Da Sana’ar Kosai nake gudanar da rayuwata – Laraba Manu
Zainab Usman wacce aka fi sani da Laraba Manu mai kosai a bakin Nepa ofis a Gombe mace ce da ta tashi tsaye wajen Neman na kanta kuma duk wani fadi tashin rayuwa da wannan sana’a take rufawa kanta asiri. Ta bayyanawa Aminiya yadda ta fara yadda ta fara sana’ar da kuma irin rufin asirin […]
Zainab Usman wacce aka fi sani da Laraba Manu mai kosai a bakin Nepa ofis a Gombe mace ce da ta tashi tsaye wajen Neman na kanta kuma duk wani fadi tashin rayuwa da wannan sana’a take rufawa kanta asiri. Ta bayyanawa Aminiya yadda ta fara yadda ta fara sana’ar da kuma irin rufin asirin da take samu. Ga yadda hirar ta kasance.
Ta Yaya kika fara wannan sana’a kuma shekara nawa kina yin ta?
Na fara tun bani da jari nawa na kai na, har na samu jari kuma na fara wannan sana’ar, yanzu haka shekara takwas da wata hudu ke nan.
Ya za ki bayyana irin wannan sana’a ga wanda bai san yadda take ba da irin alherin da ke cikin ta?
To mai sana’ar kosan Doya da Dankalin Turawa irin wannan ba yadda za ayi a wayi gari ya dinga kukan ya zai yi da rayuwa saboda akwai rufin asiri a cikin ta.
Kin ce kin fara sana’ar tun baki da jari, ko za ki gaya mana yadda aka yi kika samu jarin?
lokacin da zan fara wannan sana’ar ta kosai, bani da jari ko na sisin kwabo. Masallacin Nepa ne suka ce na nemi wanda za su bai wa jari don yin sana’ar, sama da wata biyu ina bin wata kawata don ta so ta yi sana’ar, sai ta ki. Ganin haka ni kuwa na nuna sha’awar zan yi sana’ar sai suka bani kudin naira dubu uku, da wannan kudin na fara. Bayan na fara ita kawar tawa da sai take zuwa tayani tuya kuma.
Ganin kin fara da jarin dubu uku yanzu jarinki ya kai nawa?
Daga naira dubu uku sanda na zo, na mallaki jari nawa na kaina sama da naira dubu ashirin da biyar amma yanzu da rayuwar komai ya canja jarin ya yi kasa, ina bukatar a tallafi.
Wane rufin asiri kika samu a sana’ar?
A lokacin wata damuna da akayi ruwan sama ya rusa min dakin mahaifiyata, da kudin kosai na gina mata dakin, sannan kuma ina sanya sutura mai tsada irin wanda raina ke so.
Menene kiranki ga masu zama ba sana’a?
Ba su yi wa kansu adalci ba. Duk mai zama ba sana’a ba mace kadai ba, har namiji yana bata wa kansa lokaci ne, saboda duk wanda ya tsaya sai wani ya yi masa akwai matsala. Yanzu rayuwa ta canja shi wanda zai maka din yanzu shi ma yana iya rasawa, sannan su kuma mata kar su ce sai mazajensu sun yi musu, su tashi tsaye su nema ya zama kafin ayi miki kin yi wa kanki har ma ki taimaka ma wasu.
Daga karshe menene kiranki ga gwamnati?
Kirana ga gwamnati bani kadai ba, duk wani mai sana’a ko babba ko karama a taimaka musu saboda ganin sun dogara da kansa. Saboda zama ba sana’a shi yake jefa mutane ga halaka.