Da sana’ar babbaka nake alfahari – Muhammadu Nura

Sana’ar babbaka tana da dadadden tarihi kuma wata nau’i ce ta fawa da ta kunshi babbakar kai da kafafun awaki, tumaki da shanu da rakuma. Wakilinmu ya yi kacibis da wani matashi mai suna Muhammadu Nura wanda ake wa lakabi da Muslim, da ke gudanar da sana’ar babbakar kan awaki Unguwar Hausawa da ke Kalaba, […]

Da sana’ar babbaka nake alfahari – Muhammadu Nura
Da sana’ar babbaka nake alfahari – Muhammadu Nura

Sana’ar babbaka tana da dadadden tarihi kuma wata nau’i ce ta fawa da ta kunshi babbakar kai da kafafun awaki, tumaki da shanu da rakuma. Wakilinmu ya yi kacibis da wani matashi mai suna Muhammadu Nura wanda ake wa lakabi da Muslim, da ke gudanar da sana’ar babbakar kan awaki Unguwar Hausawa da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba, inda ya tattauna da shi  kamar haka:

Ko za ka gabatar mana da kanka?
Sunana Muhammadu Nura amma ana kirana da lakabin Muslim, lakabin da na samu saboda ina kamanta gaskiya. Wata rana daga cikin abokaina muna zaune, sai daya daga cikinsu ya ce gaskiya abin da na kamanta ya kamata a ce mini Muslim.
Ina gudanar da sana’ar babbakar kawuna, muna babbaka kawunan awaki zuwa tumaki da na shanu, har rakuma ma idan an kawo kawunansu, zan iya babbakewa.
Yaushe ka fara wannan sana’a ta babbaka?
Yanzu ina da shekara 15 da fara ta.
A ina ka koyi babbaka?
Na fara ta a garin Bungudu da Jihar Zamfara. Can na koye ta, ina makaranta lokacin. Idan muka taso daga makaranta sai in zo mahauta  ina rika yi musu aiki kadan-kadan har na koyi aikin na iya, tun suna sanya ni babbaka har ma ya kai ina iya aikin nama.
Yanzu maimakon ita ce da ake hadawa a yi babbaka, na ga wata na’ura kake amfani da ita tana hura wa wutar iska sai kuma gawayi; yaya za ka kwantata yadda kake amfani da wannan sabuwar fasaha?
Wancan zamani suna ba mu kudi mu sayo itace, sai mu kunna wuta, sannan sai muka ga akwai wahala. Muka ga wannan injin na makera sai muka ce su sayo mana shi. Shi ne suka sayo, muka kafa shi a kasa muke amfani da shi. Da mun kunna wutar wannan injin muna juya shi yana hura wutar cikin kankanen lokaci sai mu yi babbaka mai yawa.
Ko sana’ar babbaka tana biya ma bukatunka tun daga lokacin da ka fara ta zuwa yanzu?
Alhamdulillahi, bakin gwargwado na samu a yanzu fiye da wancan zamani. Wancan zamani muna samun a wuni bai fi Naira 500 ba, wani lokacin kuma 400. Idan kuma kasuwa ta yi mana kyau wata rana har Naira 600 nake samu. Yanzu kuma muna yin ta Naira dubu biyu zuwa Naira dubu uku, har zuwa Naira dubu hudu.
Mene ne babban burinka a wannan sana’a?
Ina fatan wannan sana’a ta zama abin da zan dogara da ita, in taimaka wa wani ma. Kuma in yi wa ’ya’yana kyakkyawan fandisho na rayuwa. Duk a cikin wannan sana’a na yi aure na haihu, na yi suna duk a ciki. Na sayi fili ma, ina niyyar ginawa duk da wannan sana’a ta babbaka.
Ko a cikin ’ya’yanka za ka so wani ya zama magajinka ko makaranta za ka fi so su fi yi?
Gaskiya a yanzu suna makaranta.
Ga shi kai matashi ne, bakin gwargwado kamar yadda ka ce kana samu, wasu matasan da sun ga Naira ta fara zuwa sai tunanin kara aure. Kai ma kana da irin wannan ra’ayi?
Gaskiya ina da burin kara aure amma ba haka ba, ina son sai Allah Ya kara daukaka ni a kan wannan sana’a, na gama tallabar ’ya’yana sun yi karatun addini da na zamani. Saboda ko da ni ko ba ni, nan gaba za su iya taimaka wa iyayensu mata.
Ka taba neman taimako ko rance daga karamar hukumarku ko gwamnatin jiha don ka bunkasa wannan sana’a taka?
A’a, ban taba ba, sai dai ina so ’yan uwa da abokan arziki su tallafa mini domin bunkasa wannan sana’a don ni ma in jawo wasu su amfana jikina.