwantar dukiyar da aka tanada don giggina sababbin tashoshin bayar da wutar lantarki da kuma kyautata hanyoyin rarraba ta zuwa dukkan lungunan da ake bukatar amfani da ita. Ba abin da aka yi don kwato wannan dukiyar, domin gafiyoyin da suka handame ta sun tsira da na bakunansu.
Gwamnatocin da suka biyo baya ma haka nan suka shantake game da batun karfafa wutar lantarki, ba wani abin da suka yi sai burgar aiki da yanka wa talakawa karairayi game da wa’adin kammala ayyukan, sai kuma daga bisani a sake yankan wani wa’adin, a kuma kawo wata ladifiyar hujja a dangana ta da gazawar da aka yi wajen cika alkawurran. Ba wani abu ba ne ke hana kammala ayyukan samar da wutar lantarkin ba illa jajircewar shugabanninmu wajen sayar da hukumar wuta ta PHCN ga kamfanonin Turawa, wadanda ke wasa da hankalin gwamnati wajen biyan awalajar kamfanonin da suka taya, aka kuma sallama musu, amma ba ki biya kan kari. To yanzu ga shi nan kowa ya gani, wai an yi wa ‘ya mugun miji, tabarbarewar wutar lantarki ta kai intaha a kasar nan kafin saukar gwamnatin da ta gabata wacce haka nan ta danka wa Shugaba Buhari mulkin kasar na cikin matsanancin duhu, kuma babu wata na’urar da ke motsawa saboda karancin wutar da ta talauta talakawan kasar nan. Haka nan dai wadancan gwamnatocin da shugabansu suka shantake, suka shiga sharholiyar banza da dukiyar da ya kamata a sarrafa ta wajen inganta hanyoyin samar da wutar lantarkin da za su farfado da masana’antun da suka durkushe da siradansu. Babu kunya, ba tsoon Allah, suka yi ta cika baki da fariyar banza, wai suna samar da wadatacciyar wuta, kuma hakan na amfanan masana’antu, alhali kuwa kowa ya san sun dade da zama fanko.
Shi ya sa Shugaba Buhari bai yi wani kawaici ba wajen fayyace wa ‘yan Najeriya cewa kasar fa ta tsiyace, kuma gwamnatinsa ta tashi tsaye wajen daukar matakan magancewa da suka hada da kwato dukiyar haram din da azzalumai suka handame da kuma dukufa ka’in da na’in wajen fadada ayyukan gona da hakar ma’adinai, domin wadannan ne kawai masana’antun da aka tabbatar za su iya samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa da magidantan da ba su da abin yi. Yin haka shi ne mafi a’ala, kuma idan an samu nasarar kwato dukiyar da aka sassace, aka tsibe a ketare, sai a fara aiki da su wajen tallafa wa matasan da ke sha’awar noma, sauran kuma a karkata su wajen hakar ma’adinai. Idan aka bar dukiyar mu da aka sace a kasashen ketare, za a kara wa mai karfi karfi ne, kuma hakan bai kamata ba, domin da rashin kira karen bebe ya bata.