Da sana’ar dinki na dauki dawainiyar karatuna -Musa Tela

Wani matashin tela da ke sana’ar dinkin kaya a Lagas mai suna Musa Isa ya ce ya kuduri aniyar yin amfani da sana’arsa ta dinki ya dauki nauyin karatunsa na boko don ya yi aikin gwamnati.Musa Isa, dan  kimanin shekaru 24, wanda aka haifa a Jihar Kano, ya yi furucin haka ne yayin da yake […]

Da sana’ar dinki na dauki dawainiyar karatuna -Musa Tela

Wani matashin tela da ke sana’ar dinkin kaya a Lagas mai suna Musa Isa ya ce ya kuduri aniyar yin amfani da sana’arsa ta dinki ya dauki nauyin karatunsa na boko don ya yi aikin gwamnati.
Musa Isa, dan  kimanin shekaru 24, wanda aka haifa a Jihar Kano, ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, “Gaskiya sana’ar dinki, a ganina, wahala gare ta. Shi ya sa na yanke shawarar yin aikin gwamnati, wanda ya fi sana’ar dinki sauki. Kuma ni da ma na fi sha’awar yin aikin gwamnati. Shi ya sa lokacin da nake koyon dinki ina firamare da na kammala da ita na rika daukar dawainiyar karatuna na sakandare har na kammala. Ga shi yanzu ina neman shiga makarantar gaba da sakandare kuma ina da burin da na kammala zan nemi aikin gwamnati na rika yi. Shi ke nan na yi bankwana da  sana’ar dinki”.
Ya ci gaba da cewa, “Abin da ya sa ka ji na ce aikin gwamnati ya fi sana’ar dinki sauki shi ne, aikin gwamnati ba kullum ake yi ba, akwai hutun Asabar da Lahadi, amma shi dinki  babu hutu. Musamman ma a sana’ar dinkin kayan sanyi na yara, ba ka da wani hutu, kullum a cikin aiki kake, sai ka ce inji. Ni kuma mutum ne mai son sararawa da hutawa, ba na sha’awar kullum na kasance cikin aiki ba hutu sai ka ce agogo”.
Musa, wanda ake yi wa lakabi da Abba, ya bayyana cewa bai fuskanci wata matsala ba lokacin da yake koyon sana’ar dinki.
Saboda haka sai ya ce cikin dan lokaci kadan ya koyi dinki a wurin maigidansa ba tare da wata matsala ba. “Ka san idan aka ce akwai yarinta, kwakwalwar mutum tana ja, ba za ka sha wahalar koyon abu ba. Shi ya sa lokacin da na shiga sana’ar nan, ina da karancin shekaru don a lokacin ina makarantar firamare. Saboda haka ina shiga sai na iya ba tare da wani kbata lokaci ba. Kodayake na dan sami matsala ta rashin sauri, amma duk da haka daga bisani na kware. Da an ba ni kaya, cikin dan kankanen lokaci, sai na kammala shi”. Inji shi.
Ya bayyana cewa ya sami nasarori da dama kamar daukar nauyin karatunsa na sakandare da samun kudin da zai rika daukar nauyin kansa da na iyayensa.
Ya yi kira ga matasa su rike sana’ar hannu domin tana da alfanu a rayuwar dan Adam.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50